DAGA INA MATSALAR TAKE ? (11)
Daga cikin abunda muke gani yanzu daga wasu jama'a cikin 'dariqar Tijjaniyya ; akwai qudurcewarsu ga halascin komai , da watsarwarsu ga shari'ar musuluci bisa hujjar cewa su sun riga su gano haqiqa ; sun gano cewa Allah shine yake aikata ko wane irin aiki , sawa'un ayyukan alheri ko na sharri , don haka , tuddan dai su sun gano wannan al'amari , to babu abunda zai haramta awurinsu ; dukkan abunda za su aikata halal ne , saboda Allah ne yake aikatawa . Don haka Shari'ar da manzanni su ka zo da ita , shari'a ce ga mahjubai wa'danda aka shamakancesu daga gano wannan haqiqa , don haka , duk wanda ya yi tarbiyya ta sufanci har ya samu fatahi ( ya zama ya gano cewa kowa ma Allah ne , kuma Allah ne ke aikata komai ) , to shi ya riga ya tsallake shari'ar manzanni , ya tsallaka zuwa ga haqiqa ; matakin da babu haram acikinsa , babu wani abun bauta makadaici da kowa yake bautamawa .
Shehu Abubakar Atiku ya yi bayanin ma'anar wannan mataki na haqiqa inda yake cewa :
" والحقيقة نظره لبواطن الأمور ، وشهود الفعل من الله تعالى "
"Haqiqa itace kallon ma'abocinta ga ba'dinin al'amura , da halartowarsa cewa dukkan ayyuka su na fitowane daga Allah "
( مناهل الرشاد ، ٤٩_٥٠)
Wannan aqida ta watsi da dokokin shari'ar musulunci na umarni da hani bisa hujjar cewa an riga an gano haqiqa , tsohuwar aqidace acikin harka ta Sufanci , an sameta tun a qarni na uku , daga cikin wa'adanda aka jingina mu su wannan aqida akwai Husain bun Mansur Alhallaj , daga bayansa kuma aqidar ta yadu acikin mabiya harkar sufanci .
Abul Hasan Al'ash'ary wanda ya rayu a qarni na uku zuwa qarni na hudu , ya tabbatar da cewa lallai acikin Sufaye akwai masu aqidar watsar da dokokin Addinin Musulunci na umarni da hani , da halastawarsu ga dukkan komai , ga maganarsa nan kamar haka :
" وفي النساك من الصوفية من يقول بالحلول ، وأن الباري يحل في الأشخاص ، وأنه جائز أن يحل في إنسان وسبع وغير ذلك من الأشخاص .
وأصحاب هذه المقالة إذا رأوا شيئا يستحسنونه قالوا : لا ندري لعل الله حال فيه ، ومالوا إلى اطراح الشرائع ، وزعموا أن الإنسان ليس عليه فرض ، ولا يلزمه عبادة إذا وصل إلى معبوده "
" A cikin ma su bauta daga Sufaye akwai wa'danda suke qudurta saukowan Allah acikin jikin halittu , kuma lallai Allah yana sauka acikin jikin mutum da dabbobi ma su kai bara , da ma wasu gangan jiki .
Ma su wannan aqida idan su ka ga wani abu da ya burgesu sai su ce : ba mu sani ba , wataqila Allah ne ya sauka acikinsa , sai su ka karkata zuwa ga watsi da dokokin Shari'a , kuma suka ringa cewa : lallai matuqar mutum ya sadu da abun bautansa , to babu wani farali akansa , kuma babu wata bauta da take lazimtarsa "
( مقالات الإسلاميين ، ٣١)
wannan bayani na Abul hasan Al'ash'ary yana tabbatar da cewa lallai wannan aqida ta komai halal ; tsohuwar aqidace acikin tafiyar Sufanci , kuma wa'danda aka sansu da wannan aqidar acikinsu sune dai masu dauke da aqidar allantar da halittu .
Kamar yanda muka Kawo daga Shehu Abubakar Atiku Sanka ; inda yake mana bayani akan ma'anar addininsu na haqiqa cewa ; shine mutum ya ringa kallon al'amura ta ba'dininsu , kuma ya ringa ganin cewa ayyukansa duka Allah ne yake yinsu . wannan mataki shine qofar fita daga shari'ar Allah gaba 'daya ; ta hanyarsa ne suke watsi da shari'a , su halastawa kansu komai , su ringa 'daukan kansu a matsayin Alloli masu zaman kansu , kuma wannan matakin shine mafi qololuwan mataki da mutum zai isa zuwa gareshi a harkar sufanci , kuma ma'aboda wannan matsayi sune kamulallu aharkar , kamar yanda Shehu Tijjani ya tabbatar da hakan a rubutunmu na biyu a wannan matashiya .
Su wa'dannan Mutane su na ganin cewa zaka bautawa Allah ne kawai kafin ka isa zuwa matakin cewa ai duka ayyukanka Allah ne yake yi , amma da ka isa zuwa wannan matakin to shikenan an na'de maka shari'a gaba 'daya , kuma daga lokacin an yaye maka dabaibayi na bauta , shikenan ka zama mai cikakken 'yanci !
Shehu Abdulaziz Addabbag yana qara tabbatar da wannan batu sai yake cewa :
" Shi mai bauta baya ku'buta daga bautan Allah sai alokacin da ya fara ganin cewa ai bautanma daga Allah take fitowa a bisa ba'dini , kuma wannan quduri ya dawwama acikin tunaninsa , amma idan wannan quduri ya faku daga barin tunaninsa ; ya koma yana ganin ai shine yake yin ibada ba Allah ba , to ba bu shakka ya fi kusanci zuwaga halaka sama da kusancinsa zuwa ga ku'buta "
" والعابد لا ينجو من عبادته إلا إذا كان يراها من ربه باطنا ، ويدوم ذلك على فكره ، فإن غاب ذلك عن فكره وجعل يراها منه فهو إلى العطب أقرب منه إلى السلامة "
( الإبريز ، ٣٩٣)
Bayanan wannan mutumi sun qunshi abubuwa kamar haka :
1. Bautan bawa ga mahaliccinsa sababine na halakar bawa , don haka ya kamata bawa ya samawa kansa hanyar tsira daga wannan halaka .
2. Bawa yana iya ku'buta daga bautan mahaliccinsa ; hanyar da zai bi ya kai zuwa ga haka kuma itace : ya ringa ganin cewa ayyukan da yake yi na bauta , Allah ne yake yinsu . Amma mutuqar baya ganin haka to babu shakka zai halaka !!
Wanann magana da wannan mutumi ya yi na cewa : matuqar bawa baya ganin cewa ayyukansa Allah ne yake yinsu ( ta yanda zai zo ya daina bauta ) , to zai halaka " , Shehu Ibrahim shima ya fa'di makamanciyar maganar , yana cewa :
matuqar akwai wani shamaki da yake shamakance bawa daga ganin cewa shima Allah ne , kuma ayyukansa Allah ne yake yinsu , to babu shakka akwai wani nau'i na azaba da zai samu bawa akan haka "
" ما لم يفن العبد في ذات الله تعالى لم يكمل إيمانه ، وما بقي حجاب فهنالك نوع من العذاب يلحق العبد ، ومهما حصل الحجاب حصل العقاب "
( جواهر الرسائل ، ٥٩/٢)
A jumlace dai , wannan mataki na haqiqa shine hanyar ficewa da bautantakan bawa ga mahaliccinsa zuwa qudurce allantuwar bawan, da ficewarsa daga dokokin da Manzan Allah ya zo da su . Duk wanda ya kai wannan matakin a sufanci to shine ya samu fatahi da irfani , ya yage shamakin da ke tsakaninsa da zama Allah , ya gano cewa komai ma Allah ne ; wanda ya kai wannan mataki to ya tsallake gadar bauta , ya haye matakin allantaka .
Amma wanda bai isa zuwa ga wannan mataki ba , shine suke kira mahajubi ; wanda aka shamakance shi daga gano haqiqa ; ya gane cewa komai Allah ne , dukkan ayyuka Allah ne yake aikatasu . wanda yake a wannan mataki shine gama_gari , mabiyin shari'ar manzan Allah , wanda bauta take lazimtarsa , dokoki na umarni da hani suke dabaibaye da shi !!
A rubutunmu na gaba zamu cigaba da kawo zantukan Malaman Tijjaniyyah akan wannan batu , inda suke tabbatar da cewa lallai akwai mutanen da suka fi qarfin bin shari'ar Annabi Muhammad , ta yanda komai yake zama halal a haqqinsu .
Allahu ya tsare mana Imanin Mu