Subscribe Our Channel

 MAGANA A KE A KAN CARBI!

Na yi mamaki da na ga prof ya sake dawo da wannan maganar, duk da ban sani ba kila tana ta ruruwa ne a kasa.

1. Ni bani da fahimtar bidi'antar da carbi a sake, amma duk wanda ya ke rayuwa musamman a irin kasashen mu, ganin yadda yan bidi'a suka mayar da carbi, to ba wani abin a tayar da hakarkari ne wajen ba shi kariya ba.

2. Da Prof ya halarto da littafin اقتداء الصراط المستقيم, watakila da bai yi sabi zarce ba, domin shari'ar Musulunci a wurare da dama yana kyamatar da kaman-ceceniya da wadanda suka khalafa masa. Babu shakka carbi wadanda suke yakar Sunnah a yanzu su suka mayar da shi kamar shi'ãr a wajen su.

3. Kamata ya yi Prof ya ce; yin tasbihi da hannu shi ne Sunnah, amma ja'izi ne idan ka yi da carbi! Amma ya kasa sai cewa yake wai yi da hannu ya fi falala!!!

4. Sai maimaitawa ya ke wai wancan fatawar zafin kai ne! Ga shi kuma ya fadi Manyan Malaman da suka ta fi akai!! Anya wannan maganar ta sa ita ma ba wani zafin kan ba ne kuwa!!!

5. Kamar prof ya 'karantar (takhfif) da ilimi ko binciken masu akasin fahimtar sa akan mas'alar, ban cika bibiyar sa ba, amma ina ga ba dabi'ar sa ba ce, don wannan salon bai dace da shi ba.

6. To wai wani zurfin ilimi ko bincike ne ke cikin abin da babu ãyah babu Hadisi akai! Kenan kurewa dai komawa za a yi zuwa "البراء الأصلية "

Ko kuma hikayoyin wadansu magabata da kila suka yi amfani da shi. Duk idan ka gama tarawa ba za su iya kai shi ko mustahabbi ba! Da wannan ne ake bayar da goron gayyatar!!!

7. Kiyasin carbi da speaker ni har yanzu "عندى فيه نظر" Lura da cewa sun saba a asali! Shi wannan asalin domin ibada aka kirkire shi, sabanin speaker. Ga wadansu jama'a can sun riki hotunan mutanen kirkin su, amma yan bayan suka mayar da su abin bauta.

8. Abin da ya fi dacewa ga Prof ya karfafi jama'a ne akan su wadatu da abin da Manzon Allah SAW Ya wadatu da shi, Shi da sahabban sa.

9. Muna lokaci ne na shubuhat da yakar Sunnah, abin da da'awar ta fi bukata yanzu shi ne kira zuwa ga الاعتصام بالسنة

10. Daga karshe ina fata Prof zai koma ya yi muraja'ar kalaman sa ya kuma dauki matakin gyara. Ina rokon Allah SWT Ya kara yalwata kirjin Prof.

Bslm (Khidir Ibrahim)

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter