Subscribe Our Channel

 WARWARE SHUBUHAR MASU QANQANTA MAS'ALAR TAWAYE GA AZZALUMAN SHUWAGABANNI (2)


(Tsohon rubutu ne)


TSOKACI AKAN MUHADARAR MALAM MUSA ASADUS SUNNAH (3)


Daga cikin kuskuren da Malam Musa ya afka ciki gameda mas'alar haramcin tawaye ga Azzaluman Shuwagabanni shine : yanda yake ganin cewa mas'alar mas'alace mai sauqi wacce ya halatta a yi sa'bani acikinta ta yanda baya halatta a bidi'antar da wanda ya sa'bawa daidai acikinta .


Abunda ya kamata mu sani shine : Ita mas'alar wajibcin biyayya ga Azzaluman Shuwagabanni da haramcin tawaye garesu mas'alace mai girman gaske ; tana daga cikin tushe daga tussa na Aqidar Ahlussunah , Hadisan Annabi sun tabbata gameda ita ta hanyar gangami ( Tawaturi ) , kuma magabata sun yi Ijma'i akan tabbatar da ita , babu wa'danda suka sa'ba acikinta sai Khawarijawa da 'yan bidi'ar qungiyoyin Mutakallimun ( Mu'tazila , Murji'a , Asha'ira , Maturudiyyah ) 


Malaman Hadisi sun ruwaito Hadisan acikin littattafansu mabanbanta ; tun daga kan Assihahu da littattafan Sunan da Masanid da sauransu , hakanan Malaman Musulmi sun taskace Hadisan acikin littattafan da suka qunshi Aqidar Ahlussunah ta hanyar riwaya daga Annabi da Sahabbai da Tabi'ai da wa'danda suka zo bayansu cikin qarnoni masu falala , kamar wa'dannan littattafan :


1 .شرح أصول اعتقاد أهل السنة لهبة الله اللالكائي 

2. السنة لابن أبي عاصم 

3. السنة لعبدالله بن الإمام أحمد 

4. الإبانة الكبرى لابن بطة العكبري 

5. الشريعة للآجري 

6. كتاب الاعتقاد للبيهقي 

7. السنة للخلال 

8. شرح مذاهب أهل السنة لابن شاهين 

9. السنة للكرماني 

10.السنة للمزني 

Hakanan Malaman Musulmi sun ringa sanya wannan mas'alar daga cikin tushe na Aqidar Ahlussunah acikin littattafan Aqida na Ahlussunah wa'danda ake tattaro mas'aloli na Aqida da Magabata su ka yi Ijma'i akansu ; duk wani littafi da aka tattaro aqidar magabata acikinsa sai ka ga ya ambaci wannan mas'alar .


Don haka , wannan mas'alar tana daga cikin tushe na Aqidar Ahlussunah , duk wanda ya ganganta sa'bawa acikinta to babu shakka ya fita daga Sunnah .


Malamai da dama sun hikaito Ijma'in magabata akanta , zamu kawo wani sashi daga ciki :


1. Al'imam Alkirmany ( almajirin Al Imamu Ahmad) , ya na cewa :


" هذا مذهب أئمة العلم وأصحاب الأثر ، وأهل السنة المستمسكين بعروقها ، المعروفين بها ، المقتدى بهم فيها ، من لدن أصحاب النبي (ص) إلى يومنا هذا ، وأدركت من أدركت من علماء الحجاز والشام وغيرهم عليها ، فمن خالف شيئا من هذه المذاهب ، أو طعن فيها ، أو عاب قائلها فهو مخالف مبتدع خارج من الجماعة ، زائل عن منهج السنة وسبيل الحق ...

ولا تخرج على السلطان ، وتسمع وتطيع ، ولا تنكث بيعته ، فمن فعل ذلك فهو مبتدع مخالف مفارق للجماعة " 


(إجماع السلف في الاعتقاد للكرماني ، ٣٢_٤٨)


2. Abdullahi bin Abi Zaid Alqairawany , yana cewa :


" فمما أجمعت عليه الأمة من أمور الديانة ، ومن السنن التي خلافها بدعة وضلالة : أن الله تبارك اسمه له الأسماء الحسنى والصفات العلى ...

والسمع والطاعة لأئمة المسلمين ، وكل من ولي أمر المسلمين عن رضا أو عن غلبة فاشتدت وطأته من بر أو فاجر فلا يخرج عليه جار أو عدل " 


( الجامع ، ١٠٧_ ١١٦)


3. Al Imam Annawawy shima ya ce : 


" وأما الخروج عليهم وقتالهم فحرام بإجماع المسلمين وإن كانوا فسقة ظالمين " 


( المنهاج ، ١٢/٢٢٩)


 Wa'dannan bayanai suna tabbatar da cewa lallai mas'alar haramcin tawaye ga Azzaluman Shuwagabanni mas'alace da Ahlussunah su ka yi Ijma'i akanta , wannan ya sa wa'danda aka sani da sa'bawa wannan mas'alar sune qungiyoyin bidi'a daga Kwarijawa da Mu'utazilawa da rassansu cikin qungiyoyin Mutakallimun .


Alhafiz Ibnu Abdil Barr yana cewa : 


 وإلى منازعة الظالم الجائر ذهبت طوائف من المعتزلة وعامة الخوارج ، وأما أهل الحق ، وهم أهل السنة والجماعة فقالوا هذا هو الاختيار أن يكون الإمام فاضلا عدلا محسنا ، فإن لم يكن فالصبر على طاعة الجائر أولى من الخروج عليه " 

( التمهيد ) 


Muhammad bin Aliy Al 'Dabary yana cewa : 


" إذا وجد من الإمام الفسق في أفعاله فإن ذلك لا يوجب خلعه . وذهبت المعتزلة والأشعرية إلى أنه يوجب خلعه " 


( الإيضاح في أصول الدين وقواعده ، ٤٣٣) 


 A taqaice dai , wannan mas'alar Hadisan Annabi ta hanyar gangami sun tabbatar da ita , kuma magabata sun yi Ijma'i akanta ; don haka tana daga cikin tussa na Aqidar Ahlussunah wa'danda duk wanda ya ganganta sa'ba musu ake qirga shi daga cikin 'yan bidi'a . Shaikhul Islam yana cewa : 


 " من خالف الكتاب المستبين ، والسنة المستفيضة ، أو ما أجمع عليه سلف الأمة خلافا لا يعذر فيه ، فهذا يعامل بما يعامل به أهل البدع " 


( البحرينية ، ٧٣)


_______________________________


Wani zai iya cewa : ya za ace wannan mas'alar ta zama tushe daga cikin tussa na Aqidar Ahlussunah alhalin kuma ga shi wasu cikin magabata sun sa'ba mata , kamar Abu Hanifa da wasunsa ? 


Amsa akan wannan ta fuskoki kamar haka : 


1. Lallai mas'ala tana zama daga cikin tussa na Aqidar Ahlussunah ta hanyoyi guda uku ( kamar yanda zancen da muka kawo a baya na Shaikhul Islam ya qunsa ) : ko dai hukuncin mas'alar ya zama bayyananne qarara acikin Alqur'ani , ko kuma Hadisai su tabbatar da ita ta hanyar Tawaturi , ko kuma Magabata su yi Ijma'i akanta 

Ko kuma mu ce : Duk mas'alar da bayaninta yake afili a fayyace acikin Alqur'ani ko Sunnah , sawa'un mas'alar Aqidace ko ta fiqhu ; to wannan mas'alar ta zama daga cikin tussa na Aqidar Ahlussunah ( kamar yanda Shaikhul Islam ya qarrara hakan acikin Majmu'ul Fatawa da Dar'u Ta'arudil Aqli wan Naqli ) .


 Shaikhul Islam ya ce : 


" بل الحق أن الجليل من كل واحد ( المسائل الاعتقادية والعملية ) مسائل أصول ، والدقيق مسائل فروع " 


( الفتاوى ، ٦/٥٦)


To ka ga kuwa wannan mas'alar bayaninta ya tabbata qarara acikin Hadisai Mutawaturai kuma an hikaito Ijma'in magabata akanta , don haka ba ya halatta a sa'ba acikinta .


2. Idan Nassosa suka tabbata akan mas'ala qarara , Sai wani Malami ko wasu Malamai su ka sa'ba acikin wannan mas'alar ; ba a izina da sa'bawarsu , sa'bawarsu bata sauya hukuncin mas'alar ; ba a 'daukar sa'bawar tasu a matsayin abun lura , a'a ana 'daukan hakanne garesu amatsayin zamiya da tuntu'be wanda ba ya sauya komai gameda mas'alar . 


Al Imam Abu Is'haq Ash Sha'diby yana cewa : 


 " فإذا كان بينا ظاهرا أن قول القائل مخالف للقرآن أو للسنة لم يصح الاعتداد به ، ولا البناء عليه " 


Hakanan yana cewa game da irin wannan sa'bawa : 


" إنه لا يصح اعتمادها خلافا في المسائل الشرعية ، لأنها لم تصدر في الحقيقة عن اجتهاد ، ولا هي من مسائل الاجتهاد ، وإن حصل من صاحبها اجتهاد فهو لم يصادف فيها محلا ، فصارت في نسبتها إلى الشرع كأقوال غير المجتهد . 

وإنما يعد في الخلاف الأقوال الصادرة عن أدلة معتبرة في الشريعة ، كانت مما يقوي أو يضعف . وأما إذا صدرت عن مجرد خفاء الدليل أو عدم مصادفته فلا . فلذلك قيل إنه لا يصح أن يعتد بها في الخلاف ، كما لم يعتد السلف الصالح بالخلاف في مسألة ربا الفضل ، والمتعة ، ومحاشي النساء ، وأشباهها من المسائل التي خفيت فيها الأدلة على من خالف فيها " 


( الموافقات في أصول الشريعة ، ٤/١٢٤)


Ibnu Asim Almaliky ya wa'ke ma'anar wannan zance na Sha'diby acikin littafinsa inda yake cewa :


وزلة العالم لا تعتمد ....... في مأخذ العلم ولا تقلد 

وفي الخلاف بعد لا يعتد ...... بها ولا في بابه تعد 

وإنما تذكر تنبيها على ....... أن يتحاشى مثلها إن نقلا 

وهي منافاة الدليل القطعي ...... المقتفى سبيله في الشرع 


(نيل المنى لابن عاصم ) 


Alhafizul Alhakamy shima yana cewa : 


وكل خُلف لا إلى برهان ..... وجوده ونفيه سيان 


( وسيلة الحصول إلى مهمات الأصول ) 


A wani wurin Sha'diby ya ce gameda sa'bawa acikin irin wannan mas'alar : 


" فأما المخالفة في القطعي فلا إشكال في اطراحه ، ولكن العلماء ربما ذكروه للتنبيه عليه وعلى ما فيه ، لا للاعتداد به " 


( الموافقات ، ٤/١٢٥)


Kai hatta acikin mas'aloli na ijtihadi Malamai sun yi ittifaqi akan cewa : ba ya halatta a yi aiki da ra'ayi mai rauni , kuma ambaton zantuka masu rauni acikin mas'aloli na ijtihadi ba dalili bane akan halascin dogaro akansu . 


Abdullahil Alawy yana cewa acikin Alfiyyarsa : 


 وذكر ما ضعف ليس للعمل ...... إذ ذاك عن وفاقهم قد انحظل .


( مراقي السعود لمبتغي الرقي والصعود ) 


Don haka , samun wasu 'dai'daikun Malamai su sa'bawa wata mas'ala da Nassoshi na Shari'a su ka tabbatar da ita , ko Ijma'i ya tabbata akanta ; hakan ba ya sauya mas'alar daga matsayinta , kuma ba ya halattawa wani sa'bawa dalilai na Shari'ah akan mas'alar , kuma ba a la'akari da wannan sa'bawar ta su . 

Don haka , sa'bawar Abu Hanifa ko waninsa akan wannan mas'alar ba ya rushe wannan Ijma'i na magabata , Kuma hakan ba ya mayar da mas'alar a matsayin mas'ala ta ijtihadi da ya halatta a yi sa'bani acikinta . 


Idan wani ya ce : To wace irin mas'alace ake la'akari da sa'bani acikinta , Kuma ya halatta a yi sa'banin acikinta ? 


Sai mu ce da shi : mas'alar da ya halatta a yi sa'bani acikinta itace : Duk mas'alar da ta zama dalilanta 'boyayyu ne , ko kuma akwai cin_karo azahiri tsakanin dalilan da su ka zo akanta , ko kuma ya zamana babu dalili kwata_kwata akanta Sai dai a yi qiyasi acikinta ; to wannan itace mas'alar da ya halasta a yi sa'bani acikinta , Kuma ba ya halatta a fasiqantar ko a kafirtar acikinta , ko a danganta wanda ya sa'ba acikinta zuwa ga 'bata . Ita tattaunawa ake yi acikinta domin shiryantarwa zuwa ga abunda ya fi kusanci da daidai , da bayanin ra'ayi mai rauni daga mai qarfi , da kuma qarfafan juna wurin bincike na ilimi da fa'da'dawa acikinsa , abun dogaro acikinta shine abunda ya fi kusa ga dalilai na Shari'ah da manufofinta . 

Misalin irin wannan shine : Galibin mas'alolin fiqhu da ake samun sa'bani tsakanin mazhabobin Fiqhu na Sunnah . 


Shaikhul Islam yana cewa : 


" و الصواب الذي عليه الأئمة أن مسائل الاجتهاد ما لم يكن فيها دليل يجب العمل به وجوبا ظاهرا ، مثل حديث صحيح لا معارض له من جنسه ، فيسوغ إذا عدم ذلك فيها الاجتهاد ، لتعارض الأدلة المتقاربة ، أو لخفاء الأدلة فيها " 


( بيان الدليل على بطلان التحليل ، ٩٤ ) 


Hakanan yana cewa :


" فإذا كان القول يخالف سنة أو إجماعا قديما وجب إنكاره وفاقا ، وإن لم يكن كذلك فإنه ينكر بمعنى بيان ضعفه " 


( بيان الدليل ، ٩٣)


Al Imam Ash Shafi'iy yana cewa wurin banbancewa tsakanin mas'alar da ya halatta a yi sa'bani acikinta da wacce ba ya halatta a yi sa'bani acikinta : 


" الاختلاف من وجهين : أحدهما محرم ، ولا أقول ذلك في الآخر .

كل ما أقام الله به الحجة في كتابه أو على لسان نبيه منصوصا بينا : لم يحل الاختلاف فيه لمن علمه .

وما كان من ذلك يحتمل التأويل ويدرك قياسا ، فذهب المتأول أو القايس إلى معنى يحتمله الخبر أو القياس ، وإن خالفه فيه غيره : لم أقل إنه يضيق عليه ضيق الخلاف في المنصوص " 


( الرسالة للشافعي ، ٥٣٦)


Anan Shafi'iy ya banbance mana tsakanin mas'alar da ya halatta a sa'ba acikinta da wacce bai halatta ba ; ya bayyana cewa duk mas'alar da nassi ya tabbata akanta qarara ; to ba ya halatta a yi sa'bani acikinta , wacce kuma babu nassin qarara akanta ; to ana iya sa'bawa acikinta . 


Idan wani ya ce : To yanzu ya za a yi gameda wasu 'dai'daikun magabata da aka samu sun sa'ba acikin irin mas'alolin da ba ya halatta a yi sa'bani acikinsu ? Shin za a bidi'antar da su ne ko kuma ya ya za a yi ? 


Amsa anan kamar haka : 


1. Da farko wajibine a kiyaye alfarma na Shari'a ; a tabbatar mata da abunda ta tabbatar , a kore mata abunda ta kore , a kira mutane zuwa ga abunda ta tabbatar , a ja kunnensu akan abunda ta haramta ; wannan wajibine a tsayu da shi ba tare da la'akari da sa'bawar mai sa'bawa ba . 


2. Duk wanda aka samu ya sa'ba acikin irin wa'dannan mas'aloli daga cikin magabata na qwarai , ko daga cikin Malamai mujtahidai wa'danda suke gudana akan tushe na Shari'ah ; to ana 'daukan wannan sa'bawar tasu ne amatsayin zamiya da tuntu'be ; ba ya halatta a yi musu biyayya akan sa'bawarsu , kuma wajibine a yi martanin wannan sa'bawar ta su tare da kiyaye musu mutuncinsu da darajarsu , kuma hakan ba ya hukunta fitarsu daga Sunnah saboda rashin gangantawarsu ga sa'bawa Shari'a . 


Shaikhul Islam ya na cewa :


" إن الرجل الجليل الذي له في الإسلام قدم صالح وآثار حسنة ، وهو من الإسلام وأهله بمكانة عليا ، قد يكون منه الهفوة والزلة ، وهو فيها معذور ، بل مأجور ، ولا يجوز أن يتبع فيها ، مع بقاء مكانته ومنزلته في قلوب المؤمنين " 


( بيان الدليل ، ٩٠)


 Sha'diby shima ya ce : 


 " إن زلة العالم لا يصح اعتمادها من جهة ، ولا الأخذ بها تقليدا له ، وذلك لأنها موضوعة على المخالفة للشرع ، ولذلك عدت زلة ...

كما أنه لا ينبغي أن ينسب صاحبها إلى التقصير ، ولا أن يشنع عليه بها ، ولا ينتقص من أجلها ، أو يعتقد فيه الإقدام على المخالفة بحتا ، فإن هذا كله خلاف ما تقتضي رتبته في الدين " 


( الموافقات ، ٤/١٢٣)

Wa'dannan bayanai suna tabbatar da abunda mu ka gabatar a baya , kuma suna bayar da amsa akan qalubalen da Malam Musa Asadussunnah ya jefo cewa : Shin Shi ma Abu Hanifa 'dan bidi'a ne tunda mun ce yin Khuruji ga Azzaluman Shuwagabanni bidi'ane ? 


Adunqule dai , mas'alar haramcin tawaye ga Azzaluman Shuwagabanni mas'alace da malamai su ka hikaito ijma'in Ahlussunah akanta , kuma ba ya halatta wani ya sa'ba acikinta , kuma qungiyoyin bidi'a sune su ka sa'bawa Ahlussunah akanta , kuma samun wasu 'dai'daikun magabata da su ka sa'ba acikinta ba ya warware Ijma'in magabata akanta , kuma hakan ba ya halatta sa'bawa shari'a saboda sa'bawarsu , kuma sa'bawar ta su ba ta hukunta bidi'ancinsu ko halatta mutuncinsu .

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter