DAGA INA MATSALAR TAKE (14) ?
A 'kar'kashin wannan matashiya , mun kawo bayanai daga turaku na 'dari'kar Tijjaniyya ; wa'danda suke bayyana ha'ki'kanin matafiyar 'dari'kar , na allantar da halitta , da halatta muharramai , da fifita matsayin Shehinnansu akan matsayin Annabawa da manzanni , da 'daukan Shari'ar Annabi Muhammad a matsayin addinin gidadawa jahilai , itakuma shari'arsu ta ba'diniyyah ( ha'ki'ka) a matsayin addinin wayayyu masu ilimi da fahimta .
Wa'dannan miyagun 'kudurori bisa ha'ki'ka sune sinadaran da suke gudanar da 'dari'kar Tijjaniyyah , duk da cewa bisa doka ta 'dari'kar , duk wa'dannan miyagun 'kudurori wa'danda su ka yi hannun riga abayyane ga Addinin Annabi Muhammad , ba'a bayyanasu ga jama'a ; ana boyesu ne sai ga wanda ya yi imani ga dokokin da Shehu Tijjani ya shimfi'da na sabuwar shari'arsa ta Tijjaniyyah ( kamar dai yanda 'yan ba'diniyyah na farko suke yi ) , amma duk wanda yake ba mabiyin 'dari'kar ba , ko kuma bai kafu ba sosai acikin 'dari'kar ; to duk wa'dannan miyagun a'kidu na kafirci da alfasha za'a ringa 'boyesu daga garesu , sai a ringa bayyana masa 'dariqar a tufa ta addinin musulunci .
Wannan shine tafarkin da shuwagabannin 'dari'kar su ka gudana akansa a wurin da'awa ; tun daga kan shehu Tijjani har zuwa kan mu'kaddaman 'dari'kar da su ka zo bayansa .
Zamu kawo wani sashe na zantukan Shehu Tijjani inda yake tabbatar da abunda muka ambata .
Shehu Tijjani yana wasici ga wani muridinsa sai yake cewa da shi :
" Abunda nake yi maka nasiha da shi iyakar nasiha ; kai bari ma , wajibine ka kiyayeshi , duk wanda ya sa'ba masa tabbas ya halaka ; wasiyyar itace 'boye dukkannin abunda muka ambata maka a baya, sannan kuma da 'boye dukkan sirrika ( miyagun 'kudurori na kafirci da fajirci ) ba tare da togaciya ba , saboda su sirrika 'kaburburansu sine 'kirazan 'yantattu , kuma dai sirrika 'kaburburansu sune 'kirazan za'ba'b'bu , kuma sirrika 'kaburburansu sune 'kirazan manya_manya.
Wani daga cikin manya yana cewa :
" Sirrika awurina yana cikin wani gidane da aka kullesa , makullansa sun 'bace , kuma 'kofarsa tana kulle .
Babu wanda zai ringa 'boye sirrika ( a'kidun kafirci da fajirci ) sai wanda yake ma'abocin karamci , amma kuma miyagun mutane sune suke watsa sirrika "
Ga bayanansa nan da lafuzzansa :
" فالذي أوصيك به كل الوصية ، بل هي واجبة من خالفها هلك ، وهو الكتم عما ذكرناه لك قبل ، ثم الكتم مطلقا من غير استثناء ، فالأسرار قبورها صدور الأحرار ، والأسرار قبورها صدور الأخيار ، والأسرار قبورها صدور الكبار .
قال بعض الكبار :
السر عندي في بيت له غلق ** ضاعت مفاتحه والباب مقفول
لا يكتم السر إلا كل ذي ثقة ** والسر عند لئام الناس مبذول .
( جواهر المعاني ، ٢/ ٢٠٣)
A cikin wannan bayani na Shehu Tijjani zamu ga yana wajabtawa mabiyansa da 'boye sirrikansu na 'dari'ka ( wanda suke a matsayin kafirci bisa shari'ar musulunci ) , kuma yana kwarzanta masu 'boye sirrikan da kambamasu , a 'dayan hannun kuma yana aibanta masu bayyana sirrikansu na 'dari'ka a matsayin miyagun mutane marasa amana .
Da wannan mutane za su fahimci bisa ha'ki'ka inkari da wasu Shehinnai suke yi akan masu bayyana ha'ki'kanin matafiyar 'dari'kar daga bakin wasu mabiyan 'dari'kar ; na allantar da shehinnai , da zagin Annabi , da halatta muharramai , duk wannan inkarin ; inkarine kawai akan mutanen bisa sa'bawarsu ga dokar Tijjaniyyah na wajibcin 'boye sirrika, amma ba wai don ita 'dari'kar ba haka take ba .
A wani wurin Shehu Tijjani yana cewa :
"Lallai muna da wani matsayi awurin Allah , wanda ya kai ma'kura a wurin 'daukaka , ta yanda ya zama haramun ne bayyana wannan matsayin , ba shine abunda na ambata muku ba ( abunda ya ambata musu shine : ya ce da su : tun daga farkon halittan halittu har zuwa 'karshenta , babu wani waliyyi da zai sha ko ya shayar face daga tekun Shehu Tijjani yake sha kuma yake shayarwa .
Sannan kuma ya ce : Annabi ya fa'da masa cewa : matsayinsa " Shehu Tijjani " ya fi 'daukaka daga dukkan matsayi .
Kuma ya ce : ruhinsa da ruhin Annabi Muhammad matsayinsu kamar matsayin yatsan tsakiyane da manuniya na tafin hannu ) , da zan bayyana muku wannan matsayi ; da ma'abota gaskiya da sanin Allah sun yi ijma'i akan kafirci na , ballantana kuma gama_garin mutane "
Ga bayanansa nan kamar haka :
"إن لنا مرتبة تناهت في العلو عند الله تعالى ، إلى حد يحرم ذكره ، ليس هو ما أفشيته لكم ( وهو قوله لهم : " لا يشرب ولي ولا يسقي إلا من بحرنا ،من نشأة العالم إلى النفخ في الصور "
وقوله مشيرا بأصبعه السبابة والوسطى : روحه صلى الله عليه وسلم وروحي هكذا "
وقوله لهم : إن النبي (ص) أخبره بأن مقامه أعلى من جميع المقامات " ) ، ولو صرحت به لأجمع أهل الحق والعرفان على كفري فضلا عمن عداهم "
( رماح حزب الرحيم ، ٢/ ٢٧٨)
A wannan bayanai zamu ga a aikace Shehu Tijjani yana aiwatar da dokar da ya gindaya a 'dariqarsa na 'boye sirri ; ta yanda yake 'boye wani mummunan 'kuduri _ duk da cewa ya bayyana wasu wa'danda suma kafircine tsagwaro _ kuma ya tabbatar da kansa cewa da zai bayyana wannan sirri da ba'abota gaskiya da ilimi zasu yi ijma'i akan kafircinsa !!
Anan akwai ababe biyu :
1. Shehu Tijjani ya yarda lallai musulmin da basa 'kudurce miyagun A'kidu irin nasa sune ba'abota gaskiya da sanin Allah . kenan shi shehu Tijjani ba ma'abocin gaskiya bane da sanin Allah acikin wa'dannan miyagun sirrikan nasa da yake 'boyewa .
2. Shehu Tijjani ya yarda da cewa wa'dannan sirrikan nasa sirrika ne na kafirci bisa shari'ar musulunci , kuma ijma'i na malaman musulmi ya tabbatar da kafircin duk mai 'dauke da wannan sirrika , kuma wannan matsaya ta malaman musulmi itace matsaya ta gaskiya .
Wannan yana tabbatar da cewa lallai wa'dannan mutanen sun yarda cewa bisa shari'ar musulunci su ba musulmai bane , kamar dai yanda muka gabatar a wannan matashiya fitowa ta sha uku , inda Inyass ya tabbatar da kafircin mai 'dauke da miyagun A'kidunsu bisa shari'ar musulunci , amma kuma ya ce bisa addininsu na ha'ki'ka mai wannan A'kidu shine ma mumini !!
A wani wurin Shehu Tijjani ya 'kara fayyace magana yana cewa :
"Da zan bayyana abunda Allah ya sanar da ni , da ma'abota sanin Allah sun ha'du akan kasheni "
" لو بحت ما علمنيه الله تعالى لأجمع أهل العرفان على قتلي "
( رماح حزب الرحيم ، ٢/ ٤١٣)
A wani wurin kuma , Shehu Tijjani yana bayanin dokarsu ta bai 'daya aharkarsu ta ba'diniyyah ( ha'ki'ka ) , sai yake cewa :
" Cikakku daga cikin ma'abota wannan tafarki ( ba'diniyyah / ha'ki'ka ) sun 'boye magana acikin matakai na ke'bantaccen Tauhidi ( shine matakan tauhidi da muka ambata daga shehu Tijjani a rubutunmu na biyu a wannan matashiya , inda ya kasa mutane gida uku , ya sanya masu 'daukan komai a matsayin Allah a matsayin cikakku ke'bantattu , masu bautan Allah kuma a matsayinsu na halittu bayi ( mabiya Annabawa ) , sai ya sanya su a matsayin jahilai marasa fahimta !) , domin tausayawa ga 'daukacin jama'ar musulmai , kuma domin sassautawa ga masu jidali cikin shamakantattu ( mabiya Annabi Muhammad , wa'danda aka shamakancesu daga ganin komai a matsayin Allah ) , kuma domin ladabi ga ma'abota wa'dannan zantuka daga manya_manyan masana Allah "
Ga nan lafuzzansa :
"أخفى الكاملون من أهل الطريق الكلام في التوحيد الخاص شفقة على عامة المسلمين ، ورفقا بالمجادل من المحجوبين ، وأدبا مع أصحاب ذلك الكلام من أكابر العارفين "
( جواهر المعاني ، ١/١٤)
Wa'dannan bayanai na Shehu Tijjani duka suna tabbatar da cewa lallai suma sun yarda da cewa matafiyarsu daban da matafiyar musulunci ; saboda abunda addininsu ya 'kunsa na miyagun A'kidu da suke warware a'kidun musulunci daga tushensa , don haka basu da mafita wurin ribatar musulmi zuwa ga tafarkinsu sai ta hanyar munafunci ; ta hanyar 'boye ha'ki'kanin tafarkinsu da bayyana sa'banin ha'ki'kaninsa .
A rubutunmu na gaba zamu cigaba da kawo zantukan shuwagabannin Tijjaniyyah wa'danda su ka raineta bayan shehu Tijjani ; inda su ma suke tabbatar da abunda ya tabbatar na wajibcin 'boye sirrikansu akan mabiya daga gamayyar al'ummar musulmi .