Subscribe Our Channel

 Ka nemi ilimi akaron farko domin amfanin kanka :

قال الحافظ ابن رجب الحنبلي : 

قال بعض السلف : " بلغنا أن الذي يطلب الأحاديث ليحدث بها لا يجد ريح الجنة " 

قال الحافظ : يعني من ليس له غرض في طلبها إلا أن يحدث بها دون العمل بها " 

Ibnu Rajab ya ce : wani daga cikin magabata ya ce : " labari ya iso garemu cewa : Duk wanda yake neman ilimin hadisi kawai domin ya karantar da shi ; to ba zai ji 'kamshin Aljanna ba " 

Ibnu Rajab ya ce : ma'anar zancen shine : wanda yake neman ilimin ba don ya yi aiki da shi ba , a'a kawai yana nema ne domin ya karantar " 

( شرح حديث ما ذئبان جائعان ، ٥٨) 

Abun lura : 

1. Neman ilimi ibada ne , don haka wajibi ne a sanya ikhlasi acikinsa ; a nemi yardan Allah shi ka'dai awurin nemansa .

2. Neman ilimi ba don aiki da shi ba , sai kawai don neman daukaka awurin mutane ta hanyar malumtuwa akansu ; hakan hanyace ta shiga wuta , kuma hakan nau'i ne na shirka ga Allah acikin ibada . Manzon Allah ( s.a.w) ya tabbatar da cewa duk wanda yake neman ilimi don wannan manufar ; to yana daga cikin wanda za'a fara kunna wuta da su a ranar lahira ( Al'imamu Muslim ya ruwaito hakan daga cikin Hadisin Abu Huraira ) . 

3. Ba bu laifi idan Mutum yana neman ilimi don ya yi aiki da shi kuma ya karantar da shi , wannan ma shine nagartacciyar manufar neman ilimi . Amma nemansa don a karantar kawai ba don a yi aiki ba , wannan hanyar halaka ne .

✍️ ✍️ 

Ustaz Abu Ahmad Ateeq ( Hafizahullah)

11-march-2023

18-Shaaban-1444H



 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter