Daga cikin gujewan magabata game da Riya :
Ibnu Rajab Alhanbaly ya ce :
"كان إبراهيم النخعي إذا دخل عليه أحد وهو يقرأ المصحف غطاه "
" Ibrahim Al Nakha'iy ya kasance idan yana karanta Alqur'ani sai wani ya shigo wurinsa , sai ya rufe ' Qur'anin "
( شرح حديث ما ذئبان جائعان، ٧٠ )
Abun lura :
1. Tsananin nisantar magabata game da Riya .
2. Nisan da ke tsakaninmu da magabata wurin nisantar riya ; su magabata kullewa kawunansu 'kofofin riya suke yi , mu kuma riyar itace ma asalin ayyukanmu !
Wasu masu wa'azi da 'daliban ilimi saboda fitinar riya ta cinyesu ; hatta karatun da zai yi tsakaninsa da matarsa sai ya yayatashi a duniya kowa ya gani , wani kuma idan ya tafi aikin Hajji ko Umara , to duk wani motsinshi acan sai ya dauko shi ta hanyar hoto ko video ya yadawa duniya kowa ya gani , wani kuma ko karatu zai yi acikin mota sai ya daukowa duniya ya nuna mata .
Allah ya yaye mana wannan mummunan 'dabi'a ta riya .
✍️ ✍️
Ustaz Abu Ahmad Ateeq (hafizahullah)
10-03-2023
17-shaaban-1444H