DAGA INA MATSALAR TAKE ? (10)
Daga cikin abunda wasu daga cikin mabiya 'dariqar Tijjaniyya su ka ringa bayyanawa a kwanakin baya , wanda kuma wasu daga cikinsu su ka bayyana inkari akansu shine : fifitawarsu ga Shehu Ibrahim Inyaas akan Manzon Allah (s.a.w) !!
Babu shakka dukkan mai imani zai damu , kuma hankalinsa zai tashi idan ya ji mutumin da yake danganta kansa ga musulunci kuma yake qudurce irin wannan mummunan aqida , amma fa abunda ya kamata mu sani shine :
Tun asali fa dama can acikin Sufaye akwai jama'ar da su ke qudurce cewa : Waliyyi ya fi Manzo daraja !! , daga cikin wa'danda aka kiyaye wannan aqida daga garesu akwai Muhammad bn Araby Al 'Da'iy Al Makky , da sauran shuwagabannin Sufanci da su ka biyo bayansa su ka gudana akan magudanarsa a harkar sufanci .
Daga cikin Shuwagabannin Sufanci na baya_baya wa'danda suke 'dauke da wannan aqida akwai Shehu Abdul Aziz Addabbag ; wanda yake bango mai qarfi ga Sufayen da su ka zo bayansa , kamar Shehu Tijjany da wasunsa . Yana cewa acikin littafin da Almajirinsa Ahamd Mubarak ya rubuta dangane da shi :
" كل ما أعطيه سليمان في ملكه ، وما سخر لأبيه داود ، وأكرم به عيسى ، أعطاه الله وزيادة لأهل التصرف من أمة النبي صلى الله عليه وسلم ؛ فإن الله سخر لهم الجن والإنس والشياطين والريح والملائكة ، بل وجميع ما في العالم بأسرها ، ومكنهم على إبراء الأكمه والأبرص وإحياء الموتى "
" Dukkan abunda aka baiwa Annabi Sulaiman acikin mulkinsa , da abunda aka horewa mahaifinsa Dawud , da abunda aka karrama Annabi Isa da shi , to Allah ya bawa waliyyai masu jujjuya al'amuran halittu dukkan haka har ma da qari akansa ; saboda Allah ya hore mu su Aljanu da mutane da She'danu da Iska da Mala'iku , kai da ma dukkan halittun da su ke cikin duniya gaba 'dayanta , kuma ya ba su dama akan warkar da makafi da kutare da rayar da matattu "
( الإبريز من كلام سيدي عبد العزيز ، ٤١٧)
Acikin maganar wannan Mutumi zamu ga ya tabbatar da cewa halittu gaba 'dayansu tun daga kan Mala'iku da Annabawa da manzanni da sauran bil adama gaba 'dayansu , da ma dukkan halittu , dukkanninsu suna qarqashin wa'dannan waliyyanne da ya yi musu laqabi da ( Ahlut tasarrufi ) .
Kamar yanda tuntuni aka samu masu wannan aqida cikin sufaye , to hakanan an samu cikin Shehinnai mabiya 'dariqar Tijjaniyyah .
Shehinnan Tijjaniyyah tun daga kan wanda ya qirqiro 'dariqar ( Shehu Tijjany ) , har zuwa kan shehinnan cikin 'dariqar nasa su ma suna qudurce cewa : lallai akwai wasu waliyyai wa'danda su ka fi Manzanni daraja !!
Wa'dannan Shehinnai sun tabbatar da hakan ta hanyoyi daban _ daban ; wani lokaci su na fa'din hakan qarara , wani lokaci kuma su na fa'din zancen da ya ke lazimta wannan ma'ana .
Shehu Tijjani ya tabbatar da fifikon waliyyai akan Annabawa da Manzanni inda yake cewa :
" فالخليفة الولي أوسع دائرة في الأمر والنهي والحكم من الرسول الذي ليس بخليفة "
"Waliyyi halifa ( wanda yake amadadin Allah !! ) ya fi yalwan matsayi wurin umarni da hani da hukunci sama da Manzo wanda ba halifa ba "
( جواهر المعاني ، ١/١٥٨)
Daga wannan zance na Shehu Tijjani zamu ga yana bada qa'ida ne cewa : duk waliyyin da yake amadadin Allah _ kamar yanda su sufaye su ke qudurcewa _ to sama ya ke amtsayi akan Annabawa da Manzanni wa'danda su ba amadadin Allah su ke ba .
A wani wurin ma Shehu Tijjany ya fifita kansa ne da mabiyansa akan dukkan bil adama ; ya nuna cewa mutane baki dayansu sun qarar da rayuwarsu a banza sai dai kawai wa'danda su ke mabiya 'dariqarsa !!
Ga nan maganarsa kamar haka :
" أعمار الناس كلها ذهبت مجانا إلا أعمار أصحاب الفاتح لما أغلق "
( رماح حزب الرحيم ، ٣٩٩/٢)
Hakanan a wani wuri kuma yana cewa : Allah ya bashi wasu sirrika daga cikin saba'ul masani ( suratul fatiha ) , sirrikan da bai bawa Annabawa ba "
" أعطاني الله في السبع المثاني ما لم يعطه للأنبياء "
( رماح حزب الرحيم ، ٤١٣/٢)
Wannan magana ta biyu na Shehu Tijjany ta na nuna yanda shi yake 'daukan kansa a matsayi mafi 'daukaka ga matsayin Manzanni ; ta yanda yake zarce mu su acikin wani ilimi na shari'a .
Zancensa na farko kuma , gaba 'daya ma yana wofintar da dukkan bil adama ne ;ta yanda yake ganin babu wanda bai yi asarar rayuwarsa ba cikin mutane sai kawai wanda yake mabiyin 'dariqarsa !!
Babu shakka wannan magana ta wuce a ce yana fifita kansa akan wani manzo , a'a , sai dai a ce yana fifita mabiyansa ne akan dukkan bail adama !!
Shehu Inyass ya bi tafarkin Shehu Tijjani , ta yanda shima yake qudurce fifikon Shehu Tijjany akan dukkan manzanni ; ta yanda yake tabbatar da gabatuwan Shehu Tijjany akansu alokacin da dukkansu su ke bayansa ...
Ana danganta wata magana zuwa ga Shehu Abu Yazid Albis'damy ; wacce take nuna yanda yake gabatar da kansa akan Annabawa , wanda kuma akan wannan maganar da wasu maganganu daban da ake jingina masa wasu malamai suke kallonsa a matsayin Zindiqi .
Wannan maganar kuwa itace _wai _ yana cewa :
"غصت بحرا وقف الأنبياء بساحله "
" Na kutsa tekun da Annabawa su ka tsaya a bakin ga'barsa "
Wannan mummunan zance wanda ya qunshi fifita wani mutum akan Annabawa shine Shehu Inyass ya maimaitasa akan Shehu Tijjani dangane da matsayinsa tsakanin Manzanni !!
Yana cewa : Shehu Tijjany yana kutsawa cikin wani irin teku wanda manzanni suka tsaya can baya curko_curko
Da albarkatun Shehu Tijjani ne dukkan zuciyoyi suke sauyawa Su zama ni'imtattu tsaftatattu , Su koma kamar nuhasi "
"يغوص ودون ذاك البحر رسل ## وقوفا إرث إرس مثل آس
بفيض الختم يقلب كل قلب ## نضارا خالصا مثل النحاس
( تحفة أطايب الأنفاس ، ١٠٨)
Kamar yanda Inyaas yake ganin Shehu Tijjani a matsayin shine ja_gaba ga Manzanni , hakanan 'daya daga cikin almajiran Inyas shima yana ganin Shehu Tijjani a matsayin Shugabane ga Manzan Allah (s.a.w ) ; ta yanda yake 'daukan Annabi Muhammad a matsayin mabiyine ga Shehu Tijjani a cikin Tijjaniyya , Muqaddimine acikin dariqar kamar sauran muqaddimai wa'danda dukkansu su ke qarqashin Shehu Tijjany .
Shehu Abubakar Atiku sanka shine ya fa'di wannan maganar , yana cewa :
" والشيخ حقيقة في الطريقة سيدنا التجاني رضي الله عنه ، بل جده صلى الله عليه وسلم والمقدمون نواب له فقط "
"Bisa haqiqa Shehin 'dariqar Tijjaniyya shine shugabanmu Shehu Tijjany , bari ma , hatta kakansa manzan Allah da sauran muqaddimai dukkansu wakilan Shehu Tijjani ne kawai "
( مناهل الرشاد ، ١٠٦)
Wa'dannan maganganu na wa'dannan mutane duka su na nuna cewa Waliyyai _a game _sun fi manzanni daraja , kuma Shehu Tijjani _a ke'be _ ya fi Annabi Muhammad da sauran manzanni daraja .
Don haka , a yau idan mu ka ji wani batijjane ya fito yana fifita shehinsa akan Annabi Muhammad , to mu san da cewa hakan ba baqon abu ya zo da shi ba a Tijjaniyyah , a'a yana aiki ne da abunda yake tabbatacce acikin 'dariqar Tijjaniyyah .
A rubutunmu na gaba zamu yi bayani ne akan abunda wasu mabiya Tijjaniyyah suke bayyanawa na qudurcewarsu ga halaccin komai .