Subscribe Our Channel

 DAGA INA MATSALAR TAKE ? (2)

A rubutunmu na farko mun kawo maganganun Shehu Tijjany inda yake tabbatar da munanan 'kudurorinsa na allantar da waliyyai da ma allantar da dukkan halittu .

A wancan rubutun mun ce a rubutu na gaba zamu kawo daga cikin zantukan Shehu Ibrahim Inyass inda shima yake tabbatar da wannan mummunar a'kida ta allantar da waliyyai da ma dukkan halitta , amma _har yanzu_ zamu cigaba da kawo wani shashe na maganganun Shehu Tijjany inda yake 'kara tabbatar da wannan a'kidar tasa ta allantar da halitta .

An tambayi Shehu Tijjany dangane da ma'anar fa'din Allah ma'daukaki :

"إنا عرضنا الأمانة على السماوات و الأرض و الجبال فأبين أن يحملنها و أشفقن منها و حملها الإنسان "

Ma'anar Amana da Allah ya bada labari cewa 'Dan Adam ya 'dauketa shine : dokoki na Shari'a ; na umarni da hani , hakanan kuma ma'anar "الإنسان " da Allah ya fa'da acikin Ayar shine : jinsi na Mutum .

Amma shi Shehu Tijjany sai ya fassara Kalmomin kamar haka :

"الأمانة هي القيام بحقوق مرتبة الحق في كلية معانيها خلقية و إلهية ، فلم تطق حمل هذا الأمانة السماوات و الأرض ، فأشفقن منها و حملها الإنسان ، و هو الإنسان الكامل الذي يحفظ الله به نظام الوجود ، وبه يرحم جميع الوجود ، وبه صلاح جميع الوجود ، و هو حياة جميع الوجود ، و به قيام جميع الوجود ، ولو زال عن الوجود طرفة عين واحد لصار الوجود كله عدما في أسرع من طرفة العين ، و هو المعبر عنه بلسان العامة قطب الأقطاب و الغوث الجامع " 

"Abunda ake nufi da wannan amanar shine : tsayuwa da ha'k'ko'kin matsayin Allah acikin dukkan ma'anonin matsayin ; ha'k'ki na halittawa da na bautantaka , amma sammai da 'kassai basu iya 'daukan wannan amanar ba , sai suka ji tsoro , amma sai Mutum ya 'dauki amanar , Mutumin da ake nufi shine cikakken Mutum ; shine wanda Allah yake kiyaye tsarin halittu ta hanyarsa , kuma ta hanyarsane yake tausayawa dukkan halittu , kuma ta hanyarsa gyaruwan dukkan halittu , kuma shine rayuwar dukkan halittu , kuma ta hanyarsa ne tabbatuwar dukkan halittu , da ace zai gushe daga kulawa da halittu daidai da 'kyaftawar ido , to da dukkan halittu an rasa su cikin 'kasa da 'kyaftawar ido , irin wannan Mutumin shine wanda gamagarin Mutane suke kiransa da 'KU'DUBI ko GAUSI"

( جواهر المعاني ، ٩٦/١)

A cikin wannan bayani na Shehu Tijjany , yana tabbatar da cewa Waliyyi 'Ku'dubi shine wanda Allah ya fawwala masa dukkan matsayi na Allah ; ya fawwala masa halittan halittu , kuma ya fawwala masa rainon halittun gaba 'dayansu , kuma ya fawwala masa al'amarin bauta ; wato ya yarje masa ya zama shine abun bautan halittu .

A wani wurin Shehu Tijjany ya 'kara fayyace maganar 'karara inda ya tabbatar da cewa : Shi waliyyi shine wanda Allah ya ajiyeshi amadadinsa ; don haka dolene ya zama yana 'dauke da ma'anar wanda yake amadadinsa ( Allah ) ; ta yanda zai zama ya mamaye dukkanin ma'anoni na ubangijintaka da allantaka , wanda da haka ne zai kiyaye dukkan halittu .

Ga bayanansa kamar haka :

" من استخلفه الحق لا بد أن يكون فيه معنى ما من مستخلفه ، و هو احتواؤه على جميع الأسماء الكونية الإلاهية ، التي بها نظام الكون و قوامه " 

( جواهر المعاني ، ١١٤/١)

A wani wurin kuma ya 'kara bayani 'karara cewa : dukkan bawan da Allah ya bayyana acikin sirrinsa , to zai mallaka masa dukkan sirrikan komai ; sai ya zama yana jujjuya dakkan al'amuran halittu bisa zatinsa ; da zaran ya yi nufin faruwan wani abu to nan take abun zai faru .

Ga maganar tasa nan kamar haka :

" إذا تجلى الله لسر عبد ملكه جميع الأسرار ، و ألحقه بدرجة الأحرار ، وكان له تصرف ذاتي ، متى توجهت إرادته لأي شيئ خارق كان انخرق له في الحين ، إلا أن بعضهم يضيف لها كلمة "كن" ، وبعضهم بمجرد الإرادة " 

( جواهر المعاني ، ١٩٧/٢)

Hakanan ya 'kara bayani 'karara cewa Waliyyi wanda yake a madadin Allah , dukkan al'amuran halittu suna hannunsa ; shike yanda yaga dama da halittu , aduk inda Allah yake ubangiji shine a madadin Allah a wurin , kuma babu wata halitta da take fita daga ikon wannan waliyyi .

Ga shinan inda yake tabbatar da wannan batu :

" إن الله اتخذ خليفته في الأكوان من هذا الجنس ( الإنسان) ، وهو ال,فرد الجامع ، و هو محيط بالعالم كله ، والعالم كله في قبضته و تحت حكمه وتصرفه ، يفعل فيه كلما يريد بلا منازع ولا مدافع ، و قصارى أمره أنه كان حيثما كان الرب إلها كان هو خليفة عليه ، فلا خروج لشيئ من الأكوان عن ألوهية الله تعالى ، كذلك لا خروج لشيئ من الأكوان عن سلطة هذا الفرد الجامع ، يتصرف في المملكة بإذن مستخلفه " 

( جواهر المعاني ، ٢٣٠/٢)

A wani wurin kuma ya ce dangane da wannan Waliyyi : shine ruhi na dukkan halittu , babu wani bagire a duniya face wannan waliyyin shike da iko akan wannan bagire ...

Ga maganarsa daga bakinsa :

" هو الروح في جميع الموجودات ، فما في الكون ذات إلا هو الروح المدبر لها ، و المحرك لها ، و القائم فيها ، ولا في كورة العالم مكان إلا و هو حال فيه متمكن منه " 

" Shine ruhi acikin dukkan halittu , babu wani jiki a duniya face wannan waliyyin shine ruhin dake jujjuya wannan jiki , kuma shike motsa wannan jikin , kuma shine mai tsayar da wannan jikin , a fa'din duniya gaba 'daya babu wani bagire face wannan waliyyin yana nan awannan bagire kuma yana da cikakken iko akan wannan bagire " 

( جواهر المعاني ، ٢٢٥/٢)

Kai Shehu Tijjany dai ya 'kar'kare magana inda ya ce : wannan waliyyi 'ku'dubi shine yake kar'ban rayukan halittu , kuma shine zai busawa matattu rai su tashi , shike sanya bishiya ta yi 'ya'ya ....

Yana cewa :

" يفعل ما يريد في كل ما أراده ، يحي الموتى إذا شاء ، و يناديها فتجيبه مسرعة و لو كانت رميمة ، ويثمر الشجرة اليابسة في الحين إذا شاء " 

"Waliyyin yana aikata abunda yaga dama cikin dukkan abunda ya nufa , idan yaga dama sai ya rayar da matattu , kuma idan yaga dama zai kira mushe sai ta amsa masa cikin gaggawa koda kuwa mushen ya rududduge , kuma idan yaga dama sai yasa bishiyar da ta bushe ta fitar da 'ya'ya nan take " 

( جواهر المعاني ، ٢٢٥/٢)

A cikin wa'dannan maganganu na Shehu Tijjany dukkansu abunda yake tabbatarwa shine : Waliyyi 'Ku'duby shine yake halittan dukkan halittu , kuma shine yake kar'ban rayukansu , kuma shine yake jujjuya al'amuransu , kuma idan halittun sun yi bauta to shi suke bautamawa ...

Babu shakka wannan a'kida kafirci ce ; dukkan wanda ya sha'ki 'kamshin Musulunci ba za'a yi sa'bani da shi ba akan ka'fircin wannan a'kida .

Idan Shehu Tijjany ya bayyana matsayin Waliyyi 'Ku'duby bisa wannan ma'ana , to ba zaka yi shakka ba idan ka ji wani batijjane da ya yarda da Shehu Tijjany ya allantar da shi Tijjanin , ko wani daga cikin Shehinnan 'dari'ka bisa hujjar cewa ai wannan shehin waliyyi ne 'ku'dubi !!

Shehu Tijjany ya fa'da'da allantarwar da yake 'kudurcewa ga wasu halittu , har ya kai ga yana ganin komai ma Allah ne !!!

Yana kasa Mutane gida uku : 

1. wa'danda suke bautan Allah a matsayinsa na mahaliccinsu abun bautansu ; wa'dannan a wurinsa sune gamagari masu bauta ( mabiya Annabawa ) .

2. Wa'danda suke ganin dukkan abunda suke yi Allah ne ya hukunta musu haka ( don haka su babu wani abu da yake haramun awurinsu saboda Allah ne ya hukunta musu dukkan abunda suke yi ) : Shehu Tijjany yana kwarzanta wannan kaso , amma yana ganin tawayarsu ta yanda suke ganin cewa akwai Allah daban sannan kuma akwai halitta ; abunda ya dace shine su daina ganin banbanci tsakaninsu da Allah ; a'a su 'dauka kawai cewa suma Alloli ne , saboda bisa ha'ki'ka kowa ma Allah ne !! 

3. Wa'dannan sune wa'danda suke ganin suma Alloli ne ; saboda kowa ma Allah ne !! 

Wa'dannan sune masu kamala awurin Shehu Tijjany , su ko sun yi wata bauta to Allah ne yake bautawa Allah , idan Allah ya baka wani abu , to Allah ne ya bawa Allah ...

Su ma'obota wannan mataki basa 'kudurta samuwan wani abu a matsayin halitta , a'a , su a wurinsu kowa ma Allah , babu abunda ba Allah ba !!!

Ga nan bayanin nasa daga bakinsa :

"الناس ثلاثة : قوم هم بشهود ما منهم إلى ؛ و هم العباد و العامة .

وقوم هم بشهود ما من الله إليهم ، و هم الخاصة .

وقوم هم بشهود ما من الله إلى الله .

فالخاصة الأولى و إن كانوا في غاية العلو فيلحقهم النقص من حيث يشهدون أن الله هو المهدي لهم و المعطي ، فنقصهم هو شهود وجودهم مع وجود الحق سبحانه و تعالى ، و الكمال و التمام للطائفة الثانية : هم بشهود ما من الله إلى الله ، فليس لنفوسهم عندهم شأن حتى يعطيها أو يهدي إليها ، بل انحمق وجودهم تحت وجوده ، فلا أين ولا كيف ولا غيرية إلا الله وحده ، فهذا هو الكمال . هو المعطي لا غيرية ، بل هو من عند نفسه لنفسه ، إذا ارتفع الحجاب شهدت العالم كله شأنا من شؤون الحضرة الأحدية ، فليس إيراده الأشياء إلا منه لنفسه ، والعالم كله شؤونه ، وهذا المشهد هو مشهد الأفراد " 

( جواهر المعاني ، ٢٤٣/٢)

A bayanansa yana ganin wa'danda suke 'daukan cewa komai Allah ne sune cikakku , kuma ba kowa ne yake dacewa ba ga kaiwa wannan matakin sai wane_da_wane .

Wannan matakin shine matakin Siddi'kai a wurinsa ; sune wa'danda suke ganin komai ma Allah ne , basa 'daukan kansu a matsayin halitta .

Yana 'kara bayani akan wa'danda suka kai wannan matsayi sai yake cewa :

" خرقوا حجاب الظواهر و بلغوا من باطن الألوهية إلى رتبة حق اليقين ، فما الكون عندهم كله إلا صفات الله و أسماؤه " 

"Waliyyai Siddi'kai sun yage shamaki na zahirin halittu ( wanda yake shamakance mahajubi daga ganin 'daukar komai a matsayin Allah) , sai suka isa zuwa ga gaskiyar ya'kini ( tabbatar da allantakar komai ) ta hanyar ba'dinin allantaka , don haka su a wurinsu dukkan halittu ba komai bane face sifofin Allah da sunayensa " 

( جواهر المعاني ، ١١٠/١)

 A wani wurin kuma Shehu Tijjany yana 'kara tabbatar da wannan a'kida tasu sai yake cewa : koda ababe ne marasa rai za su ji suna cewa su Allah ne , to tabbas su zasu tabbatar cewa lallai wannan abun Allah ne .

Ga maganarsa kamar haka :

" فأنا لو سمعنا كلاما من جماد تكلم و قال إنني أنا الله لا إله إلا أنا فاعبدني ، لكان ذلك الجماد هو الإلاه " 

" Lallai mu da zamu ji wani daskararren abu zai yi magana ya ce :lallai nine Allah babu abun bauta sai ni " , tabbas da zai tabbata shi 'din Allah ne " 

(جواهر المعاني، ١٠٤/١)

Wa'dannan wani sashe ne na zantukan Shehu Tijjany inda yake tabbatar da a'kidarsu ta allantar da komai .

Don haka , ayau duk wani 'Dan Tijjaniyyah da ya bayyana yana allantar da wani shehi , ko ya game duka ya ce kowa ma Allah ne , to maganarsa ba sabuwa bace ; a'a tana da asali acikin 'Dari'kar Tijjaniyyah , asalin wanda ya 'kir'kiri 'dari'kar shima wannan itace a'kidarsa . 

Duk wanda ka ji yana inkari akan masu bayyana wannan a'kidar ayanzu cikin mabiya Tijjaniyyah , yana cewa wai su ba 'Yan Tijjaniyyah bane , ko ya ce wai Turakun Tijjaniyyar ba haka suke ba , to wannan mutumin 'dayan mutane biyu ne :

Ko dai ya jahilci 'dari'kar Tijjaniyyar ; magana kawai yake da jahilci , ko kuma munafiki ne wanda yake 'boye ha'ki'kanin mummunan a'kidarsa ta kafirci , kamar yanda su Shehu Tijjanin da Khalifofinsa suka ja kunnen mabiyansu da su ringa 'boyewa jama'a irin wannan munanan 'kudurori na kafirci , kamar yanda zamu kawo maganganunsu akan haka nan gaba .



Rubutunmu na gaba zai yi bayani ne akan maganganun Inyaas na tabbatar da allantakar Shehu Tijjani da ma allantakar komai .


Allah ya kiyaye mana imaninmu , ya ku'butar da wa'danda suka halaka bisa jahilci .

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter