Subscribe Our Channel

 Tsokaci akan Muhadarar Malam Musa Asadussunnah (2)

Daga cikin mas'alolin da Malam Musa ya ta'basu acikin wannan Muhadarar tasa akwai mas'alar yin tawaye ga Azzaluman Shuwagabanni ; Malam Musa yana ganin halascin yin hakan , yana mai kafa hujjah akan wannan ra'ayin nasa bisa ababe kamar haka :

1. Wai ai Abu Hanifa shima yana ganin halascin hakan 

2. Ba bu wanda ya bidi'antar da Abu Hanifa akan haka 

3. Tunda Abu Hanifa yana ganin hakan to mas'alace ta sa'bani kenan da ya halasta wani ya sa'bawa wani acikinta

A dunkule wa'dannan sune madogarar Malam Musa akan ganin halascin khuruji , har ma ya jefa qalubale ga abokan husumarsa akan su kawo masa wanda ya bidi'antar da Abu Hanifa akan wannan ra'ayi nasa ! 

Abun tambaya anan shine : shin da gaskene Abu Hanifa yana ganin halascin tawaye ga Azzaluman Shuwagabanni ? 

Malamai da dama sun ruwaito acikin littattafansu jinginawa Abu Hanifa ra'ayin halascin tawaye ga Azzaluman Shuwagabanni , zamu ambaci wasu daga cikinsu kamar haka :

1. Abdullahi bin Al'imamu Ahmad ya ruwaito daga almajirin Abu Hanifa ( Abu Yusuf) yana dangantawa Abu Hanifa wannan ra'ayi 

(السنة ، ١٨٢)

2. Ismail bin Harb ( Almajirin Al Imam Ahmad) shima ya ruwaito hakan daga Abu Is'haq Alfazary yana danganta wannan ra'ayi ga Abu Hanifa .

( السنة للكرماني ، ٢٨٩)

3. Ibnu Shahin shima ya ruwaito danganta wannan ra'ayi ga Abu Hanifa .

( شرح مذاهب أهل السنة ، ٣٣)

4. Alfasawy shima ya ruwaito hakan .

(المعرفة والتاريخ ، ٢/٧٨٨)

4. Al'uqaily shima ya ruwaito danganta hakan gareshi 

( الضعفاء ، ٤/٢٨٣)

Wa'dannan Malaman duk sun kawo wa'dannan ruwayoyinne da suka tabbatar da danganta wannan mummunan ra'ayi ga Abu Hanifa domin su yi suka akansa kuma su kushesa . 

Ba wannan ra'ayin ka'dai suka ruwaito dangantashi ga Abu Hanifa ba , a'a sun ruwaito danganta wasu munanan ra'ayoya ga Abu Hanifa , daga cikinsu ma har da ra'ayin da Malamai suke yin hukuncin kafirci ga ma'abocinsa , kamar aqidar cewa Alqur'ani halittane . 

Malaman Sunnah acikin littattafansu kamar littafin Assunnha ta Abdullahi bin Al'imamu Ahmad , da Assunnah na Alkirmany , da Sharhu mazahibu Ahlissunnah na Ibnu Shahin , da Ta'wilu Mukhtalafil Hadis na Ibnu Qutaibah , da wasu littattafan Sunnah masu tarin yawa ; sun ringa bu'de babi na musamman acikin littattafansu domin bayyana miyagun ra'ayoyin Abu Hanifa , da tahziri akansa , da kawo zantukan manyan Malaman Musulmi na zamaninsa da wa'danda suka zo bayansa da suka raunanasa , suka yi watsi da shi bisa munanan ra'ayoyinsa , kamar Al'imam Al'auza'iy , Al'imamu Malik , Al'imamu Ahmad , Al'imam Is'haq Ibnu Rahuyah , Hammad bin Salamah , Sufyan Ibnu Uyainah , Sulaiman bin Mihran Al A'amash , da sauransu .

Duka Malamai suna kawo wannanne ba don a yi koyi da Abu Hanifa acikin kurakuransa ba , ko don a 'dauki mas'alolin da Abu Hanifa ya sa'bawa Sunnah akansu a matsayin mas'aloli masu sauqi da ya halatta a yi sa'bani akansu , a'a sun yi hakane domin bayyanawa mutane munin ra'ayin Abu Hanifa acikin wa'dannan mas'aloli , da bayyana akasin ra'ayinsa amatsayin yardajjen matsaya ta magabata Ahlussunati Wal Jama'ah .

_________________________________

Duk da abunda aka ruwaito na tabbacin miyagun aqidu ga Abu Hanifa , to an samu wasu riwayoyi da suke nuna tubarsa daga wasu ra'ayoyin daga cikinsu ; kamar ra'ayin jahamiyyanci na cewa Alqur'ani halittane . Al Imam Albaihaqy ya ruwaito abunda yake nuna tubansa daga wannan ra'ayi daga almajirinsa Abu Yusuf . 

( الأسماء والصفات ، ٥٥١)

Hakanan abunda wasu Malaman Mazhabar Abu Hanifan suke ambatawa amatsayin aqidar shi Abu Hanifan _ duk da ba riwaya suke yi zuwa gareshi ba _ shima yana iya nuni akan cewa _ wata qila _ Abu Hanifan ya sauka daga wasu da dama daga cikin abunda ake danganta masa na sa'bawa Mazhabar Sunnah acikin wasu babuka na Aqida .

Daga cikin irin wa'dannan mas'aloli akwai mas'alar tawaye ga Azzaluman Shuwagabanni ; Abu Ja'afar Addahawy ya ambaci haramcin tawaye ga Azzaluman Shuwagabanni amatsayin aqidar Abu Hanifa acikin littafinsa na Aqida ( العقيدة الطحاوية).

Hakanan Al'imam Albazdawy cikin Malaman Hanafawan shima ya ambaci haramcin tawayen amatsayin ra'ayin almajiran limamin mazhabar tasu baki 'dayansu .

Yana cewa : 

" الإمام إذا جار أو فسق لا ينعزل عند أصحاب أبي حنيفة بأجمعهم ، وهو المذهب المرضي ، وعند القدرية والخوارج والروافض ينعزل " 

( أصول الدين للبزدوي، ١٩٦)

A taqaice dai , danganta ra'ayin halascin tawaye ga Azzaluman Shuwagabanni zuwa ga Abu Hanifa tabbatacce ne , Malamai sun tabbatar da hakan acikin littattafansu , kuma sun kawo hakanne domin aibantawa da kushewa ga Abu Hanifa . 

Sannan kuma wasu Malaman Mazhabar Abu Hanifan sun danganta masa sa'banin wannan ra'ayin , wanda hakan _ wata qila_ yana iya nuni akan saukansa daga wannan mummunan tafarki na Khawarijawa .

Don haka , Malaman da suka danganta masa wannan ra'ayi sun yi hakanne a bisa suka ga Abu Hanifa , da bayyana mummunan tafarkinsu domin nasiha ga Al'ummah , wa'danda suka danganta masa sa'banin haka kuma sun yi hakanne domin wanke shi daga wancan mummunan ra'ayi na sa'bawa Sunnah .

Da wannan zaka fahimci wauta a ilmance na Malam Musa ; ta yanda yake hujjah da sa'bawar Abu Hanifa ga Sunnah ( wanda akan hakan Malamai suka jarraha Abu Hanifa suka aibantasa suka tsoratar akansa ) ,wurin wai shima ya bijirewa Sunnar !! 

Wato Shi Malam Musa hujjah yake yi akan zunubin wani Malami domin ya halatta wannan zunubin ga kansa !!

Shi Malam Musa har yanzu bai san cewa a addinin Musulunci ba a yin hujja da kuskuren wani mai kuskure wurin halatta abunda Allah ya haramta ba .

Allah ya sawwake !

A addinin Musulunci ba a barin abunda ya tabbata a Shari'ah saboda sa'bawar wani mutum , Al'imam Ibnu Qutaibah yana cewa :

" ولا عذر في مخالفة رسول الله صلى الله عليه وسلم بعد العلم بقوله " 

( تأويل مختلف الحديث ، ١٠٧)

A rubutunmu na gaba za mu yi bayanine akan shin wannan mas'alar mas'alace mai sauqi da ya halatta a samu sa'bani akanta ?

Sheikhana Ateeq Sulaiman



 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter