Hammadu bnu Salamata bni Dinaar, Abu Salamah Al- Basriy.
Imamu Ahmad bn Hanbal, Aliyu bnul Madiniy da Yahya bn Ma'een duka suka ce: babu maruwaici mafi inganci cikin almajiran Thabit Al- Bunaniy kamar Hammadu bn Salamah.
"أثبت الناس في ثابت حماد بن سلمة".
Wannan ya sa Imamu Muslim ya riwaito Hadisin Hammadu daga Thabit daga Anas dan Malik (ra) daga Annabi (saw) a "Usul" ba a "Shawahid" ba.
Ibnu Hibban ya ce:
ولم يكن من أقران حماد مثله بالبصرة في الفضل والدين والعلم والنسك والجمع والكتبة والصلابة في السنة والقمع لأهل البدعة ولم يكن يثلبه في أيامه إلا قدري أو مبتدع جهمي لما كان يظهر من السنن الصحيحة التي ينكرها المعتزلة
الثقات لابن حبان (6/ 216 - 217)
"A cikin tsaran Hammad babu kamarsa a garin Basra wajen Falala da Riko da Addini da Ilimi da Ibada da tara Hadisai da marubuta da Tsayuwa a kan Sunna, da kwankwasan 'Yan Bidi'a. A zamaninsa babu mai sukarsa sai Baqadare, ko Dan Bidi'a Bajahame, saboda yadda yake bayyana Ingantattun Hadisai wadanda Mu'utazilawa suke kinsu".
Ibnu Adiyyi ya ruwaito labaru guda biyu a kan Hammadu bn Salamah ta hanyar wani mutum mai suna Abu Abdillah Muhammad bn Shuja'i bn Al- Thaljiy, cewa:
1- -Wai- Hammad yana ruwaito wasu Hadisan da ba a sansu ba, bayan ya fita wani gari mai suna Abbadaan, sai ya dawo yana ruwaito su, -wai- ana zaton Shaidan ne ya jefa masa su.
2- -Wai- kuma ba ya iya haddace Hadisi, wai ana yi masa cushen Hadisai a cikin Littafinsa. -Wai- yana da wani Agola mai suna Ibnu Abil Auja'i, -wai- shi yake yi masa cushen Hadisan karya a cikin Littatafansa.
To bayan Ibnu Adiyy ya ambaci wadannan labarai sai ya ce:
وأبو عبد الله بن الثلجي كذاب وكان يضع الحديث ويدسه في كتب أصحاب الحديث بأحاديث كفريات
الكامل في ضعفاء الرجال (3/ 47)
"Abu Abdillah bn Al- Thaljiy MAKARYACI NE, ya kasance yana kirkiran Hadisai ya cusa su a cikin Littatafan Malaman Hadisi".
Al- Thaljiy ya ruwaito labarin Agolan ne daga wani mai suna: Abbad, wanda shi ma ba wani abin kirki ba ne.
Ibnu Hajar ya ce:
وعباد أيضا ليس بشيء، وقد قال أبو داود: لم يكن لحماد بن سلمة كتاب غير كتاب قيس بن سعد يعني كان يحفظ علمه
تهذيب التهذيب (3/ 15)
Don haka labarin Agolan Hammad karya ne kawai.
Saboda haka, duk Hadisin da Hammadu bn Salamah ya ruwaito daga Thabit, kuma Imamu Muslim ya ruwaito shi a "Usul", to Hadisi ne tabbatacce ingantacce, kamar Hadisin makomar Baban Annabi (saw).
Kuma maganar da ake yada cewa; Agolansa yana yi masa cushen Hadisan karya, labarin daga Makaryaci Ibnul Thaljiy ya fito. Kuma da ma 'Yan Bidi'a sun tsani Hammadu bn Salamah, shi ya sa suke yi masa batanci da karerayi, kawai saboda rikonsa da Sunna da tsananin kyamarsa ga Bidi'a.