DAGA INA MATSALAR TAKE ?(6)
A rubutnmu fitowa da ta gabata mun kawo maganganun Shehu Inyas inda yake tabbatar da Shehu Tijjani a matsayin Allah , ta yanda yake jingina masa ayyuka na ubangijintaka kamar : halittan halittu , da gudanar da su , da rayar da su da azurtasu .
A yau zamu kawo maganganunsa ne inda 'karara yake cewa Shehu Tijjani shine tsantsan Allah .
Shehu Inyas yana cewa : Shehu Tijjani shine a madadin Allah a ban 'kasa , don haka duk wanda ya ga Shehu Tijjani to ha'ki'ka Ubangijin halittu ya gani "
Ga nan maganarsa kamar haka :
" خليفة الله في أرض لذلك من ## رآكم فقد رآ رب البريات "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ٨٤)
Anan Shehu Inyas ya tabbatar cewa Shehu Tijjani shine Halifan Allah aban 'kasa , wanda wannan matsayi kuma ma'anarsa a wurin Sufaye shine : Wanda yake shine rayuwar dukkan halittu , mai gudanar da su , dukkan halittu idan sun yi wata bauta to shi suke bautamawa .
Shehu Tijjani da kansa ya yi bayanin ma'anar wannan matsayi na walittaka bisa wannan ma'anar kamar yanda muka kawo a fitowa ta farko da ta biyu na wannan matashiya .
Daga cikin abunda ya ambata akwai kamar haka :
" هو الروح في جميع الموجودات ، فما في الكون ذات إلا هو الروح المدبر لها والمحرك لها ، والقائم فيها، ولا في في كورة العالم مكان إلا هو حال فيه متمكن منه "
(جواهر المعاني ، ٢٢٥/٢)
A wani wurin kuma ya ce : Shehu Tijjani shine sha'anin Allah , alamar duniya , kuma shine albarkatun Allah , kuma shine tsantsan Allah "
Ga nan maganarsa :
" فشأن الحق رمز الكو ## ن فيض الله عين الله "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ١١٨)
A wani wurin kuma ya ce :
" همامي تاج أهل الله ## همامي عين عين الله "
"Shehu Tijjani shine abun damuwar zuciyata , kuma shine kambin ma'abota Allah , kuma shine tsantsan zatin Allah "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ١٢٢)
A wani wurin kuma yake cewa : Mabayyanar zatin Ubangiji na , kuma ha'ki'kanin Allah shine zatin Shehu Tijjani "
Ga nan maganarsa kamar haka :
" فإن الشيخ مظهر ذات ربي ## و عين العين عين أبي العباس "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ١٠٧)
A wani wurin kuma ya ce :
" فبرهام عبيد و هو ملك ## لهذا القطب جحجاح همامي "
" Barhama ( Inyass) 'dan 'karamin bawane mallakar wannan 'Ku'dubi Shugaba abun damuwata ( Shehu Tijjani ) "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ١٠٤)
Wa'dannan maganganu na Inyass dukkansu suna tabbatar da cewa lallai Inyass yana 'daukan Shehu Tijjani ne a matsayin Allah .
Da yake Inyass ya riga ya 'dauki Shehu Tijjani a matsayin Allahnsa , saboda haka kawai sai ya mi'ka wuya gareshi ta hanyar tsayuwa tu'kuru wurin bauta masa da mafi girman nau'uka na bauta ; ta yanda yake ro'konsa da ya tsaftace masa zuciyarsa , ya yafe masa zunubansa , ya kiyayeshi daga sharrin ma'kiya , ya saukar da ruwan sama ga halittu , ya tsirar musu da tsirrai ...
Ga maganganunsa nan kamar haka :
" و قد ألم بنا شكوى و ضاق فؤا ## دي بالجوى زحزحن غمي و تنجيني
فكن مجني على ما أتقي و سرا ## جي في الظلام و خريتي فتهديني
إذا أخذت زمامي كنت ذا رشد ## و لا تكلني إلى تفسي فتغويني
إني ارتكبت ذنوبا شددت أسفي ## طهر فؤادي عن غم و عن رين "
" cuta ta sauka akanmu kuma zuciyata ta 'kuntata da damuwa , don haka ka nesanta damuwata daga barina, kuma ka tseratar da ni ( ya Shehu Tijjani) .
Ka zama ( Shehu Tijjani ) kariya gareni daga dukkan abunda nake tsoro , kuma ka zama fitila gareni acikin duhu , kuma ka zama madugu gareni sai ka shryar da ni .
Idan ka yi ri'ko da ragamata to zan rayu ina mai shiriya , don haka kada ka fawwala ni ga zuciya ta sai ta halakani .
Lallai na aikata zunubai masu yawa wa'danda suka tsananta damuwata , don haka ka tsaftace zuciyata daga damuwa da kuma tsatsa "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ٨٩ )
A wani wuri kuma ya ce : Ina so in kai ga wani babban matsayi wanda babu wani matsayi sama da shi , don haka kaimin baiwan wannan matsayin , ka shiryar da ni , ni ma sai in shiryar "
Ga nan maganarsa :
" أريد مقاما ليس من فوق فوقه ### مقام ، فهب لي ذاك أَرشد أُرشِد "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ٧٩)
A wani wurin kuma ya ce : ka kwaranyewa dukkan musulmi damuwarsu ( ya Shehu Tijjani ) "
" ونفس كروب المسلمين جميعهم ## فإني و قفت اليوم قربك مجتدا "
Awani wurin kuma yake cewa : Ya kai Shehu Tijjani ka kiyaye zuciyar masoyinka , ka kareshi daga ma'kiya da suka kewayeshi .
Ya Shehu Tijjani ka yi baiwan saduwa da kai , ga ni nan a bakin 'kofarka a tsaye , ga ma'kiya nan gefena kewaye da ni.
Ya kai Shehu Tijjani Ka biya min bu'katuna , ka rayar da garuruwa , saboda kaine kake sanya 'kasa ta girgiza ta fitar da tsirrai "
أبا العباس حصن نفس حب ## و دافع عنه أعداء أحاطوا
أبا العباس مُنَّ الوصل إني ## ببابك واقف : حولي الحياط
أبا العباس هات مناي أحي ال ## بلاد فمنك تهتز البلاط "
( طيب الأنفاس ، حرف الطاء)
A wani wurin kuma yake cewa :
" Ya kai Shehu Tijjani ka tallafawa wannan ba'ko ( Inyass) wanda dandazon ma'kiya suka kewayeshi .
Ka mayar da makircin dukkan mai makirci ga wannan bawa ( Inyass) ya kai abun bautana , abun bautan dukkan bayi .
Daga gareka nake fatan samun bu'katuna , bayan na samu manufofina .
Kaine Ubangijina ya kai abun bautana , kuma Kaine mai bani agaji , kuma kaine mai shiryar da ni .
Bani da wanda zai taimakeni koma bayanka , kuma dama taimakon mai karamci ( mai kyauta ) shine isashshe"
"ضُمَّ يا شيخ غريبا ## حفه جمع الأعادي
فامكرن ماكر عبد ## يا إلهي للعبادي
منك أرجو نيل قصدي ## بعد ما نيل المرادي
أنت ربي يا إلهي## و غياثي أنت هادي
ليس لي غيرك عون ## و كفى عون الجوادي "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ١٢٤)
Acikin dukkan wa'dannan maganganu na inyass yana tabbatarwa 'karara cewa Shehu Tijjani shine Allahnsa , kuma shi yake bautamawa .
A rubutunmu na gaba zamu Kawo maganganunsa da yake 'kudurce cewa : kowa ma Shehu Tijjani ne ; a'kidar da ake kiranta a cikin Tijjaniyya da : " Alha'ki'katul Ahmadiyyah " .