Subscribe Our Channel

 Iyayena da Mutuncina Kariya ne ga Annabi Muhammad (saw)


Jin zafi da ɗaukar mataki idan wawaye sun ci zarafin Annabi (saw) alama ce ta ƙarfin Imani. Saboda son Manzon Allah ginshiƙi ne na imani a cikin Addinin Muslunci.


To amma babu waɗanda suke ba mu ciwon kai idan irin wannan abin takaici ya faru sai ƙungiyoyi biyu masu faɗa da juna a kan siyasa. Ta yadda a kullum idan abin takaici irin wannan ya faru sai su yi ƙoƙarin siyasantar da lamarin.


Daga wannan lamari ya faru shi kenan sai ya zama wasu sun samu ƙofar kafirta shugabannin ƙasashen Musulmai ta hanyar kiransu da sunan Munafukai.


Su kuma ɗaya ɓangaren sai su tashi haiƙan suna inkarin irin matakan da ake ɗauka, na kiran a ƙaurace ma kayayyakin kasuwanci na kamfanonin ƙasar da ta ci zarafin Annabi (saw), -wai- da sunan an saɓa wa shugaba "Waliyyul Amri".


To wa ya gaya maka dole sai "Waliyyul Amri" ya ce na yi inkarin munkari kafin na yi?!

"Waliyyul Amrin" nan fa ana yi masa ɗa'a ne a kan kyakkyawa, kuma wajibi ne a saɓa masa idan ya yi umurni da mummuna. Idan ya yi zalunci ne kuma sai a yi haƙuri, ba za a yi masa bore da tawaye ba, matuƙar yana amsa sunan Musulmi.


Wannan shi muka sani a Salafiyyar gaskiya.


Saboda haka duk lokacin da wawaye suka ci zarafin Annabi (saw) wajibi ne ka taimaki Annabi (saw), ka ba shi kariya, ka ɗauka masa fansa ta dukkan hanyar da ta sawwaƙa gare ka, don neman yardar Allah, ba don ka gwarzanta shugaban ƙasar da kake goyon baya, ka jefi sauran shugabanni da Malamai da Munafurci ba, matukar ba su nuna goyon baya ko ba da kariya ga wawayen arna da suke izgilancin ba.


Ɗaukar fansa ga Annabi (saw) a irin wannan mataki yana kasancewa ne gwargwadon iko da ƙarfin imani. Wani Mumini ne mai ƙarfi, zai iya ɗaukar babban mataki, wani kuma Mumini ne mai rauni a kan wannan lamari. Amma dukansu akwai alheri a tare da su. Annabi (saw) ya ce:

«المؤمن القوي خير وأحب إلى الله من المؤمن الضعيف، وفي كل خير»

صحيح مسلم (4/ 2052)


"Mumini mai ƙarfi ya fi alheri da soyuwa a wajen Allah fiye da Mumini mai rauni, amma kowannensu akwai alheri a tare da shi".


Marasa albarka a wannan lamari su ne Zindiƙai Munafukai marasa imani, waɗanda da ma an sansu da magana mai lahani. Su ne a kullum masu goyon bayan kafirai, suna kare su. Kafirai su zagi Manzon Allah (saw) amma su kuma sai su fito suna kare su, suna ba su mafita, suna zargin Musulmai masu ɗaukar fansa ga Annabi (saw).


Saboda haka matsayin Manzon Allah (saw) jan layi ne a wajen Mumini, ba abin wasa ba ne.


Muminai suna ba da iyayensu da kawunansu fansa ga Manzon Allah (saw). Hassan bn Thabit (ra) ya ce:

فإن أبي ووالده وعرضي *** لعرض محمد منكم وقاء

صحيح البخاري (5/ 117) صحيح مسلم (4/ 1936)


Ma'ana; Babana da mahaifinsa da mutuncina, duka kariya ne ga mutuncin Annabi Muhammad (saw).


Saboda haka za mu cigaba da kawo muku babbar Sunna a irin wannan lamari, wato "Hija'i" (waƙoƙin zambo) ga wawaye. Insha Allahu za mu kawo muku "Hija'in" Shaikh Aliy bn Abdulkhaliƙ al-Ƙarniy a kan wawaye masu ɓatanci ga Annabi (saw).

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter