DAGA INA MATSALAR TAKE ?(12)
A rubutunmu na fitowa ta sha 'daya , mun kawo bayanai daga wasu malaman sufanci , inda su ka tabbatar da cewa : lallai bauta tana iya saraya daga bawa matuqar ya samu tarbiyyah ta sufanci ya isa zuwa ga haqiqah , ya gano cewa lallai komai ma Allah ne , kuma dukkan ayyuka da bawa yake aikatawa to bisa haqiqa Allah ne yake aikatawa ba bawa ba .
Sufaye sun fa'di wasu sifofi masu yawa akan mutumin da ya yi tarbiyya ta sufanci ya samu fatahi , wanda wa'dannan sifofin duka su na nuni akan yanda shi mutumin ya ke qetare matakin aikata zunubi ; ta yanda zai wayi gari dukkan ayyukansa daidai ne , koda kuwa a zahiri ana ganin ayyukan amatsayin zunubbai to bisa haqiqa ba zunubbai bane , mahajubai wadanda basu samu tarbiyyar sufanci ba su ka gano haqiqa sune kawai suke ganin sa'bawar ayyukan ga shari'a .
Daga cikin sifofin da suke fa'di akwai kamar haka :
1. Su na cewa duk mutumin da ya samu fatahi bayan ya yi tarbiyyan sufanci ; wahayi yana sauka akansa , kuma ana umartansa da biyayya ga wannan wahayi , don haka , koda ka ganshi yana aikata wani aikin sa'bo , to a shari'ar musulunci ne ( shari'ar gama-gari) aikin yake a matsayin sa'bo , amma shi wannan mutumin awurinsa aikin ba sa'bo bane ; saboda shi yana aiki ne da wani wahayi ke'bantacce na musamman wanda aka ke'banceshi da shi aka halalta masa wannan al'amari . Don haka , shi ba akan shari'ar Annabi Muhammad yake ba , a'a , shi yana gudana ne akan haqiqa , don haka ba daidai bane aringa auna ayyukansa da shari'ar Annabi Muhammad , ballantana kuma a ce ya yi zunubi !!
Shehu Umar alfuty yana cewa :
" Lallai duka ma'abota fatahi ( wa'danda su ka yi tarbiyyar sufanci su ka tsallake shari'a su ka isa zuwa haqiqa ) su na ganin mala'iku , kuma mai kamala a tsakaninsu Mala'ika yana saukar ma sa da umarni da hani , amma hakan baya lazimta cewa shi ma'abocin shari'a ne "
" إن جميع أهل الفتح يشاهدون الملائكة ، والكامل بينهم ينزل عليه ملك بالأمر والنهي ، ولا يلزم من ذلك أن يكون ذا شريعة "
( رماح حزب الرحيم ، ٣٣٦/١)
A wani wuri kuma yana magana akan ma'abota fatahi sai yake cewa :
" Basa furuci sai da abunda suke gani ( daga wurin Allah ) , kuma suna kar'ban ke'bantacciyar doka ne ( kai tsaye ) ga ke'bantattu daga wurin Allah da kuma wurin Annabi Muhammad , wanda ke'bantacciyar dokar bata shafan gama_gari ( mabiya shari'ar Annabi Muhammad ) , saboda shi Annabi Muhammad yana bayar da gamammiyar doka ne ga 'daukacin al'umma alokacin rayuwarsa ; idan ya haramta wani abu , to haramcin yana aiki akan kowa , hakanan idan ya farlanta wani abu , farlancin yana shafan kowa , haka dai abun yake acikin dukkan hukunce_hukunce na shari'a .
Amma daga lokacin da Annabi ya bar duniya _ wanda rayuwarsa a can daidai take da rayuwarsa a duniya _ , sai ya zama yana bayar da ke'bantacciyar dokarsa ga ke'bantattu ; wanda wannan ke'bantacciyar dokar bata da alaqa da gamammiyar doka wacce aka saukar da ita ga gama_gari , ita wannan ta yanke da mutuwarsa (s.a.w) "
" لا ينطقون إلا بما يشاهدون ، ويأخذون عن الله تعالى وعن رسوله الأحكام الخاصة للخاصة ، لا مدخل فيه للعامة ، لأنه كان صلى الله عليه وسلم يلقي الأحكام العامة للعامة في حياته ؛ فإذا حرم شيئا حرمه على الجميع ، وإذا فرض شيئا فرضه على الجميع ، وهكذا سائر الأحكام الشرعية ، فلما انتقل إلى الدار الآخرة _وهي كحياته سواء _ صار يلقي إلى أمته الأمر الخاص للخاص ، ولا مدخل للأمر العام للعام فإنه انقطع بموته صلى الله عليه وسلم "
( الرماح ، ٣٣٦/١)
Daga bayanan wannan mutumin zamu fahimci abubuwa kamar haka :
* Shari'ar da Annabi Muhammad ya zo da ita , wacce Allah ya yi masa wahayinta tsawon shekaru ashirin da uku zuwa ga dukkan mutane da Aljanu ; wannan shari'a ce ta gama_gari , tana aiki ne ga wanda bai yi tarbiyya ta sufanci ba , kuma wannan shari'ar ta yanke da mutuwar Annabi Muhammad .
* Akwai doka ta musamman ke'bantacciya da take sauka ga wasu ke'bantattu ; su ne wa'danda suka yi tarbiyya ta sufanci su ka keta shamakin da ke tsakaninsu da Allah , su wa'dannan dokarsu bata shafan gama_gari , kamar yanda shari'ar gama_gari bata shafansu !!
Da wannan bayani na wannan mutum zamu fahimci cewa : a bisa doka ta sufanci ; dukkan wanda ya samu fatahi , to dukkan abunda yake haramta a shari'ar musulunci to shi yana halalta gareshi , saboda shi ba shari'ar musulunci yake runsunamawa ba , a'a , shi wata sabuwar doka yake bi wacce ba ta musulunci ba .
Wannan ya sa sufaye suke yekuwa cewa : bai dace ba aringa auna ayyukan waliyyi da shari'ar musulunci ; saboda shi wannan shari'ar ba itace shari'ar da yake kai ba .
Shehu Abdulaziz Addabbag yana cewa :
" لا ينبغي أن ينظر إلى ظاهر الولي ويوزن عليه ، فيخسر الوازن دنيا وأخرى "
"Bai dace ba aringa kallon zahirin waliyyi a ringa aunashi ( da shari'a ) , idan mutum ya yi haka , to sai ya yi hasara duniya da lahira "
( الرماح ، ٣٢٥/١)
A wani wurin kuma yake cewa :
" علامة المحبة الصافية سقوط الميزان من المريد على الشيخ ، حتى تكون أفعال الشيخ وأقواله وجميع أحواله كلها موفقة مسددة في نظر المريد "
"Alamar nagartacciyar soyayyar muridi da Shehi ; ya saryarwa da shehinsa ma'aunin shari'ar musulunci ; ta yanda zai ringa ganin dukkan ayyukan shehinsa da zantukansa , da dukkan halayensa ; daidai suke sun dace "
( الرماح ، ٣١٩/١)
2. Suna ganin bai yiwuwa mutumin da ya samu fatahi ya yi zunubi ma gaba 'daya , saboda shi har kullum yana tare da Allah ; yana kallonsa yana hira da shi , don haka , ba zai yiwuba ace wai yana zunubi , sai dai kawai mahajubi mabiyin shari'ar gama_gari ya ringa ganin an sa'bawa shari'ar da yake kai , amma bisa haqiqa babu wannan magana !!
Shehu Addabbag yana cewa :
" إن أهل الفتح الكبير يغفر لهم ما تقدم من ذنبهم وما تأخر ، وحسناتهم مقبولة ، وسيئاتهم كلها ترجع حسنات إذا فعلوها قبل الفتح ، وأما بعد الفتح فإنها لا تصدر منهم معصية ؛ لأنها لا تصدر إلا من المحجوبين ، وهم رضي الله عنهم في مشاهدة الحق دئما ، ولأجل أن مشاهدة الحق تمنع من المعصية "
" Lallai ma'abota babban fatahi ana gafarta mu su abunda ya gabata na zunubansu da abunda ya jinkirta , kuma kyawawansu dukkansu kar'ba'b'bune , munanansu kuma dukkansu za su koma kyawawa idan sun aikatasu kafin samun fatahi , amma bayan samunsu ga fatahi , to ai dama bai yiwuwa sa'bo ya fito daga garesu ; saboda ai sa'bo baya fitowa sai daga mahajubai ( mabiya shari'ar Annabi Muhammad ) , amma su kam ma'abota fatahi ai har kullum suna cikin kallon Allah ne , kuma ai kallon Allah yana hana aukawa cikin sa'bo "
( الإبريز ، ٦٥٩)
Shehu Umar alfuty shima ya tabbatar da wannan batu , yana cewa :
" koda ka ga sa'bo ya bayyana ga wanda ya samu fatahi , to kawai kaine kake ganin hakan a zahiri , amma a haqiqa abun ba haka yake ba , saboda halin da yake ciki na dawwamar ganin Allah , wannan halin zai hanasa sa'bo "
" فالمخالفة إن ظهرت عليه فإنما هي بحسب ما يظهر لنا ، لا في الحقيقة ، فإن المشاهدة التي هو فيها تأبى المخالفة "
( الرماح ، ٢٦٨/١)
3. Su na cewa : wanda ya samu fatahi dukkan abunda ya aikata daidai ne ;yana aikata ayyukane gwargwadon halin mutanen da suke tare da shi ; idan ya zama yana cikin mashaya giya da zinace_zinace , da luwadi da sauran alfasha , to shima kawai sai ya dinga shan giya da caca da luwa'di da zina da kisa . Ammafa duka wa'dannan miyagun ayyuka shi ba haramun bane gareshi , a'a , ya aikatasu ne kawai domin ya bayyana haqiqanin halin mutanen da yake tare da su domin su gyara halinsu , amma shi ba sa'bo ya yi ba , shi mai wa'azi ne a fakaice !!!
Shehu Addabbag ya ce :
" Idan Allah ya nufi ta'bewar wasu mutane da rashin amfanuwarsu ; sai ya hore mu su wani waliyyi da zai ringa aikata irin munanan ayyukan da suke ciki na sa'bo , kawai sai su ringa tsammanin shima waliyyin 'dan ayarinsune , amma al'amarin ba haka bane , yana ma iya yiwuwa a al'amari na walittaka ka ga waliyyi ya zauna ya na shan giya tare da mashaya giya , sai su yi tsammanin ko shima mashayin giya ne , amma yanda al'amarin yake shine : ruhin waliyyin ne ta riki'de acikin wata sura daga wasu surori , sai ruhin nasa ta bayyana abunda wannan surar ta bayyana , amma bisa haqiqa babu wani sa'bo da ya aikata "
" و إذا أراد الله شقاوة قوم وعدم انتفاعهم بالولي سخره الله فيما هم فيه من قبح ومخالفة ، فيظنون أنه على شاكلتهم ، وليس كذلك ، حتى أنه يتصور في طور الولاية أن يقعد الولي مع قوم يشربون الخمر وهو يشرب معهم ، فيظنون أنه شارب الخمر ، وإنما تصورت روحه في صورة من الصور وأظهرت ما أظهرت ، وفي الحقيقة لا شيئ "
( الإبريز ، ٤٧٣)
A wani wurin kuma ya ce :
" Idan Allah ya nufi ta'bar da wasu mutane ; sai waliyyi ya bayyana tare da su da inuwar zatinsa , sai ya ringa aikata miyagun ayyukan da suke aikatawa ( wato ba shine yake yin zunuban ba , a'a inuwarsa ce take tarayya da mutanen wurin aikata alfasha !!) "
" وإذا أراد الله شقاوة قوم ظهر الولي معهم بظل ذاته ، وجعل يرتكب ما يرتكبون "
( الإبريز ، ٤٧٤)
A wani wuri kuma ya ce :
" lallai babban waliyyi yana bayyana ga mutane yana aikata sa'bo , amma bisa haqiqa shi ba mai sa'bo bane , gaskiyan lamari shine ; ruhinsa ne ya shamakance zatinsa , sai ruhin ta bayyana a sura na zatinsa , don haka idan aka ga surarsa tana sa'bo , to ba sa'bo bane bisa haqiqa ; saboda alal misali : idan surarsa ta 'dauki haramun zata ci , to da zaran ta sanya abun a bakinta , to zata jefar da wannan abunne zuwa wani wuri ( amma a 'ba'dini ) , abunda ya sa wannan waliyyin ya aikata irin wannan sa'bo na zahiri ; shine ta'bewar mutanen da yake tare da su "
" إن الولي الكبير فيما يظهر للناس يعصي وهو ليس بعاص ، وإنما روحه حجبت ذاته فظهرت في صورتها ، فإذا أخذت في المعصية فليست بمعصية ، لأنها إذا أكلت حراما مثلا فإنها بمجرد جعلها في فيها فإنها ترميه إلى حيث شاءت ، وسبب هذه المعصية الظاهرية شقاوة الحاضرين "
( الإبريز ، ٤٧٥)
Shehu Umar Alfuty shima ya tabbatar da wannan al'amari , inda yake cewa :
" lallai cikakken arifi idan wani sa'bo ya auku daga gareshi , to a hoto ne kawai ; amma ba a haqiqa bane , kawai dai ya nufaci jarabtar mutanen da suke tare da shi ne sai ya aikata wannan sa'bon ( amma bisa haqiqa shi ba sa'bo ya aikata ba ) "
" فالعارف الكامل إذا وقعت منه مخالفة فهي صورية غير حقيقية ، قصد بها امتحان من شاهدها واختباره "
( الرماح ، ٢٦٨/١)
4. Su na cewa : waliyyi yana aikata alfasha kamar shan giya , da zina , da luwa'di , da kisan kai ; amma shi hakan duka halal ne gareshi , saboda ya aikata ne domin ya kiyaye ikhlasinsa ; ya 'boyewa mutane haqiqanin halinsa na nagarta ta hanyar bayyana miyagun ayyuka a zahiri , domin kada mutanen su gane cewa shi waliyyine su ringa binsa , saboda hakanema gane waliyyai ya zama al'amari mai wahala ; domin waliyyan sun koma su ne mazinata , mashaya giya , Yan luwadi , 'barayi , ma'barnata ; duk domin su kiyaye ikhlasinsu !!
Shehu Tijjani ya tabbatar da wannan batu , yana bayanin hanyoyin da waliyyai suke amfani da su wurin gujewa daga tarayya da gama_garin mutane domin kiyaye ikhlasinsu , sai yake cewa :
" Wani lokaci gama_garin mutane su kan shaqi qamshin isowar waliyyai ta bayan shamaki , sai su zabura domin su ratayu zuwa garesu domin samun buqatunsu , sai su kuma waliyyan su rikitar da gama_garin ta fuskoki daban_daban , domin su kiyaye kansu daga gama_gari ; ta hanyar miyagun al'amura na zina , da mummunan qarya , da shan giya , da kisan rai , da sauran miyagun ayyuka ma su halakarwa , amma ayyukan da waliyyan suke aikatawa na sa'bo , kawai wasu surori ne na gaibi ; bisa haqiqa ba wai abubuwan sun faru bane ; kawai dai wasu ababene da ake hasashensu a qwaqwalwa , wanda mahajubi yake ganinsu a haqiqa su na faruwa , sai waliyyan su ringa aikata miyagun ayyuka a shar'ance acikin wa'dannan surori , ammafa bisa haqiqa babu abunda su ka aikata , kawai dai sun kiyaye kansune daga gama_gari ta hanyar aikata wa'dannan miyagun ayyuka domin su kiyaye matsayinsu "
" وربما شم العامة روائح وصولهم من وراء الحجب ، فنهضوا إلى التعلق بهم فيما يريدونه من أغراضهم ، فخلط عليهم العارفون بوجوه من التخليط استتارا عن العامة بإظهار من أمور من الزنا ، والكذب الفاحش ، والخمر ، وقتل النفس وغير ذلك من الدواهي التي تحكم على صاحبها أنه في سخط الله وغضبه ، والأمور التي يقتحمها العارفون في هذا الميدان إنما يظهرون صورا من الغيب لا وجود لها في الخارج ، إنما هي تصورات خيالية يراها غيرهم حقيقية ، فيفعلون في تلك الصور أمورا منكرة في الشرع ، وهم في الحقيقة لم يفعلوا شيئا ، فاستتروا بذلك عن العامة حفظا لمقامهم "
( جواهر المعاني ، ٦٧/١)
A jumlace , Sufaye su na qudurta halaccin komai ga wanda ya samu fatahi bayan tarbiyya ta sufanci , ta fukoki kamar haka :
_ Ta fuskar ke'bantaccen wahayi na musamman Wanda yake sauka ga ke'bantattu ma su fatahi ; wanda dokokin wahayin suka sa'bawa gamammiyar shari'ar Annabi Muhammad .
_Ta fuskar zamantakewarsu ga Allah ; ta yanda suke rayuwa tare , suke kallon juna , su na tattaunawa da juna , wanda wannan kuma yana hukunta kanguwa daga sa'bo ga Wanda ya taka wannan matsayi .
_ Ta hanyar bayyana sa'bo a zahiri domin bayanin haqiqanin halin mutanen da ake tare da su domin wa'azi garesu , ba wai don shi ma'abocin fatahin zunubi yake yi ba .
_ Aikata alfasha domin kiyaye ikhlasi .
Wa'dannan su na daga cikin hanyoyin da sufaye suke bi wurin halalta ayyukan sa'bo ga wanda ya samu tarbiyyah ta sufanci ya kai zuwa haqiqa . Don haka , aduk lokacin da wasu matasa ko shehinnai su ka bayyana , suke da'awar halalta ababen da Allah ya haramta a shari'ar musulunci , bisa da'awar cewa su sun riga sun isa zuwa ga haqiqa ; don haka su komai halalne a garesu ; to babu shakka wa'dannan mutane sune halaltattun Tijjanawa , sune suke aiki da haqiqanin abunda ya tabbata a 'dariqar Tijjaniyyah .
A rubutunmu na gaba zamu tattauna akan wasici da jagororin Tijjaniyyah su ka yi ga mabiyansu ; na 'boyewa gamayyar musulmi haqiqanin addininsu na komai Allah , da halatta muharramai na shari'a , da tabbatarwa da su ka yi akan kansu cewa su kafiraine bisa shari'ar Musulunci .