Wasu abubuwan da za su taimaka maka in ka shiga aji karantarwa.
1- Ka shiga da manufa : Wato ka tsara wa kanka me kake so ɗalibanka su koya kafin ka fito daga ajin, kar ka shiga kawai da suna za a yi karatu, a'a me za a koya a karatun.
2- Ka shiga da kayan aiki : Bayan ka tsara me kake so a fahimta, sai ka shirya me zai taimaka maka wurin fahimtar da su wannan abin cikin sauƙi, tun daga kayan rubutu, da makamantansu.
3- Ka tanaji salo tun kafin ka shiga : Ka tsara hanya da salo mafi dacewa da kake ganin za ka koyar da ɗalibanka abinda kake so su fahimta cikin sauƙi, hanyar labari ne, ko karanta karatu su amsa, ko kawo mas'ala ne su warware ko dai ya ne ka zaɓi salon da ya dace.
4- Ka shiga da tambayoyinka : Wato bayan ka tsara me kake so su koya, sai kuma ka shirya tambayoyin da za su taimaka maka ka fahimci sun gane ko abinda kake so su gane ko ba su gane ba. Tare da haɗa su da ayyukan gida wanda za su iya yi da kansu ba wanda sai an musu ba.
5- Ka shirya yabo da kyakkyawar fata : In ka yi darasi, ka tambaya wanda ka ga ya fahimta ka mishi kyakkyawan sakamako da zai ƙara masa himma, daga kyakkyawar addu'a zuwa kyauta da makamantansu, wanda kuma ka ga ya gaza ka fahimta, ka mai fatan alheri, ka ƙarfafa mai gwuiwar lallai zai iya, kuma ka ɗora shi a hanya tare da addu'a da shawarwari.
Mal. Abu Ahmad Tijjani Haruna