ABUBUWAN DA RADDINMU NA JIYA YA KUNSA
Ganin cewa; rubutunmu na jiya mai taken:
"DA MUNGUWAR RAWA GARA KIN TASHI… Raddi ga rubutu mai taken: "Hakimiyya Daga Jami’ar Musulunci Ta Madina!"
rubutun ya yi tsawo da yawa, kuma har wasu 'yan'uwa sun koka, to sai na ga dacewar na yi bayanin abubuwan da raddin ya kunsa, don ya ba da karfin guiwar karantawa.
Ga su kamar haka:
1- Shimfida da ta kunshi bayani a kan kwadaitarwar Prof. Dr. Mansur Sokoto a kan karanta littafi mai suna: "القصة الكاملة لخوارج العصر", don sanin tushen Kungiyoyin Ta'addanci na Zamani.
2- Tsokaci a kan littafin da Malam Umar Mansur ya tallata wa mutane mai suna: (الطريق إلى جماعة المسلمين), wanda ya kunshi Akidar da Kungiyoyin Ta'addanci suka ginu a kai, da kuma tsokaci a kan mawallafin littafin da yanayin rubuta littafin.
3- Raddi a kan Akidar Sayyid Qutub ta kore samuwar "Al'ummar Musulmi" wacce take nufin kafirta al'umma, kuma Akidar ta zama hujja ga Kungiyoyin Ta'addanci na yakar Musulmai.
4- Raddi ga mawallafin littafin (الطريق إلى جماعة المسلمين) bisa Akidarsa ta kore samuwar "Jama'ar Musulmi".
5- Yaye shubuhar takaita ma'anar "Jama'ar Musulmi" a kan Jama'a ta khalifancin Daula kadai.
6- Yaye shubuha a kan samuwar Dauloli fiye da daya a cikin al'ummar Musulmi.
7- Bayanin "Hakimiyyar" Sayyid Qutub, da tabbatar da cewa; Hakimiyya ce irin ta Khawarijawan farko, wacce Sayyidina Aliyu (ra) ya ce a kanta:
((كلمة حق أريد بها الباطل)).
8- Misalai na maganganun Sayyid Qutub, inda ya tabbatar da cewa: mutanen da suke kiran kansu Musulmai a zamaninsa kwata - kwata ba Musulmai ba ne.
9- Bayanin babban sakon da Malam Umar yake son isarwa game da Littafin da Prof. Mansur Sokoto ya dora hotonsa a shafinsa, kuma ya kwadaitar a kan karanta shi, mai suna (القصة الكاملة لخوارج العصر).
10- Raddi a kan tuhumar da Malam Umar ya yi ga mai littafin (القصة الكاملة لخوارج العصر) cewa ya rubuta littafin ne don ya biya bukatar Yariman Saudiyya, da bayanin cewa: wannar tuhuma karya ce.
11- Bayanin cewa: Akidar Sayyid Qutub a Babin Hakikanin Imani Akidar Khawarijawa ce. Da tabbatar da haka daga maganganunsa masu yawa.
12- Ambaton maganar Dr. Mahmud Assaf (na hanun daman Ustaz Hassanul Banna, kuma jigo a Rundunar Kundubala ta Sirri ta Kungiyar Ikhwan) wacce ta tabbatar da canzawar tunanin matasan Ikhwan zuwa ga Tunanin Ta'addanci a dalilin tasirin Sayyid Qutub a kansu, musamman a littatafansa guda biyu: "Fi Zilalil Qur'an" da "Ma'alim fi al-Dareeq".
Allah ya shiryar da mu gaba daya.