Subscribe Our Channel

 Carbi !


1- Carbi a Najeriyance sha'ira ce ta 'yan bidi'a da masu sukar sunna da Ahlussunna, suka shahara da riƙewa, ya kamata duk wani Ahlussunna mai kishin sunna ya kiyaye shi.


2- Tasirantuwa da Ɗariƙa ko 'yan Ɗariƙa sanadiyyar zama da su ko abota da su ko karatu a wurinsu shi ke sa ka ga Ahlussunna (Ɗan Izala, ko Basalafe) na riƙe carbi.


3- Annabi Sallallahu alaihi Wasallama bai riƙe carbi ba, bai koyar da aiki da carbi ba, da hannu ya ƙirga tasbihinsa, kai ma in kana kishin koyi da Annabi Sallallahu alaihi Wasallama za ka iya.


4- Ƙin riƙe carbi, ko bada fatawar bidi'ancin riƙe carbi, da kwaɗaitar da mutane nisantar shi da riƙo da sunnar ƙirga tasbihi da hannu ba zafin kai ba ne, kuma ba ƙarancin bincike ba ne ko ƙarancin ilimi, ba kuma rashin zurfafa karatu ba ne da taƙaituwa kan kutayyibat, ita kanta mas'alar dama duk kutayyibat aka rubuta a kanta.


5- Baya ga cewa mai kwaɗaitar da a yi tasbihi da hannu yana da ladan koyar da sunna, kuma yana da hadisi. Amma mai goyon bayan a riƙe carbi, raba mutane yake da sunna yana ɗora su kan ja'izi, wanda yana daga cikin hanyoyin da sheɗan ke zo wa mutum.


Mal. Abu Ahmad Tijjani Haruna

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter