Subscribe Our Channel

 Akan CARBI


  Sau da dama akwai masa'il da akan bujiro da su a wannan sahar ta fesbuk amma rashin takaituwar tattauna su tsakanin masu dikka cikin ta ko ince mallami ko ɗaliban ilimi (na gaske) sai hayaniya ta hana mu kananan ɗalibai mu anfana da abunda wannan ma'ana take ƙunshe da shi na ilimi ko kuma abunda tattaunawar ta kunsa na fa'ida, domin kowa kai kar ace bai ce komai ba, dan haka sai hayaniya ta kaure aita jifan juna da maganganu iri iri. 


1 yanzu mas'alar CARBI wasu gani suke mas'alar mai sauƙin gaske ce da kowa ka iya tofa albarkacin bakinsa wajan halartawa ko haramtawa amma fa a hakikanin gaskiya abun ba haka yake ba, mas'alar tana buƙatar abar mallamai suyi sukuwa kanta mu kuma kananan ɗalibai mu anfana da abunda ke ciki na ilimi. 


2 dalilin da yasa nace ba mas'ala ce mai sauƙin gaske ba, kawai wani ɗan tsokaci na gani na Dr Nura Sulaiman Sulaiman dan gane da wasu dalilai da lallai sai an lura dasu da kyau kafin mai halartwa ya halarta shi ne ka'ida guda biyu kawai da ya kawo kamata haka: قاعدة الترك da kuma قاعدة الأمر بالشيء هل يقتضي النهي عن ضده؟ wannan yake nuna maka kai mai halartawa kana bukatar warware waɗannan ƙa'idodin wajan tabbatar da naka hukuncin, hakan kuna na bukatar nazari sosai


 3 haka a daya bangaren na masu halartawa sukai yiwa قاعدة الترك kai'di da manufar shari'a a babin tasbihi ko ibada gaba ɗaya, ma'ana مراعاة مقصود الشارع في الأبواب wanda daga nan sukai indilaki cewa a wannan babin manufar shari'a shi ne Attausi'a da kuntatawa ba, مقصود الشارع في باب الذكر والتسبيح بل في باب العبادات التوسعية في الأدوات والآلات المعنية في تحقيق الغاية so sai suka ce carbi Ala ce da ka iya taimakawa wajan azkar shirin shari'a ko barin sa baya hukunta bari domin lura da manufar shari'a a wannan babin, wannan shi ne asalin da Sheik أحمد محمد النجار na ɗora fatawarsa akai ta halarta amfani da Carbi, abu ne kuwa sananne cewa lura da manufar shari'a yana taimakawa wajan dabdi da tahkiku na hukunci, yana taimakawa mai bada fatawa da kuma wanda za a bawa fatawar kamar yadda Sheik fad'l Abdallah Murad ya fada a littafin sa mai suna فقه الصيام so mai haramtawa sai ya tunkuɗe wannan dalilin kafin nan. 


4 Dr Nura Sulaiman ya kara fadin wani wajahi da kai iya maida abun bid'a ma'ana reke CARBI inda yake kudirce yin tasbihi da CARBI hakan ibada ne na iya maida abun bid'a, kuma gaskiya masu amfani da carbi lokacin da suke ibadar da wannan carbin suna ƙudurta hakan cewa ibada suke a wannan hai'ar ai kuwa akwai bukatar nazari


5 haka ƙiyasin carbi da Lasifika kamar yadda masu halartawa suke fada shi ma akwai فارق gaskiya tsakanin lasifika da carbi wannan kuwa suka ne قادح ga kiyasin, naga Shek Khidir Ibrahim ya yi isha zuwa ga wannan gabar itama


  So manufar wannan tsokacin shi ne wannan mas'alar gaskiya tana bukari mallamammu suyi magana akai da mu zan akan basira muke, ina fatan malamammu za su yi mana tsokaci kai mu anfana, kar su barmu da yan hayaniya cikin masu cewa Haram ko halal


  Allah ya yi mana jagoranci, Tabbas kowanne bangare ns bukatar Nazari sosai kan mas'alar, amma wannan fahimta ta ce 

والله أعلم


Mal. Abu Ahmad Tijjani

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter