A cikin littafinsa كتاب بيان البدع الشيطانية التي أحدثها الناس في أبواب الملة المحمدية Sheikh Usman bin Fodio (Rahimahullahu) yace akan "CARBI":
ومما يلحق بهذه البدع اتخاذ بعض الناس المسبحة في يده كاتخاذ المرأة السوار في يدها، وتعليقها في عنقه وهو بدعة مكروهة
"Daga cikin abinda yake haɗuwa da waɗannan Bid'o'i shine abinda wasu mutane suke yi na rike carbi a hannu kamar yanda mace take sanya awarwaro a hannunta, da kuma rataya carbin a wuyansu, wannan Bid'a ne abin ƙi." Bai tsaya anan ba, sai yace:
وأما المسبحة في نفسها فجائزة
"Amma sai dai ita carbi a karan kanta, halal ce." (Shafi na 12).
A CIKIN BAYANIN Sheikh Usman bin Fodio (Allah SWT yayi masa rahama) ya nuna ita carbi a karan kanta ba haramun bane a yi amfani da ita. Iyaka, mutane su fahimta, wannan baya nufin wai yin haka shine "Sunnah", kawai ja'izi ne, abu da yake halatta. Don haka, "Rikar carbi" baya bayar wa mutum ladan koyi da Annabi SAW, amma mutum zai samu ladan zikirorin da yake yi.
A fahimta, akwai aikin Annabi SAW da yake wajibi سنة واجبة kamar tsarin alwala da Sallah da abubuwa da yawa; akwai aikin Annabi SAW da yake abin so ne a aikata kuma in aka yi za'a samu lada amma ba wajibi bane سنة مستحبة kamar Sallar Walha da wasu nafilfilu da sanya wata kalar riga da Annabi SAW yake sakawa amma da niyyar koyi da shi; akwai aikin Annabi SAW da yake zama haramun سنة محرمة kamar yin aure fiye da mata huɗu; da saurasu. Ita carbi ba ta cikinsu, dukda an samu Annabi SAW ya tabbatar da sashin wasu Sahabbai da yin amfani da abin kirge wanda ba carbi ba, misali tsakonkoni.
A cikin maganar Sheikh Usman bin Fodio akwai tarayya da maganar Ibn Taimiyya (Rahimahullahu) cewa rikar abin irge ba haramun bane, amma ba shine Sunnah ba. Ga maganarsa:
وعد التسبيح بالأصابع سنة… وأما عده بالنوى والحصى ونحو ذلك فحسن، وكان من الصحابة رضي الله عنهم من يفعل ذلك، وقد رأى النبي صلى الله عليه وسلم أم المؤمنين تسبح بالحصى، وأقرها على ذلك. وروي أن أبا هريرة كان يسبح به
"Irga tasbihi da yatsun hannu Sunnah ce....amma irgasa da kwallon dabino ko tsakonkoni da makamantar wannan abu ne mai kyau ba mai muni ba; a cikin Sahabbai an samu masu aikata haka. Annabi SAW ya ga ɗaya daga cikin matansa tana tasbihi da tsakonkoni, ya barta akan haka. Haka nan, an ruwaito cewa, Abu Hurairah (RA) ya kasance shi ma yana yin haka..." [Cikin مجموع الفتاوى - Majmu'ul Fatawa, 22/506]
Faɗin cewa, "Carbi halal ne" baya nufin daidai yake da abinda Annabi SAW yayi ko ita wata Sunnah ce da mutum zai samu wata lada akai, iyaka ana nufin ba haramun bane. Sannan, har ila yau, duk da rikar carbi na halatta amma rikar carbi bashi da falala kamar yin amfani da yan yatsu, saboda Annabi SAW ya tabbatar da falala ne ga yin amfani da yan yatsu banda wani abu koma bayan wannan.
A kullum, shi Musulmi kuwa, ya kan dage ne ya kara ganin yana yin abu yanda Annabi SAW yayi don ya samu lada da falala na koyi da Annabi SAW, kuma musamman a yayinda Annabi SAW yace yan yatsu da ake tasbihi da zikiri dasu zasu yi shaida ga mutum a Ranar Kiyama.
ALLAH YA DATAR DA MU.
Dr. Abdulmalik Sani