Subscribe Our Channel

 Yana daga cikin abin takaici a ce abin da yake a bayyane qarara ga musulmi amma kuma a samu wasu sashe na musulmi su makance da gangan wurin kin ganin wannan lamari , har hakan ya larurantar da nusar da mutane akan wannan lamari , irin wannan mummunan yanayi shi ya larurantar da malamai yin rubuce_rubuce musamman don su tabbatar da falalar Sahabbai , saboda an samu wadanda su ka makantar da kansu da gangan daga ganin falalar tasu . 


Mu ma yanzu wasu sun larurantar mana da magana akan wajibcin jibintar musulmi me zunubi akan Bayahude Kafiri da yake ta'addanci akan wannan musulmin . 


Za mu wadatu da kawo sababin saukar Ayoyi biyar din farko na Suratur Rum , se mu yi gajeren ta'liqi akansa . 


Ya tabbata acikin littafan Tafsiri da Hadisi da Sira ta hanyar ganganko ( tawaturi ) cewa Rumawa Nasara sun yi yaqi tskaninsu da Majusawa Farisawa , se Majusawa su ka yi nasara akan Nasara a yankin qasar Sham , se Mushrikan Quraishawa su ka yi farin ciki akan haka , saboda majusawa sun fi kusanci da su sama da Kiristoci Rumawa ; saboda su biyun Majusawan da Mushrikan dukkansu ba su da littafi , su kuma Musulmi se su ka yi baqin ciki akan nasarar Majusawan akan Kiristoci ; saboda Kiristocin sun fi kusa da Musulmi , saboda su ma Kiristoci su na da Littafi kamar Mususulmi . Bayan faruwan wannan lamari se Surarur Rum ta sauka , acikinta Allah yake yi wa Musulmi bushara da samun nasarar Kiristoci akan majusawa , kuma yake umurtansu da su yi farin ciki da wannan nasarar saboda kusancin Kiristoci da su idan aka kwatantasu da Majusawa . 


Ibnu Taimiyyah yana magana akan sababin saukar surar se ya ke cewa : 


" فإنها نزلت كما استفاض في التفسير والمغازي والحديث في اقتتال الروم والنصارى والفارس والمجوس، وكانت المجوس قد غلبت النصارى على أرض الشام وغيرها ، فغلبت الروم ، وفرح بذلك مشركو قريش ، لأن المجوس إليهم أقرب من النصارى ، لأن كلاهما لا كتاب له ، واغتم لذلك المؤمنون ،لأن النصارى إليهم أقرب ؛ لأنهم أهل كتاب " 


(الفتاوى ، ٣٢/١٨٨)


Al Imamut Tirmizy ya ruwaito da isnadinsa HASAN daga Ibnu Abbas yana bayani game da ayoyi biyun farko na Suratur Rum se yake cewa : 


" كان المشركون يحبون أن يظهر أهل فارس على الروم ؛ لأنهم وإياهم أهل أوثان ، وكان المسلمون يحبون أن يظهر الروم على فارس ؛ لأنهم أهل الكتاب " 


(جامع الترمذي ، ٣١٩٣) 


Ababen lura : 


1. Annabi da Sahabbansa sun yi baqin ciki akan nasarar Majusawa akan Kiristoci , kuma daga baya sun yi farin cikin nasarar Rumawa akan Majusawa .


2. Annabi da Sahabbansa sun so nasarar Kiristoci ne akan Majusawa saboda kusancinsu da kiristocin ta fuskar addini . Hakanan sun yi baqin cikine da nasarar Majusawa akan Kiristoci saboda rashin alaqa kwata_kwata tsakaninsu da majusawan ta fuskar addini . 


Wannan yana nuna cewa adawar da musulmi ze yi ga Kafirai adawace mataki_mataki ; gwargwadon girman kafircin Kafiri da fajircinsa gwargwadon adawarka da qiyayyarka gareshi . 


3. Wannan yana nuna cewa Musulmi ze yi fatan nasara ga Kafiri me sauqin adawa da kafirci akan Kafiri me zazzafar adawa da girman Kafirci . 


Idan mun fahimci haka za mu fahimci wajibcin jibintar Musulmi a yayin da suke yaqi tsakaninsu da Kafirai ko da kuwa musulmin masu zunubai ne da miyagun bidi'o'i da dabi'u . 


Wannan ya sa mazhabar Ahlus Sunnah ta gudana akan temakon shugaba musulmi wurin yaqin kafirai ko da kuwa Shugaban fajirine fasiqi Azzalumi ; saboda maslahar temakonsa akan yaqan Kafirai ta fi mafsadar zamowansa fasiqi azzalumi , kuma yana da haqqin jibintar sauran musulmi gareshi sabanin su Kafiran . 


Shaikhul Islam yana cewa :


فالأقل ظلما ينبغي أن يعاون على الأكثر ظلما ، فإن الشريعة مبناها على تحصيل المصالح وتكميلها وتعطيل المفاسد وتقليلها بحسب الإمكان " 


( منهاج السنة ، ٣/١٥٨)


Da wannan za mu fahimci wauta da jahilcin wadanda suke tawaqqufi ko goyon bayan zaluncin da Yahudawa suke yi wa musulmi a qasar Filasdin na qwace mu su qasa , da yi musu kisan kiyashi wai saboda acikin musulmin Filasdin din akwai yan ikhwan da yan Shi'a ! 


Lazimin wannan mugun ra'ayin shine : ba za a temaki musulmi ba akan Kafiri se idan Musulmin ya zama kamili Salafy ! Amma idan ya zama Dan bidi'a to ba za a temakeshi ba akan Kafiri ! 


Ka ga lazimin wannan ra'ayi na jahilci shine haqiqanin ra'ayin Shi'a Rafidha da Mu'tazila , da suke cewa : ba za a temaki musulmi ba akan yaqan Kafirai se idan Musulmin ya zama ma'sumi ! 


Ibnu Taimiyyah ya kawo wancan ra'ayi karkatacce se ya ce : 


" وهذا الرأي من أفسد الآراء ، وهو رأي أهل البدع من الرافضة والمعتزلة وغيرهم ، حتى قيل لبعض شيوخ الرافضة : إذا جاء الكفار إلى بلادنا فقتلوا النفوس وسبوا الحريم وأخذوا الأموال هل نقاتلهم؟ فقال لا ، المذهب أنا لا نغزوا إلا مع المعصوم ، فقال ذلك المستفتي _ مع عاميته _ : والله إن هذا لمذهب نجس " فإن هذا المذهب يفضي إلى إفساد الدين والدنيا " 


( منهاج السنة ، ١٥٨) 

Shi ya sa atsawon tarihi aka samu Rafidha ba sa goyon bayan musulmi wurin yaqar Kafirai , kai har ma temakon Kafiran suke yi , haka suka yi alokacin da Tatar suka shiga garin Bagdad suka karya shugabancin Abbasiyyah , haka ma suka yi alokacin da Amerika ta shiga qasar Iraqi a shekarun baya . 


Masu wannan lalataccen ra'ayi suna yin watsi da jibinta na wajibi da Allah ya sanya shi tsakanin dukkan muminai , Allah ya ce : 


"والمؤمنون والمؤمنات بعضهم أولياء "

Acikin ayar nan Allah ya rataya jibintane akan imani , saboda Allah ya rattaba hukuncin jibintane akan lafazin " المؤمنون " ، shi kuma lafazine me dauke da sifa ( المشتق و اسم الفاعل) ، a ilimin Shari'a , duk lokacin da aka jeranta hukunci akan lafazi me dauke da sifa ; to hakan yana nuni akan cewa ma'anar lafazin itace illar hukuncin . 


Malaman Shari'a suna cewa : 


" إذا رتب الحكم على وصف دل على العلية " 


Don haka , duk wanda yake mumini to yana da haqqin jibintaka daga yan uwansa muminai gwargwadon imaninsa . 

Sannan kuma , saboda Allah ya qarfafa mana kiyaye wannan haqqi na jibintaka , se ya kawo saqon a sura ta labari ( الخبر ) ، duk da cewa saqon saqone na umarni (الإنشاء ) ، wato jumlace ta insha'i aka zo da ita a sura ta labari , a ilimin larabci akan zo da zance a wannan salon domin qarfafawa akan tabbatar da saqon da ya qunsa , da rashin saba ma sa . 


Don haka , duk wanda ya yi tawaqqufi akan temakon Musulmin Filasdin akan Yahudawa da abin da ze iya yi garesu na temako , ko ya goyi bayan yahudu akansu ; to haqiqa ya sabawa Allah da manzansa da magabatan musulmi na qwarai .


Sheikhanã Ateeq Sulaiman Hafizahullah.

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter