DAGA INA MATSALAR TAKE ?
A duk lokutan zagayowar bukukuwa Maulidin Shehu Ibrahim Inyas da 'yan 'Dariqar Tijjaniyyah suke gudanarwa ; akan samu 'bullowar wasu saututtuka daga wasu mabiya 'Dari'kar Tijjaniyyar , wanda sautukan suka 'kunshi allantar da wasu shehinnai da fifitasu akan Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam , da dai wasu miyagun maganganu na kafirci da munafurci .Wasu daga cikin jagororin Tijjaniyya sun fito sun yi tur ga masu bayyanawa'dannan a'kidu na kafirci , kuma suka bayyana barrantarsu daga mummunan tafarkinsu , kuma suka yi da'awar barrantar matafiyar wa'dannan mutane daga ha'ki'kanin matafiyar Tijjaniyya .Babu shakka akwai da yawa daga cikin mabiyan Tijjaniyya wa'danda basa 'kudurce irin wa'dannan miyagun a'kidu na kafirci wa'danda wa'dannan mutane suke bayyanawa da sunan 'dari'kar Tijjaniyyah , amma fa abunda muke inkari shine : da'awar da ake yi cewa wai Shehu Tijjany da Shehu Ibrahim sun barranta daga matafiyar wa'dannan 'Yan ha'ki'ka masu allantar da shehinnai , ko kuma ace wai su ba 'Yan tijjaniyya bane !Mu abunda muke cewa shine : bisa ha'ki'ka wa'dannan mutane masu allantar da shehinnai sune mabiya Tijjaniyyah na asali , kuma sune masu koyi na gaskiya ga Shehu Tijjany da Shehu Inyass , Saboda bisa ha'ki'ka ita 'dari'kar Tijjaniyyar 'dari'ka ce da Shehu Tijjany ya girka ta bisa turaku na a'kidar allantar da komai , da halatta komai . Akan haka yagina 'dari'karsa , kuma shima abunda yake 'kudurtawa kenan , shima Shehu Ibrahim hakan shine a'kidarsa , kuma abunda ya yita ya'dawa kenan tsakanin mabiyan 'darikarsu .
Zamu kawo wasu zantuka daga bakin Shehu Tijjany wa'danda suke tabbatar da cewa lallai yana 'kudurta a'kidar allantar da wasu halittu da ma allantar da dukkan halittu .
1. MAGANGANUN SHEHU TIJJANY NA ALLANTAR DA WALIYYAI :
Shehu Tijjany ya ce :
" و حقيقة أنه يسلب من جميع الصفات البشرية ، و يتحلى با لأخلاق الإلاهيةظاهرا و باطنا "
" Ha'ki'kanin Waliyyi shine wanda za'a zare masa dukkan sifofin mutumtaka , sai ya 'kawatu da sifofin Allah zahirinsa da ba'dininsa "
( جواهر المعاني ، ٢/ ١٥٣)
Hakanan yana cewa :
" لو كشف عن حقيقة الولي لعبد ، لأن أوصافه من أوصاف إلهه و نعوته مننعوته ، لأنه ينسلخ من جميع الأوصاف البشرية ، كما تنسلخ الشاة من جلدها ، و يلبس خلعة الأخلاق الإلاهية ، فلو كشف للعبد لعبد الولي "
" Da za'a bayyana ha'kikanin waliyyi to da an ringa bauta masa ; saboda sifofinsa jinsin sifofin Allansa ne , kuma kamanninsa jinsin kamannin Allah ne , kuma shi waliyyi yan sa'bulewa daga dukkan sifofi na mutumtaka kamar yanda ake sa'bule Akuya daga fatarta , sai ya sanya tufa na 'dabi'ar Allantaka , don haka , da za'a yiwa mutane bayanin ha'ki'kanin waliyyi to da an koma bautarsa "
( جواهر المعاني ، ١٥٣/٢)
A wani wurin kuma ya ce :
" إن للعارف وقتا يطرأ عليه الفناء و الاستغراق ، حتى يخرج عن دائرة حسه و شهوده ، ويخرج عن جميع مداركه و وجوده ، لكن تارة يكون ذلك في ذات الحق سبحانه وتعالى ، فيتدلى له من قدوس اللاهوت من بعض أسراره فيضا ، يقتضي منه أنه يشهد أن ذاته عين ذات الحق لمحقه فيها واستهلاكه فيها ، و يصرح في هذا الميدان بقوله : سبحاني لا إله إلا أنا وحدي "
"Lallai Waliyyi Ãrifi yana da wani lokaci da fana'i yake bijiro masa , ta yanda zai fita daga yanayi na jin samuwarsa da halarto kansa , amma a wani lokaci yana samun hakan ne acikin zatin Allah , to daga nan sai wasu sirrika na tsarkin allantaka su gangaro su zu'bo acikin wannan Waliyyin , wanda da wannanne waliyyin zai ringa jin cewa lallai zatinsa shine tsantsan zatin Allah , saboda ya riga ya 'kare acikin zatin Allah , a irin wannan bagiren ne sai waliyyin ya bayyana cewa : Tsarki ya tabbata gareni , babu abun bauta sai ni ka'dai "
( جواهر المعاني ، ١٥٢/٢)
An tambayi Shehu Tijjany dangane da ma'anar matsayin 'ku'dubanci saiyake cewa :
" اعلم أن حقيقة القطبانية هي الخلافة العظمى عن الحق مطلقا ، في جميع الوجود جملة و تفصيلا ، حينما كان الرب إلها كان هو خليفة في تصريف الحكم و تنفيذه ، في كل ما عليه ألوهية الله تعالى ، ثم قيامه بالبرزخية العظمى بين الحق و الخلق ، فلا يصل إلى الخلق شيئ كائنا ما كان من الحق إلا بحكم القطب و تنفيذه و توليه ، ونيابته عن الحق في ذلك "
( جواهر المعاني ، ١٥٨/٢)
A dun'kule abunda Shehu Tijjany yake cewa anan shine :
Shi waliyyi 'Ku'dubi shine wanda yake a madadin Allah a duk inda Allah yake abun bauta ; shi ke zantar da hukunci akan dukkan halittu , babu wani abu da wani abun halitta zai samu daga Allah face sai ta hanyar wannan Waliyyin ; shike wakiltan Allah a wurin raba arzi'kin halittu .Hakanan yana bayanin ma'anar maganar Shaikh Ahmad zarruq inda yake cewa : ya ke iska , ki tsaya haka da izinina "
" يا ريح اسكني عليهم بإذني "
sai Shehu Tijjany ya ce :
"معنى ذلك أنه خليفة استخلفه الحق على مملكته تفويضا عاما ، أن يعمل في المملكة كلما يريد "
"Ma'anar haka shine : Allah ne ya ajiyesa a madadinsa adukkan masarauta ta Allah , ya fawwala masa komai fawwalawa gamamme ; ta yanda zai ringa aikata abunda yaga dama acikin masarautar Allah "
(جواهر المعاني، ١٥٨/٢)
2. MAGANGANUNSA DA SUKE NUNA CEWA KOMAI ALLAH NE :Shehu Tijjany ya ce :
" اعلم أن أذواق العارفين في ذات الوجود ، أنهم يرون أعيان الموجودات كسراب بقيعة ، فما في ذوات الوجود كله إلا الله سبحانه وتعالى تجلى بصورها و أسمائها ، وما ثَمّ إلا أسماؤه و صفاته ، فظاهر الوجود صور الموجودات ، صورها و أسماؤها ظاهرة بصورة الغير و الغيرية ، وهو مقام أصحاب الحجاب الذين حجبوا بظاهر الموجودات عن مطالعة الحق فيها ، وإنما مرتبة الصديقين الكون عندهم معتقد فقط ، و الظاهر المحض إنما هو وجود الحق وحده في كل شيئ"
"Ka sani lallai abunda waliyyai Arifai suke ji dangane da zatin halittu shine : su suna ganin zatin halittu kamar kawalwalniya ne kawai ) abunda zaka yi tsammanin samunsa daga nesa , amma idan ka matso kusa sai ka tarar babu shi ( , amma bisa ha'ki'ka babu abunda ke cikin zatin halittu gaba 'dayansu sai Allah , shine kawai ya bayyana a surar daake gani na halittun da sunayensu , amma fa babu komai acikin zatin halittun sai sifofin Allah da sunayensa , don haka zahirin halittu hotonsune kawai ) amma ha'ki'kaninsu Allah ne ( , hotonsu da sunayensu shine a zahiri suke nuna cewa su sun banbanta da Allah , wannan kuma shinematsayar Mahajubai ;wa'danda zahirin halitta ya shamakance su daga 'kudurta samuwar Allah acikin halittar .Amma matsayar Siddi'kai itace : su halittu tabbatar da samuwarsu magana ce kawai , amma abunda yake tsantsan zahirin magana shine ; samuwar Allah shi ka'dai acikin zatin dukkan halitta "
( جواهر المعاني ، ١٦٦/٢)
Shehu Tijjany ya ce :
" فكل عابد أو ساجد لغير الله في الظاهر فما عبد ولا سجد إلا لله تعالى : لأنه هو المتجلي في تلك الألباس...ولو أنها برزت لعبادة الخلق و برزت له بدون تجليه فيها لتحطمت في أسرع من طرفة عين ،لغيرته سبحانه وتعالى لنسبة الألوهية لغيره تعالى ...قال تعالى : " لا إلاه إلا أنا " يعني لا معبود غيري ، و إن عبد الأوثان من عبدها ، فما عبدوا غيري ولا توجهوا با لخضوع و التذلل "لغيري ، بل أنا المعبود فيهم
(جواهر المعاني ،٧٦/٢)
Adun'kule abunda yake cewa shine : duk wanda ka ganshi yana bautan wanin Allah a zahiri , ko yana masa sujjada , to bisa ha'ki'ka Allah yake bautamawa , kuma Allah yake yiwa sujjada ; saboda Allah ne ya bayyanaacikin jikin wannan halittan , don haka bisa ha'ki'ka Allah yake bautamawa ba wannan abun halittan ba . Kuma da ace Allah bai bayyana ba acikin jikin wannan abun halittar har ake bauta masa , ai da abun halittar ya tarwatse saboda tsananin kishin Allah , amma tunda daihar abun halittar bai tarwatse ba alokacin da make bauta masa , to babushakka Allah ne ya bayyana acikin sa , don haka masu bautan Allah suke bautamawa .
Shehu Tijjany ya ce Ibnu Araby ya ce :
" قلت لهرون : يا نبي الله : قوله فلا تشمت بي الأعداء ، أين العدو الذي تشير إليه ؟ و هل ثم شيئ خارج عن الله تعالى ؟ أو كما قال له ، و أنا معشر العارفين نرى كل شيئ هو الله ، فكيف يتصور أن يكون عدوا ؟ قال له سيدنا هرون عليه الصلاة و السلام : ما ترونه كذلك هو الله في نفس الأمر ، قال له هرون : فاتك من الله بقدر ما فاتك من معرفته "
" Ibnu Araby ya ce wa Annabi Harun : wai me kake nufi da ka cewa Annabi Musa : kada ka sanya Ma'kiya su yi min dariya " , dama akwai wani abune wanda ba Allah ba ? ai mu waliyyai Arifai muna ganin cewa komai ma Allah ne , to ta yaya za'a ce akwai wani abokin gaba ? sai Annabi Haruna ya ce masa : e, duk abunda kake ganin bisa ha'ki'ka Allahne ya bayyana a yanda halittar take , don haka , Allah zai su'buce maka gwargwadon yanda ka jahilci ha'kikaninsa"
(جواهر المعاني ، ١٨٦/٢)
Wa'dannan maganganu na Shehu Tijjany dukkansu suna nuni akan cewa lallai halitta yana iya zama Allah , saboda Allah yana bayyana acikin halittunsa , kamar yanda kiristoci suke fa'din haka dangane da Annabi Isa .
Babu shakka wannan a'kida kafirci ne mummuna , Musulmi sun yi ijma'i akan kafircin dukkan wanda ke 'kudurta allantakar wani abun halitta , Allah da kansa ya kafirta kiristoci yayin da suka 'kudurta allantakar Annabi Isa bisa cewa wai Allah ne ya sauko acikin jikinsa ,don haka shima ya zama Allah .
Allah yana cewa :
"لقد كفر الذين قالوا إن الله هو المسيح بن مريم "
Ibnu Hajar Alhaitamy duk da cewa shima gawurtaccen Sufy ne amma ya tabbatar da ijma'in Musulmi akan Kafircin Sufayen da suke 'kudurce cewa Allah yana sauka acikin jikin wasu halittu , yana cewa a sharhinsa ga hadisin waliyyi wanda wa'dannan sufaye suke ri'kewa a matsayin hujjarsu na allantar da waliyyansu :
" و زعم الاتحادية و الحلولية بقاء هذا الكلام على حقيقتة ، و أنه تعالى عين عبده أو حال فيه ... ضلال و كفر إجماعا ، فاحذرهم ، فإنهم ربما لبسوا على ضعفاء العقول ، فاستهووهم و أضلوهم ، لتزييهم بزي الصوفية ، والصوفية بريؤون منهم ، فقاتلهم الله أنى يؤفكون "
( الفتح المبين ، ٦٠١)
Hakama Al'kali Iyadw Almaliky ya tabbatar da ijma'in Musulmi akan Kafircin dukkan wanda yake 'kudurta allantar da wani abun haliitta tare da Allah , ko saukowar Allah acikin jikinsa , ko kuma 'kudurta samuwan wanda ke jujjuya al'amuran halittu koma bayan Allah , yana cewa :
" إن كل مقالة صرحت بنفي الربوبية أو الوحدانية أو عبادة أحد غير الله أو مع الله فهي كفر ، كمقالة الدهرية ...
أو أن ثَمّ صانعا للعالم سواه ، أو مدبراغيره ، فذلك كله كفر بإجماع المسلمين ، كقول الإلهيين من الفلاسفة و المنجمين و الطبائعيين ، و كذلك من ادعى مجالسة الله و العروج إليه و مكالمته أو حلوله في أحد الأشخاص ، كقول بعض المتصوفة و الباطنية و النصارى و القرامطة "
"Lallai dukkan zancen da ya fayyace kore ubangijintaka na Allah , ko ka'daituwarsa acikin haka , ko bautan wani koma bayana Allah , ko kuma bautansa tare da Allah , kamar zancen 'Yan Dahriyya ...
Ko kuma zancen ya bayyana cewa akwai wani mahaliccin halittu koma bayan Allah , ko kuma akwai wani mai jujjuya al'amuran halittu koma bayan Allah , duka wannan kafirci ne bisa ijma'in Musulmi , kamar zancen ILHIYYUN daga 'kungiyar Falasifa , da ALMUNAJJIMUN , da 'DABA'I'IYYUN , hakanan muna 'kudurta kafircin wanda yake da'awar zama tare da Allah , ko hira da shi , ko kuma ya 'kudurta saukowar Allah acikin jikin wani abun halitta , kamar yanda wasu SUFAYE suke 'kudurtawa , da BA'DINIYYA da KIRISTOCI da 'KARAMI'DA "
( الشفاء بتعريف حقوق المصطفى ، ٢٨٤/٢)
Saboda haka , alalha'ki'ka abunda muke gani yanzu na allantar da shehinnai da ake yi , ko ma allantar da komai , wanda mabiya 'Dari'kar Tijjaniyyah suke yi , duka sun koyoshine daga 'dari'kar tasu ta Tijjaniyyah ; saboda shi kanshi wanda ya 'kir'kiro 'dari'kar hakan shine a'kidarsa , kuma Musulmi sun yi Ijma'i akan kafircin duk wanda yake 'dauke da wannan A'kida .
A rubutunmu na gaba zamu tsakura daga maganganun Shehu Inyaas inda yake 'kudurta allantakar Shehu Tijjany , da ma allantakar komai , da kuma inda wasu almajiransa suke allantar da shi kuma ya tabbatar da su akan haka .