Subscribe Our Channel

 Game da ilimin Usulul Hadis : 


Idan ďalibi ya fara da littafin Tazkira ta Ibnu Mulaqqin , sai ya tsallaka Nukhbatul Fikr , daga nan sai ya karanta littafin "لغة المحدث الصغرى" ، ko wata manzuma taķaitacciya a fannin , kamar " اللؤلؤ المكنون " na Hafiz Alhakamy , ko " قصب السكر " na San'any , duk wacce zai yi a cikinsu to ya haddaceta . Daga nan kuma sai ya karanta Alfiyyar " لغة المحدث الكبرى " , wannan Alfiyyar tafi ta Suyuďy da Iraqy sauki, kuma tafi su tattaro masa'il mafi amfani a ilimin Hadisi , don haka ďalibi zai iya wadatuwa da ita daga sauran Alfiyyat . 

Sai ďalibi ya shagaltu da kutubul ilal ( ķanana) da su'alat da mas'il da marasil . 

Mafi kyawun manzumat da na sani acikin ilmul ilal sune kamar haka : 

1. نظم العقد لمسائل النقد للشيخ عبد الباري بن حماد الأنصاري 

2. المنظومة في نقد الحديث لابن حماد الأنصاري

3. شافية الغلل للعلامة محمد بن علي بن آدم الأتيوبي .


Haddace waďannan manzumat ďin alherine mai girma , ďalibi zai samu malaka mai ķarfi acikin ilimin ilal na Hadisi , samun wannan ginshiqine mai ķarfi a ilimin Hadisi , daga nan kuma sai ďalibi ya yi ta faďaďawa . 


Wannan ra'ayinane , ba dole sai ta wannan hanyar za a isa zuwa ga abun nema ba , amma dai ni ina ganin hanyace mai saukakewa . 


Allah ya taimakemu


Mal. Ateeq ne ya rubuta, sai Mal. Abi Abdillah Ahmad sidi, yayi ta'aliƙi da;


Allah ya sakawa sheikh da alkhairi, dan karin haskena:

1- Mafi kyawon littafin da ya dace dalibi ya fara da shi littafin البيقونية، kuma wannan itace sunnar maabota ilimi galibi a wannan fanni, wake ne marar yawa, kuma mai sauki, ya kuma tattara nau'oa muhimmai.

2- littafin نخبة littafi ne karami a yawa; amma ya tattara kusan dukan mas'alola na hadisi, kuma karantarsa shi kadai bai cika amfanarwa ba yadda ya kamata; dole a hada shi da sharhin نزهة

3- Ilimin ilal shi ne makura ta karshe a ilimin hadisi, kafin shiga cikinsa da fadadawa dalibi yana bukatar zurfi a musdalahu, da kuma sanin littafan jarhu wattaddil da salon mawallafansu, da fannona ma su alaka da mariwaita da littafan da aka wallafa game da su; wanda akwai littafai kebantattu ma su bayani kan haka, ba za a same su acikin littafan musdalahu ba a fayyace.

4- Akan samu Littafan malamanmu na zamani su samu mizoji da ba bu a na magabata; amma rataya dalibai ga littafan magabata shi ya fi dacewa saboda dalilai kamar haka: A- Su ne littafan da suka shahara a fannin, kuma su ne aka yiwa hidima; misali: Alfiyyatul iraqi littafan da ke alaka da ita suna da yawa, wanda karanta alfiyyar ta iraki za ta lizimta komawa ga littafai ma su alaka da ita. B- Fadadawa wajen dogaro da littafin malaman zamani saboda ya fi gamewa sila ce ta kara nisa da littafan manyan malamai magabata, na kuma san sheikh mutum ne mai kwadayin ratayuwa da littafan magabata.

Mafi dacewa ko dai a hada biyu, ko kuma na magabata ya zama asali, na malaman zamani ya zama tamkar murajia. Anan ina magana idan an samu kusancin matsayi tsakanin na magabaci da na malamin zamani, amma idan banbancin mai fadi ne, ba laifi don an wadatu da na malamin zamani


Wannan kuma ba raunana aikin malaman zamani bane; tabbas akwai wadanda ayukkansu a zahiri sun fi karfi bisa ga na wasu magabatan, sai dai: الفضل لمن سبق

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter