Subscribe Our Channel

 JINGON BATU DA PROFESSOR ISA PANTAMI YA WUCE MAGANAR HUKUNCIN "CHARBI":


Ba Proff. Isah ne ba farkon wanda yake ganin halascin amfani da Charbi ko ya dawo daga wata matsaya akanta zuwa wata, kuma irin wannan canza matsayar a cikin fahimtar wasu matsalolin Addini idan ya ginu ne akan ilimi da Adalci baya zama aibu don mutum ya canza wata matsaya cikin Mas'ala, abun lura shine gina komai akan Asasi na ilimi da Adalci.


Don haka, da ace Mal. Isha Ali pantami zuwa yayi ya bayyana matsayarsa ko ya bayyana cewa ya dawo daga abunda ya kasance akai na ƙirga charbi cikin Bidi'ah ko na haramtata saboda dalilai kaza da kaza da suka bayyana a gare shi, shike nan, ba wata magana wadda ta wuce tattaunawa dashi akan dalilansa na canza matsaya ga masu son su tattauna dashi don kaiwa ga gaskiya.


Amma sai Mal. Isha Ali pantami yaƙi tsayawa matsayar Adalci ya bar ladabin saɓani ya cakuɗa maganganunsa da yarfe da suka da ƙage ga masu riƙo da matsayar data saɓa tashi a yanzu wadda shi ya kasance akanta a can baya; kuma ya sani sarai cewa a cikin masu hani daga gareta akwai Malamai masana sama dashi nesa ba kusa ba waɗanda duniyar ilimi da SUNNAH ta yadda cewa malamai ne ababen koyi, amma yayi misisi ya saki baki akai, yayi wannan ta hanyar jifansu da:


1- ZAFIN KAI: Wannan siffa ce mai muni wadda shi isah pantami ya yadda cewa yayi fama da wannan ciwon a can baya wanda yana daga cikin ababen da suka ɗauke shi zuwa haramta Charbi, da akwai adalci da kyautata zato ba zai jefi sauran almajiran SUNNAH da malamanta da ciwon da yayi fama dashi wanda yake jin cewa ya warke a yau. Kowa dana shi dalili, kai kace ZAFIN KAI ne naka, su kuma abunda ya bayyana ne na hujjoji.


2- RASHIN ADALCI: Ishima wannan JARHI ne mai muni ga duk mai hankali ya siffantu da rashin Adalci balle Malamai na SUNNAH, idan shima yana daga cikin sabubban haramtawa da kayi a can baya, don me zaka jefi sauran malamai da cutar da kasance a cikinta a baya wadda yanzu kake jin ka warke daga gareta a yau. Shin Malaman da suka halarta CHARBI a lokacin da kake haramtawa waɗanda yau kake tutiya dasu wurin kare matsayarka ta yau, shin suma can baya kenan a wurinka Ƴan ZAFIN KAI ne marasa ADALCI ko kuwa?


3- FARA KARATU: Wannan yana nufin ƙaramta matsayarsu ta ilimi da rashin kafuwa a cikinsa, wanda jifan masu haramtawa da wannan lallai zahirin abunda yake bayyane yana ƙaryata wannan magana taka, domin daga cikinsu akwai manyan Malamai na duniya da sukayi fice a ilimi da yi mashi hidima tun kafinka da zamani mai tsayi, wannan yasa Malaman dakake ƙirgowa dasuka halarta basu jefesu da wannan sukar daka jefesu da ita, balma sun yarda da matsayinsu mai girma a ilimi da kafuwa a cikinsa.


4- RENA LITTAFIN MALAMI: Ka siffanta littafin Babban Malami Sheikh Bakar abu Zaid da abunda bai dace ba, wanda yana nuna ƙaramcin sanin makamar wallafa a abin Shari'ah daga gareka, domin girman littafi ko sauƙinsa ba shine ma'aunina sanin ƙimarsa ba a wurin malamai, abinda ya ƙunsa ne ke bayyana matsayarsa, wannan yasa wasu Malamai sunfi yarda da ƙananan littafansu akan manyan masu sifilai da yawa dasuka wallafa. Duk wanda yasan abunda ake kira ilimi, yasan wahalar tanatance shi da wahalar tattara shi a can baya da wahalar tsara shi cikin yaren ilimi yasan cewa littafin Sheikh Bakar abu Zaid wallahi littafi ne, koda zai saɓa masa a sakamako amma yafi karfin reni, domin littafi ne wanda yake bayyanar da ƴanci a binciken ƙwaƙwaf cikin batu, wanda ya haɗa fannona na ilimi masu yawa a cikinsa, ba binciken Google ba, zan iya cewa, iyakacin abunda nasani shine; masu halartawa basu wallafa wani littafi kamar na Sheikh Bakar abu Zaid ta fuskar kafuwa da ƙarfi da zirga bincike kusan duk na bayansa عيالا ne ga littafinsa.


Wasu najin ko ana masa bakin ciki ne ko tsana ce yasa aka fuskance shi a wannan batu, amma Wallahi ba haka ne ba, domin daga cikin masu halas'tawa a nan gida Nigeria, akwai waɗanda suka wuce shi a ilimi da matsayi a cikin SUNNAH da riƙo da ita da da'awa zuwa gareta, haka a cikin masu haramtawa, ba wani abu sabu daya kawo a cikin face usulubinsa na suka da yarfe ga Malamai a cikin wannan batu.


Don haka, ba'a yi masu mu'amala ba yadda aka yi masa, domin basu tattauna batun ba yadda ya tattauna shi, basu jefi ƴan uwansu malamai Ahlusunnah ba yadda yayi.


Ba yau ne Malam Isha Ali pantami ya fara barin matsayarsa ba saboda wasu dalilai masu kamada waɗanda ya ambata a cikin wannan batu ba wato dalilan Zafin kai da rashin Adalci, a can baya daya kan kujerar ministan sadarwa da wasu musamman Arna suka ɗauko wasu maganganunsa daya yi a can baya sai ya bada uzuri da cewa a lokacin YARANTA ce kuma yanzu ya canza ya jaye akan waccan matsayar.


Mukam munsan ba YARANTA ce ba, kaucewa SUNNAH ce da tafarkin magabata a abin da'awa da tushen AƘIDAH, Kamata yayi Malam ISAH ALI PANTAMI ya rarrabe koda a dunƙule ne yace: Abinda na tabbatar wanda yake dai-dai da tafarkin SUNNAH da fahimtar magabata ina akai har yanzu, wanda yake saɓanin haka na janye, amma inaaaa sai ya bada amsa a dunƙule a game a cure baki ɗaya yayi kuɗin gori yace duk YARANTA ce. 


Mafi yawanci ka lura da masu da'awa na zamani masu wuce iyaka idan suka dawo saboda wasu dalilai dabana SUNNAH ba, idan ba ALLAH Yayi masu gamnakatar da lizimtar Malaman SUNNAH na gaskiya datitijai a cikinta sai kaga sun faɗi daga zafi 100% zuwa susucewar 0%.


Kaga can baya suna kafirta shugabanni ko tsine masu saboda tsarin demokradiyya ko kiransu Ɗagutu, sai su dawo zuwa ga neman Takara da kafa jami'yyar siyasa da buga fos'toci da narkewa.


ALLAH Yayi mana Taufiƙi.


Dr. Abdulmalik Sani

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter