DAGA INA MATSALAR TAKE (13) ?
A rubuce_rubucen da su ka gabata , mun yi bayanin ha'ki'kanin a'kidu na 'Dari'kar tijjaniyyah na allantar da waliyyai da Shehinnai , kai har da ma allantar da dukkan halittu , da halatta alfasha da munkarai , da lalata shari'ar musulunci . Duka wannan mun tabbatar da shine ta hanyar kawo maganganun jagororin 'dari'kar wa'danda su ke tabbatar da hakan ; tun daga kan Shehu Tijjany zuwa kan Shehu Ibrahim Nyass , da sauran turaku na 'dari'kar wa'danda su ka zo bayansa .
Babu shakka wa'dannan a'kidu da aka gina 'dari'kar Tijjaniyya akansu a'kidu ne na kafirci ; musulmi sun yi ijma'i akan kafircin masu 'dauke da wa'dannan a'kidu _ kamar yanda bayani ya gabata akan haka a rubutunmu na farko akan wannan matashiya _ , hatta su ma kansu Shehinnan Tijjaniyyar sun tabbatar da cewa wa'dannan miyagun a'kidu da suke 'dauke da su sun mayar da su kafirai bisa ma'auni na shari'ar musulunci , ka'dai zasu barranta da kafirci ne a sa'banin ma'auni na shari'ar musulunci ; wato a ma'auninsu na addininsu na ha'ki'ka ( ba'diniyyah )
Shehu Ibrahim Inyass da kansa ya yanke hukunci na kafirci _ bisa ma'auni na shari'ar musulunci _ ga dukkan wanda yake 'dauke da wa'dannan miyagun a'kidu nasu na allantar da halittu da halatta kashe Annabawa , amma kuma ya ce a addininsu na ha'ki'ka ( ba'diniyyah ) ,mai wa'dannan a'kidu mumini ne , a musulunce ne yake kafiri !!
Shehu Inyass yana bayanin ma'anar " fana'i " a sufance sai yake cewa :
"Lallai samuwan wani halitta bayan samuwar Allah ba shine yake shamakance muridi daga ganin Allah ba , Allah ya fi 'karfin haka ( wato bai yiwuwa a ce akwai Allah , kuma akwai wani halitta koma bayan Allah , a'a dukkan samammen abu Allah ne ! ) .
A'a babu abunda yake shamakance muridi daga ganin Allah sai mummunan tunani da muridin yake yi na yiwuwan samuwar wani samammen abu koma bayan Allah , idan Allah ya so ya za'bi bawansa sai ya kawar masa da wannan mummunan tunani , sai ya zama baya ganin akwai wani abu da yake shamakance shi daga ganin Allah , to daga nan ne Tsantsan gaskiya zata zo masa ; daga nan ba zai 'kara ganin wani samammen abu ba face Allah , ba zai 'kara 'daukan kansa ba face a matsayin Allah . A wannan matakinne sai muridi ya ce ga kansa : babu abun bauta sai ni ka'dai " .
Dukkan wanda ya kai wannan mataki kafirine bisa shari'ar musulunci , saboda ya kore dukkan sunayen Allah da sifofinsa , kuma ya halatta kashewarsa ga Annabawa . Ammafa bisa addinin Haqiqa shine ma mumini , saboda ya tabbatar da wa'dannan ababe ne bisa addinin haqiqa , kuma kashewarsa ga Annabawa kisa ne bisa haqqi ( sun cancanci kisanne ) .
Wannan mataki , mataki ne mai girman garari , saboda gararinsa akan a'kidune , acikinsa akwai abunda yake yahudantarwa da kiristarwa da majusarwa "
Ga nan bayanansa da bakinsa :
" والجذب هو الوصول والفناء والفتح ، تحقيقه : أن الحق جل وعلا ما حجبه عن المريد وجود موجود معه ، تعالى عن ذلك علوا كبيرا ، بل ما حجبه إلا توهم وجود موجود معه ، فإذا أراد الله اصطفاء عبده ،_ جعلنا الله من المصطفين الأخيار بمنه وكرمه _ رفع عنه ذلك الوهم ، فلا يرى شيئا يحجبه عن الحق ، وذلك فناء في محو " يمحو الله ما يشاء ويثبت " ، فحينئذ يأتيه صريح الحق ، فلا يرى وجودا إلا الله ، ولا يرى نفسه سواه ...
وفي هذا المقام يقول : " لا إله إلا أنا وحدي " .
وصاحب هذا المقام كافر شرعا ، لنفيه الأسماء والصفات ، وقتله الأنبياء ، وهو المؤمن حقيقة ، وقتله الأنبياء قتل بالحق لا بغير الحق ، و هذا المقام عظيم الغرر لأن غرره على العقائد ، ففيه ما يهود وينصر ويمجس "
( مجموعة التعريف بالشيخ إبراهيم وفيضته ومقدميه ، للشيخ محمد ولد الشيخ عبد الله التيجاني الإبراهيمي ، ٣٤٣)
Acikin wa'dannan bayanai na Shehu Ibrahim Inyass zamu fitar da ababe kamar haka :
1. Fana'i a wurin sufaye wani mataki ne wanda duk wanda ya kai gareshi , to ya tsallake mataki na halitta ; shima ya zama Allah , kuma dukkan samammun abubuwa su ma Alloline .
Sannan kuma wanda ya taka wannan matsayin ya na iya kashe Annabawa saboda awurinsa su masu laifine da suka cancanci akashesu !!
Wannan bayani na Inyass zai yayewa da yawan mutane mamaki da suke yi na samuwan masu zagin Annabi daga cikin mabiya Tijjaniyyah , to shi Inyass ba ma maganar zagi yake yi ba , a'a shi maganar kisa yake yi gaba daya bisa cewa Annabawan sun cancanci kisan !!
Wannan mataki na " fana'i " a syfanci shine matakin da duk wani muridi a 'dari'kanci yake nufin isa zuwa gareshi ; duk fafutukan da yake yi na tarbiyya ta sufanci wanda muqaddimi ya ke 'dorashi akanta , duka yana yi ne domin isa zuwa ga wannan matsayi ; matsayin sa'bulewa daga bautantaka zuwa allantaka !!
Duk wanda yake muqaddimi a 'dariqar Tijjaniyya a bisa shari'arta dolene ya 'ketare wannan mataki na fana'i , saboda sun shar'danta acikin littattafansu na koyon shari'ar addininsu cewa dolene muqaddimi ya zama Arifi , shi ko Arifi shine wanda Allah yake bayyana acikin jikinsa , kuma yake daukan dukkan halittu a matsayin alloli !!
Don haka , a bisa shari'ar Tijjaniyya , duk wani muqaddimi , da ma wanda ba muqaddimi ba , amma ya yi tarbiyya ta Tijjaniyya ya yi wusuli ; dukkansu su na qudurta allantuwar Kansu , kuma su na qudurta halaccin kashe Annabawa da manzanni da halaccin dukkan muharramai bisa addininsu na ha'ki'ka ( ba'diniyyah ) .
2. Shehu Ibrahim ya tabbatar da cewa : dukkan wanda yake 'dauke da wannan a'kidar ta su ; kafiri ne bisa shari'ar Musulunci , amma kuma bisa addinin haqiqa shine ma mumini !
Wannan ya tabbatar maka cewa su awurinsu akwai shari'a ta musulunci ; shari'a Annabi Muhammad da mabiyansa , sannan kuma akwai addini na haqiqa ; wacce take akasin Shari'ar Annabi ta ko wace fuska ; Abunda yake shirka a addinin Annabi , to shine tauhidi a addinin haqiqa , abunda kuma yake tauhidi a addinin Annabi Muhammad to shirka ne a addinin haqiqa , wajibobi da mustahabbobi a addinin Annabi Muhammad dukkansu muharramai ne a addinin haqiqa , hakanan muharramai a addinin Annabi Muhammad su ne halal a addinin haqiqa .
Babu shakka addinin haqiqa shine kishiya ga addinin Annabi Muhammad ta ko wace fuska , shine haqiqanin addinin Ba'diniyyah wanda mabiyansa su da kansu suka yarda cewa ba addinin Annabi Muhammad suke yi ba , wannan shine haqiqanin addinin Iblis . Lallai ba abun mamaki bane mabiyin wannan addini ya fito ya zagi Annabi Muhammad kamar yanda Shugaban addinin nasu Iblis ya fito qarara ya yiwa Allah fitsara !!
3. Inyass ya yarda cewa a shar'ance masu miyagun aqidunsu ba musulmai bane , don haka muma zamu cigaba da zantar da wannan hukunci na musulunci akan masu wannan aqida .
A rubutunmu na gaba zamu yi bayanin yanda jagororin Tijjaniyya suke wasici da 'boye wa'dannan aqidu nasu ga jama'ar da basa kan tafarkinsu .