Tambaya ta 366:
JAM’I NA-BIYU A MASALLACI:
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah.
Waɗanda suka rasa jam’i amma sai kuma suka yi nasu jam’in a masallacin da limaminsu, to ko su ma jam’insu ya yi?
AMSA A366
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Malamai sun sha bamban a kan hukuncin maimaita sallar jam’i a cikin masallaci guda, amma abin da muka fi gamsuwa da shi shi ne:
Yin hakan makaruhi ne idan masallacin ya zama yana da limami ratibi tabbatacce da ladaninsa sananne, ban da wanda yake a wani wurin da mutane suke zuwa da wucewa kawai, kamar na kan hanya. Haka kuma idan ya zama masu sallar su kansu mutanen da suka saba yin sallah a masallacin ne, ban da kamar baƙi ko matafiya da suka shigo masallacin a makare bayan limamin ya kammala sallar.
Dalili a kan haka kuwa hadisin da Al-Imaam At-Tabaraaniy ya riwaito ne a cikin Al-Awsaat (4739) daga Sahabi Abu-Bakrah (Radiyal Laahu Anhu) cewa:
أَنَّ رَسُولَ اللهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ - أَقْبَلَ مِنْ نَوَاحِي الْمَدِينَةِ يُرِيدُ الصَّلَاةَ ، فَوَجَدَ النَّاسَ قَدْ صَلُّوا ، فَمَالَ إِلَى مَنْزِلِهِ فَجَمَعَ أَهْلَهُ ، فَصَلَّى بِهِمْ
Watarana Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya taho daga wani sashe na Madinah yana nufin samun sallah a masallaci, sai ya tarar da mutane sun riga sun yi sallar, don haka sai ya juya zuwa gidansa ya tara iyalinsa ya yi sallar tare da su. (Al-Albaaniy ya hassana shi a cikin Tamaamul Minnah, shafi: 155).
As-Shaikh Mash-huur (Hafizahul Laah) a cikin I’laamul Abid Bi-Hukmi Tikraaril Jamaa’ah Fil Masjidil Waahid ya nuna cewa: In da yin jam’i na-biyu halattacce ne ba da wani karhanci ba da kuwa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) bai bar falalar yin sallar da ke cikin Masallacin na Annabi ba.
Kuma Al-Hasan Al-Basariy (Rahimahul Laah) ya ce:
كَانَ أَصْحَابُ مُحَمَّدٍ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ - إِذَا دَخَلُوا الْمَسْجِدَ وَقَدْ صُلِّيَ فِيهِ ، صَلُّوا فُرَادَى
Sahabban Annabi Muhammad (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) sun kasance idan suka shiga masallaci suka tarar an riga an yi sallah, sai su yi sallah ɗai-ɗai. (Ibn Abi-Shaibah: 2/223).
Al-Imaam Abu-Haneefah da Al-Imaam Maalik da Al-Imaam As-Shaafi’iy (Rahimahumul Laahu Ta’aala) sun yarda cewa: Bai halatta a maimaita jam’i ba a cikin masallacin da yake da limami ratibi.
Hikimar wannan hanin kuma ita ce: A hana buɗe ƙofar raba kan al’umma, a janyo haɗuwar kansu a lokacin sallah. Domin a lokacin da mutane suka san cewa suna iya rasa jam’in gaba-ɗaya za su yi gaggawa wurin kintsawa da shiryawa domin zuwa masallaci da wuri a kan lokaci. Amma da zaran sun gano cewa ko da a bayan jam’in farko suna iya samun na-biyu, wannan zai sanya su riƙa yin sakaci, kuma ba za su damu ba.
Sannan kar a manta cewa: Hadisin da masu ganin halaccin maimaita jam’in suke kafa hujja da shi, watau:
« أَيُّكُمْ يَتَّجِرُ عَلَى هَذَا ». فَقَامَ رَجُلٌ فَصَلَّى مَعَه
Wanene daga cikinku zai yi sadaka ga wannan? Sai wani mutum ya miƙe ya yi sallah tare da shi. (Sahihi ne. Abu-Daawud: 574 da At-Tirmiziy: 220 suka riwaito shi).
Malamai sun tabbatar cewa babu hujja a cikinsa a kan abin da suke nunawa. Domin matuƙar abin da ke cikinsa kawai shi ne: Sallar jam’in mai nafila ce a bayan mai farilla a masallacin da limaminsa ratibi ya kammala sallar. A nan kuma ana tattauna magana a kan sallar mutanen da dukkansu ne suke yin jam’in farilla a bayan limamin masallacin ya kammala nasa da jama’a. Don haka yin ƙiyasin halinsu a kan hadisin ya zama Qiyas ma’al faariq kenan, wanda kuma bai halatta ba a fiqihiyance. (Al-Mausuu’atul Fiqhiyyatul Muyassarah: 1/250-253).
A ƙarshe dai, yana da kyau a nan mu maimaita cewa: Hukuncin wannan aikin na maimaita yin wannan jam’in makaruhi ne. Don haka waɗanda suka saɓa kuma suka yi jam’in na-biyu ba su kyauta ba ne kawai, amma sallarsu ta yi, in shaa’al Laah.
Allah ya ƙara mana shiriya.
Wal Laahu A’lam.
Muhammad Abdullaah Assalafiy
29/6/2020
10: 19pm.