CIKAKKEN SHARHIN HADISIN BIYAYYA GA SHUWAGABANNI :
Shekara shida da suka wuce mun ta'ba yin sharhi ga shahararren Hadisin nan ; Hadisin Al'irbad bin Sãriya , ta hanyar fito da wasu fa'idoji da Hadisin ya 'kunsa ta 'bangaren hani game da bidi'a da kuma hukuncin ta a cikin Addini .
A yau _ in Allah ya yarda _ zamu yi magana ne akan ga'ba ɗaya daga cikin ga'bo'bin hadisin wacce take magana akan wajibcin biyayya ga shuwagabanni .
Ga nassin ga'bar Hadisin :
" ﺃﻭﺻﻴﻜﻢ ﺑﺘﻘﻮﻯ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭ ﺟﻞ ، ﻭﺍﻟﺴﻤﻊ ﻭ ﺍﻟﻄﺎﻋﺔ ، ﻭﺇﻥ ﺗﺄﻣﺮ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻋﺒﺪ "
( ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ : ٤٦٠٧ ، ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ : ٢٦٧٦، ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ : ٤٢ )
Zamu fitar da fa'idojin da wannan ga'bar ta 'kunsa ta hanyoyi kamar haka :
1. wannan hadisin yana nuna wajibcin biyayya ga Shuwagabanni a duk yanda suke ; ma'ana shin nagartattu ne su ko ko Azzalmai ne marasa adalci .
Saboda lafazin " ﺍﻟﺴﻤﻊ ﻭﺍﻟﻄﺎﻋﺔ " da su ka zo a cikin hadisin lafuzza wa'danda suke masdarai ( ﻣﺼﺪﺭ ) kuma tattare da su akwai 'kamshin fi'ili , ma'ana zasu yi aikin da fi'ilansu suke yi ; ko dai yiwa fa'ili ruf'a ( ﺭﻓﻊ ﺍﻟﻔﺎﻋﻞ ), ko kuma yiwa maf'uli Nasba ( ﻧﺼﺐ ﺍﻟﻤﻔﻌﻮﻝ ) , bisa gwargwadon 'dabi'ar fi'illan su na samarwassu ga maf'uli ko ta'kaituwarsu ga fa'ili ( ﺍﻟﻠﺰﻭﻡ ﻭﺍﻟﺘﻌﺪﻱ ) .
To su wa'dannan lafuzza anan asalin fi'illansu suna samar da maf'uli , ta'kadirin jumlar idan an maida kalmomin zuwa fi'illansu shine kamar haka :
" ﻭﺃﻥ ﺗﺴﻤﻌﻮﺍ ﻭ ﺗﻄﻴﻌﻮﺍ ﺃﻣﺮﺍﺀﻛﻢ "
Saboda haka , tuddan dai fi'illan kalmomin 'dabi'ar su itace Samar da maf'uli ( ﺍﻟﺘﻌﺪﻱ ) , to haka ma ya kamata masdarin su su zama matu'kar masdaran sun cika sharu'd'dan haka , to kuma anan wa'dannan masdarai sun cika sharu'd'dan saboda fi'ili tare da harafin " An " ( ﺃﻥ ) suna yiwuwa su zauna a makwafin masdaran , kuma a lafazin su na masdari suna 'dauke da harafin "Alif da lamun " ( ﺍﻝ) , wanda kuma siffantuwar masdari da wa'dannan sifofi yana daga cikin fuskar da take halasta gudanar da magudanar fi'ilin sa .
Ibnu Malik ya ce :
ﺑﻔﻌﻠﻪ ﺍﻟﻤﺼﺪﺭ ﺃﻟﺤﻖ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﻤﻞ * * ﻣﻀﺎﻓﺎ ﺃﻭ ﻣﺠﺮﺩﺍ ﺃﻭ ﻣﻊ ﺍﻝ .
ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻓﻌﻞ ﻣﻊ ﺃﻥ ﺃﻭ ﻣﺎ ﻳﺤﻞ * * ﻣﺤﻠﻬﺎ ﻭ ﻻﺳﻢ ﻣﺼﺪﺭ ﻋﻤﻞ .
To idan muka fahimci wannan sai muga a lafazin Hadisin Annabi bai fa'di maf'uli ba ga wa'dannan lafuzza , sai ya ce :
" ﻭﺍﻟﺴﻤﻊ ﻭ ﺍﻟﻄﺎﻋﺔ ﻭ ﺇﻥ ﺗﺄﻣﺮ ﻋﻠﻴﻜﻢ ..."
Rashin ambaton abunda ke da ala'ka da wa'dannan lafuzza anan yana nuni akan fa'idoji biyu _ a iya abunda muka iya hararowa _ a wurin malaman Balaga :
* Ba'a ambaci Kalmar da take ala'kantuwa da Masdarin bane saboda an ambaci lafazin da yake fayyace ha'ki'kaninsa a cikin zancen da ya biyo baya ; inda Annabi ya ce :
" ﻭ ﺇﻥ ﺗﺄﻣﺮ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻋﺒﺪ "
Kenan wannan lafazin yana fayyace ibhamin da aka yi wurin rashin fayyace ha'ki'kanin maf'uli wanda yake ratayuwa ga wa'dannan masdarai guda biyu .
Ta'kadirin jumlar sai ya zama kamar haka :
" ﻭﺍﻟﺴﻤﻊ ﻭﺍﻟﻄﺎﻋﺔ ﻟﻸﻣﺮﺍﺀ ﻭﺇﻥ ﺗﺄﻣﺮ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻋﺒﺪ "
irin wannan salon zancen ya zo a cikin Al'kur'ani , inda Allah yake cewa :
" ﻭ ﻟﻮ ﺷﺎﺀ ﻟﻬﺪﺍﻛﻢ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ "
Anan Allah bai ambaci maf'ulin fi'ilin " ﺷﺎﺀ " ba , saboda lafazin da ya zo baya ya fayyace shi " ﻟﻬﺪﺍﻛﻢ "
Ta'kadirin Ayar sai ya zama :
" ﻭﻟﻮ ﺷﺎﺀ ﻫﺪﺍﻳﺘﻜﻢ ﻟﻬﺪﺍﻛﻢ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ "
zuwa da zance a bisa irin wannan salo yana daga cikin dalilan da suke sa a goge maf'uli ga Kalmar da take da bu'katuwa zuwa gare shi a wurin malaman Balaga .
Ibnu Shihnah Alhalaby yana bayanin dalilan da suke hukunta
share maf'uli ga fi'ili sai yake cewa :
" ﻭ ﺍﻟﺤﺬﻑ ﻟﻠﺒﻴﺎﻥ ﻓﻴﻤﺎ ﺃﺑﻬﻤﺎ ** ﺃﻭ ﻟﻤﺠﻲﺀ ﺍﻟﺬﻛﺮ ﺃﻭ ﻟﺮﺩ .
* Fa'idar goge maf'ulin shine gamewa ( ﺍﻟﺘﻌﻤﻴﻢ ) ; wato
umurni da biyayya ya game dukkan nau'ukan shuwagabanni ;
sawa'un Adilai ne ko Azzalumai , Musulmi ne ko kafiri .
Bisa
haka sai mu fitar da Natija kamar haka :
* wajibi ne biyayya ga shugaba a duk yanda yake ; Musulmi
ne ko kafiri , Adali , ko Azzalumi , saboda daga cikin fa'idojin
share maf'uli a wurin malaman Balaga akwai fa'idantar da
game hukunci .
Ibnu Shihnah yana cewa acikin littafin sa " ﻣﺄﺓ ﺍﻟﻤﻌﺎﻧﻲ ﻭ ﺍﻟﺒﻴﺎﻥ
" game da fa'idojin share maf'uli :
" ﺃﻭ ﻫﻮ ﻟﻠﺘﻌﻤﻴﻢ ﺃﻭ ﻟﻠﻔﺎﺻﻠﺔ * * ﺃﻭ ﻫﻮ ﻻﺳﺘﻬﺠﺎﻧﻚ ﺍﻟﻤﻘﺎﺑﻠﺔ .
Don haka babu wanda ya halatta a wareshi daga wannan
gamammen sa'ko na umurni da biyayya ga ko wane irin
shugaba sai wanda dalili ya ware shi ya haramta biyayya
gareshi .
wanda dalili na shari'a ya wareshi kuwa shine shugaba Kafiri ,
shi baya halatta ayi masa biyayya matu'kar Kafircin sa ya
tabbata , wajibine ma a sauke shi daga shugabancin matu'kar
akwai iko akan haka .
Hadisin Ubadah bin Samit shine ya ke'bance kafirin shugaba
daga rashin wajibcin yi masa biyayya , inda Annabi yake
cewa :
" ﺇﻻ ﺃﻥ ﺗﺮﻭﺍ ﻛﻔﺮﺍ ﺑﻮﺍﺣﺎ ﻋﻨﺪﻛﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻴﻪ ﺑﺮﻫﺎﻥ "
( ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ : ٧٠٥٦ )
Saboda haka Adalin shugaba Musulmi da Azzalumi dukkan su
suna nan cikin gamammen umurnin Annabi na biyayya ga
shuwagabanni , musamman ma an samu wasu hadisai
tabbatattu da suka 'kara tabbatar da biyayya ga Azzaluman
Shuwagabanni a ke'be , kamar Hadisin Ibnu Mas'ud inda
Annabi yake cewa :
" ﺇﻧﻜﻢ ﺳﺘﺮﻭﻥ ﺑﻌﺪﻱ ﺃﺛﺮﺓ ، ﻭ ﺃﻣﻮﺭﺍ ﺗﻨﻜﺮﻭﻧﻬﺎ " . ﻗﺎﻟﻮﺍ : ﻓﻤﺎ ﺗﺄﻣﺮﻧﺎ ﻳﺎ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ؟ ﻗﺎﻝ : " ﺃﺩﻭﺍ ﺇﻟﻴﻬﻢ ﺣﻘﻜﻢ ﻭ ﺳﻠﻮﺍ ﺍﻟﻠﻪ ﺣﻘﻜﻢ "
( ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ : ٧٠٥٢ )
2. lafzin " ﻭ ﺇﻥ ﺗﺄﻣﺮ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻋﺒﺪ " Shi lafazin " ﺇﻥ " yana nuni ne
akan rashin tabbatuwar aikin da aka sanya shi a matsayin
shara'di , ko kuma 'karancin sa .
kenan ma'anar jumlar itace kamar haka :
" ko da ta yiwu wani wula'kantaccen Bawa ya shugabantu
akan Ku duk da cewa hakan yana da wahalar aukuwa , to
idan hakan ya auku Ku yi masa biyayya "
wannan shine Asalin ma'anar da lafazin yake nuni zuwa gare
shi a wurin malaman Balaga ,akasin sa shine lafazin " ﺇﺫﺍ " ;
shi yana fa'idantar da tabbacin faruwàn aiki da yawaituwar
Sa , shi yasa galibi fi'ilin da yake zuwa bayansa a matsayin
shara'di yake zuwa a sura ta Aikin da ya gabata ( ﺍﻟﻔﻌﻞ
ﺍﻟﻤﺎﺿﻲ ) , domin ishara zuwa ga tabbacin samuwan shara'din
kamar kace gashinan a auke , sa'banin lafazin " ﺇﻥ " ; wanda
shi Galibi shara'din sa yakan zo a sura ta mudari'i , domin
ishara zuwa ga rashin tabbas wurin samuwar sa .
Misalin wannan Acikin Alqur'ani shine fa'din Allah ma'daukaki
:
" ﻭﺇﺫﺍ ﺃﺫﻗﻨﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺭﺣﻤﺔ ﻓﺮﺣﻮﺍ ﺑﻬﺎ "
Anan da yake rahamar Allah tana da yalwa kuma bata rabuwa
da mutane a kowane lokaci , sai Allah ya yi Amfani da lafazin
" ﺇﺫﺍ " domin nuni zuwa ga tabbacin samuwar rahamar ga
mutane da yawaitar rahamar , shi yasa maf'ulin yazo a siga
ta " Nakirah" ; wacce take nuni akan yawaituwa ( ﺍﻟﺘﻜﺜﻴﺮ ).
Amma da Allah zai yi magana akan kishiyar rahamar _ wacce
take qanqanuwa ce idin aka dangantata da Rahama _ sai ya
ce :
" ﻭ ﺇﻥ ﺗﺼﺒﻬﻢ ﺳﻴﺌﺔ ..."
Anan sai ya yi amfani da lafazin " ﺇﻥ " domin ishara zuwa ga
qarancin samuwar musiba ga mutane idan aka kwatanta da
samuwar rahama , shi yasa ma aka zo da fa'ilin " ﺳﻴﺌﺔ " a
sura ta "NAKIRAH" ; wacce anan take nuni akan 'karanci
" ( ﺍﻟﺘﻘﻠﻴﻞ ).
Al'imamu Assuyu'dy ya yi bayanin ma'anonin wa'dannan
lafuzza _a wurin malaman Balaga _ a cikin Alfiyyar sa ta
Balaga , inda yake cewa :
" ﻓﻐﻴﺮ ﻟﻮ ﻟﻠﺸﺮﻁ ﻓﻲ ﺍﺳﺘﻘﺒﺎﻝ *** ﻟﻜﻦ ﺇﻥ ﺗﺨﺘﺺ ﺑﺎ ﻟﻤﺤﺎﻝ .
ﻟﻜﻮﻧﻬﺎ ﻓﻲ ﺍﻷﺻﻞ ﻟﻠﺬﻱ ﻋﺪﻡ *** ﺟﺰﻣﺎ ﻭ ﻋﻜﺴﻬﺎ ﺇﺫﺍ ﻣﻦ ﺛﻢ ﻋﻢ "
Saboda haka anan Annabi yana umurni ne da biyayya ga
shugaba koda kuwa shugabancin nasa ya samu ne ta wata
irin hanya wacce take baquwa ga mutane .
3. Umurni da ya zo a wannan Hadisi na biyayya ga shugaba
ya zo ne a sake ( ﻣﻄﻠﻖ ) ، wato umurni da biyayya gareshi a
kowane hali ; biyayya gareshi akan aikin 'da'a da aikin sa'bo .
Amma wasu hadisai sun iyakance 'da'ar da za'a yi masa ;
cewa 'da'a ce a cikin abundà bai sa'bawa shari'a ba .
Hadisin Abdullah bin Mas'ud yana tabbatar da wannan , inda
Annabi yake cewa :
" ﺍﻟﺴﻤﻊ ﻭ ﺍﻟﻄﺎﻋﺔ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺮﺀ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﻓﻴﻤﺎ ﺃﺣﺐ ﻭ ﻛﺮﻩ ﻣﺎ ﻟﻢ ﻳﺆﻣﺮ
ﺑﻤﻌﺼﻴﺔ ، ﻓﺈﺫﺍ ﺃﻣﺮ ﺑﻤﻌﺼﻴﺔ ﻓﻼ ﺳﻤﻊ ﻭ ﻻ ﻃﺎﻋﺔ "
( ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ : ٧١٤٤ )
Acikin wannan akwai martani ga 'kungiyoyin bidi'a na
Mu'tazila da Khawarij wa'danda suke halatta tawaye ga
shugaba akan sa'bo , hakanan akwai martani ga wasu jama'a
da suka bayyana a tarihi , wa'danda ake musu laqabi da "
ALMARWANIYYAH " wa'danda suke ganin ana yiwa shugaba
biyayya acikin komai !! , da kuma Qungiyar Shi'a Rafidha ;
wa'danda suke ganin wajibcin biyayya ga limamansu acikin
dukkan komai .
Saboda Annabi bai saryar da biyayya ba ga shugaba gaba
'daya saboda ya yi umurni da sa'banin shari'a , a'a sai ya
wajabta biyayya gareshi a inda bai sa'ba da shari'a ba , kuma
ya haramta hakan a inda ya sa'bawa shari'ah.
Wannan matsakaiciyar matsaya itace mazhabar Ahlussunnati
waljama'a gameda biyayya ga shuwagabanni , Shaikhul Islam
yana cewa :
" ﺇﻧﻬﻢ ( ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ) ﻻ ﻳﺠﻮﺯﻭﻥ ﻃﺎﻋﺔ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻓﻲ ﻛﻞ ﻣﺎ ﻳﺄﻣﺮ ﺑﻪ ، ﺑﻞ
ﻻ ﻳﻮﺟﺒﻮﻥ ﻃﺎﻋﺘﻪ ﺇﻻ ﻓﻴﻤﺎ ﺗﺴﻮﻍ ﻃﺎﻋﺘﻪ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﺸﺮﻳﻌﺔ ، ﻓﻼ ﻳﺠﻮﺯﻭﻥ
ﻃﺎﻋﺘﻪ ﻓﻲ ﻣﻌﺼﻴﺔ ﺍﻟﻠﻪ ﻭ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﺇﻣﺎﻣﺎ ﻋﺎﺩﻻ "
( ﻣﻨﻬﺎﺝ ﺍﻟﺴﻨﺔ ، ٤ /٨٦ )
4. lafazin " ﺗﺄﻣﺮ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻋﺒﺪ " , yana nuni akan wajibcin biyayya
ga shugaba koda kuwa shugaban ya shugabantu akan mutane
ne ta hanyar mur'kushe da 'karfin makami da tursasasu har
ya haye kan madafan iko .
Abunda yake tabbatar da wannan ma'anar shine lafazin " ﺗﺄﻣﺮ
" , saboda ma'aunin lafazin a ilimin sarfu shine " ﺗﻔﻌّﻞ" , shi
kuma wannan wazani daga cikin ma'anoninsa a wurin
malaman sarfu akwai : " ﺍﻟﺘﻜﻠﻒ " , ma'ana zagewa da
jajaircewa akan cimma wani abu .
Kenan wannan lafazin yana tabbatar da wajibcin biyayya ga
wanda ya dafe madafan iko koda kuwa hakan ya yiwu gareshi
ne tahanyar sanya 'karfi da mur'kushe mutane har ya cimma
zama shugaba akansu .
Babu shakka matu'kar mutum ya iya mur'kushe mutane da
'karfi alokacin da babu mulki tattare da shi , to idan har ya
kai ga ya dafe madafan iko akansu , babu shakka wa'dannan
mutane basu da wata maslaha garesu da ta wuce biyayya
gareshi . Saboda matu'kar basu iya nasara akan shi ba Kafin
ya zama shugaba to babu yanda zasu iya da shi bayan ya
zama shugaba akansu .
Wannan ya sa Mazhabar Magabata ta gudana akan tabbatar
da abunda wannan lafazi yake hukuntawa ; na wajibcin
biyayya da haramcin tawaye ga Shugaban da ya haye
madafan iko ta hanyar 'karfin makami , Al'imam Ahmad bin
Hanbal ya ce :
" ﻭ ﺍﻟﺴﻤﻊ ﻭﺍﻟﻄﺎﻋﺔ ﻟﻸﻳﻤﺔ ﻭ ﺃﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ؛ ﺍﻟﺒﺮ ﻭ ﺍﻟﻔﺎﺟﺮ ، ﻭﻣﻦ ﻭﻟﻲ
ﺍﻟﺨﻼﻓﺔ ، ﻭﺍﺟﺘﻤﻊ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻋﻠﻴﻪ ، ﻭ ﺭﺿﻮﺍ ﺑﻪ ، ﻭ ﻣﻦ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺑﺎ ﻟﺴﻴﻒ
ﺣﺘﻰ ﺻﺎﺭ ﺧﻠﻴﻔﺔ ﻭ ﺳﻤﻲ ﺃﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ "
( ﺃﺻﻮﻝ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻟﻺﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ ، ٧ )
Ibnu Ba'd'dal Almaliky ya hikaito ijma'in Malamai akan
tabbatar da ma'anar da wannan lafazi ya ke nunawa , yana
cewa :
" ﻭ ﻗﺪ ﺃﺟﻤﻊ ﺍﻟﻔﻘﻬﺎﺀ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﻟﻤﺘﻐﻠﺐ ﺗﻠﺰﻡ ﻃﺎﻋﺘﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ
ﻣﻌﻪ ﻭ ﺃﻥ ﻃﺎﻋﺘﻪ ﺧﻴﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﺨﺮﻭﺝ ﻋﻠﻴﻪ ، ﻟﻤﺎ ﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﺣﻘﻦ
ﺍﻟﺪﻣﺎﺀ "
( ﺣﺎﺷﻴﺔ ﺍﻟﺘﺎﻭﺩﻱ ﺑﻦ ﺳﻮﺩﺓ ﻋﻠﻰ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ، ٦ / ٣٥٠ )
5. Lafazin " ﺗﺄﻣﺮ " yana iya nuni akan 'kulluwan Shugabancin
Shugaba ta hanyar shugabantarwar da masu wu'ka da Nama
a jagorancin mutane sukai masa ( ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺤﻞ ﻭ ﺍﻟﻌﻘﺪ ) , saboda
lafazin yana iya zama "MU'DAWI' " ne ( ﺍﻟﻤﻄﺎﻭﻉ ) na lafazin "
ﺃﻣّﺮ " , wanda hakan kuma yana daga cikin ma'anar ma'aunin
lafazin ( ﺗﻔﻌّﻞ) a Ilimin Sarfu .
Kenan ma'anar jumlar itace :
" koda masu fa'da _ aji daga cikinku sun shugabantar da
Bawa akanku , kuma bawan ya shugabantu , to Ku yi masa
biyayya "
Bisa wannan ma'anar , sai lafazin ya zama ya dace _ a
ma'ana _ da lafazin riwayar Bukhari daga hadisin Anas bin
Malik , inda Annabi yake cewa :
" ﺍﺳﻤﻌﻮﺍ ﻭ ﺃﻃﻴﻌﻮﺍ ﻭ ﺇﻥ ﺍﺳﺘﻌﻤﻞ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻋﺒﺪ ﺣﺒﺸﻲ ﮔﺄﻥ ﺭﺃﺳﻪ ﺯﺑﻴﺒﺔ
"
( ﺑﺨﺎﺭﻱ ، ٧١٤٢ )
Hakanan ma'anar lafazin ya dace da riwayar Muslim , daga
Hadisin Ummul Hasin , Annabi yake cewa :
" ﺍﺳﻤﻌﻮﺍ ﻭ ﺃﻃﻴﻌﻮﺍ ﻭ ﺇﻥ ﺃﻣﺮ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻋﺒﺪ ﺣﺒﺸﻲ ﻣﺠﺪﻉ "
Bisa wannan ma'anar , lafazin hadisin yana tabbatar da
wajibcin biyayya ga shugaba wanda masu fa'da _aji cikin
mutane suka shugabantar , koda kuwa mutane basa sonsa ,
kuma samuwan shugabanci ta wannan fuskar kar'ba'b'be ne a
shari'a . wannan shine mazhaba ta Ahlussunnah , Ibnu
Taimiyyah yana cewa :
" ﺍﻹﻣﺎﻣﺔ ﻋﻨﺪﻫﻢ ( ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ) ﺗﺜﺒﺖ ﺑﻤﻮﺍﻓﻘﺔ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺸﻮﻛﺔ ﻋﻠﻴﻬﺎ ، ﻭﻻ
ﻳﺼﻴﺮ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﺇﻣﺎﻣﺎ ﺣﺘﻰ ﻳﻮﺍﻓﻘﻪ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺸﻮﻛﺔ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﺤﺼﻞ ﺑﻄﺎﻋﺘﻬﻢ
ﻟﻪ ﻣﻘﺼﻮﺩ ﺍﻹﻣﺎﻣﺔ ...
ﻭﻟﻬﺬﺍ ﻗﺎﻝ ﺃﺋﻤﺔ ﺍﻟﺴﻨﺔ : ﻣﻦ ﺻﺎﺭ ﻟﻪ ﻗﺪﺭﺓ ﻭ ﺳﻠﻄﺎﻥ ﻳﻔﻌﻞ ﺑﻬﻤﺎ ﻣﻘﺼﻮﺩ
ﺍﻟﻮﻻﻳﺔ ﻓﻬﻮ ﻣﻦ ﺃﻭﻟﻲ ﺍﻷﻣﺮ "
( ﻣﻨﻬﺎﺝ ﺍﻟﺴﻨﺔ ، ١/١٤١ )
Sannan wannan ma'anar da lafazin yake 'dauka _ har wa yau
_ tana nuni akan wajibcin biyayya ga shugaba wanda yake
'kar'kashin shugabancin Shugaba Babba wanda ya
shugabantar da shi a wani sashe na sassan jagorancin
Mutane , kamar Al'kalanci , ko limanci , ko Gwamna , ko wata
ma'aikata daga cikin ma'aikatu na Gwamnati .
Saboda làfazin " ﺗﺄﻣﺮ " yana iya 'daukan cewa : shugabane
mai
babban shugabanci ya shugabantar da Bawan a wani reshe
daga cikin rassa na jagoranci , sai Bawan ya shugabantu .
Acikin wannan akwai martani ga malaman da suka taqaita
wajibcin biyayya ga Azzalumin Shugaba ga Shugaba mai
babban shugabanci ; su ka banbanta tsakanin mai 'karamin
shugabanci da kuma mai babban shugabanci .
Rashin banbancewa tsakanin su wurin wajibcin biyayya
garesu shine abunda wannan hadisin ya tabbatar , ko dai ta
hanyar 'kiyasi ( ﺍﻟﻘﻴﺎﺱ ﺍﻷﻭﻟﻮﻱ ، ﺃﻭ ﻓﺤﻮﻯ ﺍﻟﺨﻄﺎﺏ ) a bisa
ma'anar da lafazin ya 'dauka a wannan lamba , ko kuma ta
hanyar abunda lafazin ya nuna a zahiri a bisa ma'anarsa ta
lambar da ta gabata .
Hakanan kuma Hadisin Abu Huraira yana 'kara tabbatar da
rashin banbancewa tsakanin su , inda Annabi yake cewa :
" ﻭ ﺃﻥ ﺗﻨﺎﺻﺤﻮﺍ ﻣﻦ ﻭﻻﻩ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﺃﻣﺮﻛﻢ "
( ﻣﺴﻠﻢ : ١٧١٥ )
Anan Annabi ya yi bayanin wajibcin tsantsanta bayar da
ha'k'ki ne na shugaba a sake ( ﻋﻠﻰ ﺍﻹﻃﻼﻕ ) , bai
dabaibaye shugabancin ba da wata sifa ba sa'banin wanin ta
; ma'ana bai ce ba :
" ﻣﻦ ﻭﻻﻩ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﺃﻣﺮﻛﻢ ﻭﻻﻳﺔ ﻋﻈﻤﻰ "
ko kuma :
" ﻭﻻﻳﺔ ﺻﻐﺮﻯ "
ko kuma :
" ﻭﻻﻳﺔ ﻋﺎﺩﻟﺔ "
ko kuma :
" ﻭﻻﻳﺔ ﺟﺎﺋﺮﺓ "
Da ya zama Annabi baki dabaibaye lafazin ba da wata sifa ba
daga cikin wa'dannan sifofi , hakan yake nuna dukkan su
suna iya shiga cikin lafazin .
Saboda haka rabewa tsakanin babban shugabanci da 'karami
wurin wajibcin biyayya ga shugaba , rabewa ne da ya
sa'bawa shari'a da lafiyayyen hankali ; domin rabewa ne
tsakanin ababe biyu da shari'a ta ha'dasu wuri guda .
Ibnu Taimiyyah yana magana akan wannan mas'alar sai yake
cewa :
" ﺇﻥ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻗﺪ ﺗﻨﺎﺯﻋﻮﺍ ﻓﻲ ﻭﻟﻲ ﺍﻷﻣﺮ ﺍﻟﻔﺎﺳﻖ ﻭ ﺍﻟﺠﺎﻫﻞ ، ﻫﻞ ﻳﻄﺎﻉ
ﻓﻴﻤﺎ ﺃﻣﺮ ﺑﻪ ﻣﻦ ﻃﺎﻋﺔ ﻭ ﻳﻨﻔﺬ ﺣﻜﻤﻪ ﻭ ﻗﺴﻤﻪ ﺇﺫﺍ ﻭﺍﻓﻖ ﺍﻟﻌﺪﻝ ، ﺃﻭ ﻻ
ﻳﻄﺎﻉ ﻓﻲ ﺷﺊ ﻭ ﻻ ﻳﻨﻔﺬ ﺷﺊ ﻣﻦ ﺣﻜﻤﻪ ﻭ ﻗﺴﻤﻪ ، ﺃﻭ ﻳﻔﺮﻕ ﻓﻲ ﺫﻟﻚ
ﺑﻴﻦ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﻷﻋﻈﻢ ﻭ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻘﺎﺿﻲ ﻭ ﻧﺤﻮﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﻔﺮﻭﻉ ﻋﻠﻰ ﺛﻼﺛﺔ
ﺃﻗﻮﺍﻝ : ﺃﺿﻌﻔﻬﺎ ﻋﻨﺪ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻫﻮ ﺭﺩ ﺟﻤﻴﻊ ﺃﻣﺮﻩ ﻭ ﺣﻜﻤﻪ ﻭ ﻗﺴﻤﻪ ،
ﻭ ﺃﺻﺤﻬﺎ ﻋﻨﺪ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﻭ ﺃﺋﻤﺔ ﺍﻟﻔﻘﻬﺎﺀ ﻫﻮ ﺍﻟﻘﻮﻝ ﺍﻷﻭﻝ ؛ ﻭ ﻫﻮ ﺃﻥ
ﻳﻄﺎﻉ ﻓﻲ ﻃﺎﻋﺔ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻄﻠﻘﺎ ﻭ ﻗﺴﻤﺘﻪ ﺑﺎ ﻟﻌﺪﻝ ﻋﻠﻰ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻘﻮﻝ ، ﻛﻤﺎ
ﻫﻮ ﻗﻮﻝ ﺃﻛﺜﺮ ﺍﻟﻔﻘﻬﺎﺀ ، ﻭﺍﻟﻘﻮﻝ ﺍﻟﺜﺎﻟﺚ ﻫﻮ ﺍﻟﻔﺮﻕ ﺑﻴﻦ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﻷﻋﻈﻢ ﻭ
ﻏﻴﺮﻩ ، ﻷﻥ ﺫﻟﻚ ﻻ ﻳﻤﻜﻦ ﻋﺰﻟﻪ ﺇﺫﺍ ﻓﺴﻖ ﺇﻻ ﺑﻘﺘﺎﻝ ﻭ ﻓﺘﻨﺔ ، ﺑﺨﻼﻑ
ﺍﻟﺤﺎﻛﻢ ﻭ ﻧﺤﻮﻩ ، ﻓﺈﻧﻪ ﻳﻤﻜﻦ ﻋﺰﻟﻪ ﺑﺪﻭﻥ ﺫﻟﻚ ، ﻭﻫﻮ ﻓﺮﻕ ﺿﻌﻴﻒ ؛ ﻓﺈﻥ
ﺍﻟﺤﺎﻛﻢ ﺇﺫﺍ ﻭﻻﻩ ﺫﻭ ﺍﻟﺸﻮﻛﺔ ﻟﻢ ﻳﻤﻜﻦ ﻋﺰﻟﻪ ﺇﻻ ﺑﻔﺘﻨﺔ ، ﻭﻣﺘﻰ ﻛﺎﻥ
ﺍﻟﺴﻌﻲ ﻓﻲ ﻋﺰﻟﻪ ﻣﻔﺴﺪﺓ ﺃﻋﻈﻢ ﻣﻦ ﻣﻔﺴﺪﺓ ﺑﻘﺎﺋﻪ ﻟﻢ ﻳﺠﺰ ﺍﻻﺗﻴﺎﻥ
ﺑﺄﻋﻈﻢ ﺍﻟﻔﺴﺎﺩﻳﻦ ﻟﺪﻓﻊ ﺃﺩﻧﺎﻫﻤﺎ ، ﻭ ﻛﺬﻟﻚ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﻷﻋﻈﻢ ، ﻭ ﻟﻬﺬﺍ ﻛﺎﻥ
ﺍﻟﻤﺸﻬﻮﺭ ﻣﻦ ﻣﺬﻫﺐ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺃﻧﻬﻢ ﻻ ﻳﺮﻭﻥ ﺍﻟﺨﺮﻭﺝ ﻋﻠﻰ ﺍﻷﺋﻤﺔ ﻭ
ﻗﺘﺎﻟﻬﻢ ﺑﺎﻟﺴﻴﻒ ﻭ ﺇﻥ ﻓﻴﻬﻢ ﻇﻠﻢ ، ﻛﻤﺎ ﺩﻟﺖ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ
ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ ﺍﻟﻤﺴﺘﻔﻴﻀﺔ "
( ﻣﻨﻬﺎﺝ ﺍﻟﺴﻨﺔ ، ٨٦ / ٤ )
6. lafazin " ﺇﻥ ﺗﺄﻣﺮ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻋﺒﺪ " , yana nuni akan cewa wajibine
biyayya ga shugaba koda kuwa Bawa ne sawu'un Bawan
Azzalumi ne ko ko Adali ne . Abunda yake tabbatar da
wannan ma'anar shine ; gamewar ma'ana da lafazin " ﻋﺒﺪ"
yake 'dauke da ita a cikin hadisin , saboda shi lafazin Surassa
sura ce ta " ﻧﻜﺮﺓ " wacce aka ambaceta abayan shara'di ;
zuwa da lafazi a irin wannan yanayi yana hukunta gamewar
hukuncin da aka tabbatar ga lafazin ga dukkan abunda yake
iya 'daukan ma'anar Sa , wannan 'ka'ida ce shahararriya a
wurin Malaman Usulul fiqh , Shehinmu yana cewa a lokacin
da yake bijiro da sigogin da suke hukunta gamewar hukunci :
" ﻭﻣﺎ ﺃﺗﻰ ﻧﻜﺮﺓ ﻓﻠﺘﻌﻠﻢ ** ﻋﻨﺪ ﺳﻴﺎﻕ ﺷﺮﻁ ﺍﻭ ﻣﺴﺘﻔﻬﻢ .
Saboda haka , zuwa da wannan lafazi a wannan yanayi yana
'kara tabbatar da fa'idar da muka gabatar a lamba ta 'daya
cewa : wajibcin biyayya ga shuwagabanni ya game dukkan
wanda yake amsa sunan Shugaba ; sawa'un Adali ne ko
Azzalumi .
7. lafazin " ﻋﺒﺪ " , lafazi ne wanda aka danganta masa wani
hukunci ( ﻣﺴﻨﺪ ﺇﻟﻴﻪ ), kuma anzo da shi a sura ta " ﻧﻜﺮﺓ " ،
hakan yana fa'idantar da bayanin wula'kantuwa da
'kas'kancin sha'anin wanda aka danganta masa wannan
hukunci .
Ma'anar jumlar shine :
" koda ta yiwu wani wula'kantaccen Bawa 'kas'kantacce ya
shugabantu akanku ,to Ku yi masa biyayya "
a larabce sai jumlar ta zama :
" ﻭ ﺇﻥ ﺗﺄﻣﺮ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻋﺒﺪ ﻣﺴﺘﺤﻘﺮ ﻣﻬﺎﻥ ﻓﺎﺳﻤﻌﻮﺍ ﻭ ﺃﻃﻴﻌﻮﻩ "
Wannan fa'idar tana daga cikin fa'idojin da Suna ( ﺍﻻﺳﻢ )
Nakirah ( ﺍﻟﻨﻜﺮﺓ ) yake 'dauka idan aka zo dashi a matsayin
wanda aka jingina masa wani hukunci .
Ibnu Shihna Alhalaby yana cewa akan wannan batu :
" ﻭ ﺇﻥ ﻣﻨﻜﺮ ﻓﻠﻠﺘﺤﻘﻴﺮ * * ﻭ ﺍﻟﻀﺪ ﻭ ﺍﻹﻓﺮﺍﺩ ﻭ ﺍﻟﺘﻜﺜﻴﺮ .
Bayanin wannan ma'anar da lafazin ya 'dauka , ya zo 'karara
a wasu riwayoyi ; inda Annabi ya fayyace 'karara cewa koda
Bawan wula'kantacce ne mara daraja , to wajibine a yi masa
biyayya , Hadisin Al'imam Muslim na Ummul Hasin ya
fayyace haka a fili , Annabi yake cewa :
" ﺍﺳﻤﻌﻮﺍ ﻭ ﺃﻃﻴﻌﻮﺍ ﻭ ﺇﻥ ﺃﻣﺮ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻋﺒﺪ ﺣﺒﺸﻲ ﻣﺠﺪﻉ "
Anan Annabi ya bayyana cewa koda Bawan da shugabantu
akan mutane wula'kantacce ne ; ta yanda ya zama Ba'kin
Bawa ne , mai katsatstsen Hanci , wanda kuma duk Bawan
da yà zama a irin wannan sifa to babu shakka wula'kantacce
ne mara 'kima a wurin mutane . Amma duk da irin wannan
yanayi da ya kiwaye shugabancin Sa , Annabi bai saryar da
wajibcin biyayya gareshi ba .
8. Manzan Allah ya rattaba wasu irin yanayi _ marasa da'di _
akan shugabancin wani shugaba , ta hanyar ambaton cewa
koda shugabanci yana tattare da ababe kamar haka :
* Shugaban wula'kantaccen Bawa ne _ gashi kuma Bawa da
shi da dukiyar Sa Mallakan Ubangidansa ne _ amma kuma a
wayi gari a ce shine al'umma za su runsunamawa !!
* Koda Bawan ba Adali bane , kuma 'kwatan Mulkin ya yi da
'karfin Makami ; ya zama shugaba a bisa 'barauniyar hanya
wacce mutane suke inkarinta !!
* koda Bawan 'dorashi aka yi akan mutane , alhalin basa
'kaunassa a matsayin shugaba garesu .
Duk da irin wannan yanayi _abun 'kyama _ , da suka kewaye
wannan shughabanci , Manzan Allah bai saryar da wajibcin
biyayya ba ga shugaban , a'a sai ya wajabta biyayya gareshi
domin kiyaye maslaha mafi rinjaye na Addinin mutane da
rayuwarsu da zaman lafiyar su .
Wannan yana nuna shugaban da yake a sa'banin wa'dannan
miyagun sifofi shi ya fi cancanta da ayi masa biyayya Sama
da wanda yake akan irin wa'dannan miyagun sifofi . Kenan
anan Annabi ya fa'dakar da mutane ne akan mafi
wula'kantuwar al'amari zuwa ga mafi 'daukaka ( ﺍﻟﺘﻨﺒﻴﻪ ﺑﺎﻷﺩﻧﻰ
ﺇﻟﻰ ﺍﻷﻋﻠﻰ )
Kamar fa'din Allah ma'dauki :
" ﻓﻤﻦ ﻳﻌﻤﻞ ﻣﺜﻘﺎﻝ ﺫﺭﺓ ﺧﻴﺮﺍ ﻳﺮﻩ "
Wannan Ayar tana nuni akan cewa ; idan ya zama wanda ya
yi aiki daidai da qwayar zarra zai ga sakamakon sa , to
wanda ya yi manyan ayyuka shi ya fi cancanta da ya ga
sakamakon manyan ayyukansa .
9. Lafazin " ﻭ ﺇﻥ ﺗﺄﻣﺮ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻋﺒﺪ " , jumlace ta shara'di , wacce
take bu'katuwa zuwa ga sakamakon shara'din domin
ma'anarta ta cika , amma anan an share sakamakon
shara'din _bisa wajibi _ saboda an gabatar da lafazin da yake
nuni akan ma'anarsa , wannan lafazin shine " ﻭﺍﻟﺴﻤﻊ ﻭ ﺍﻟﻄﺎﻋﺔ
" .
Wato yanda jumlar take a asàli shine :
" ﻭﺍﻟﺴﻤﻊ ﻭ ﺍﻟﻄﺎﻋﺔ ، ﻭ ﺇﻥ ﺗﺄﻣﺮ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻋﺒﺪ ﻓﺎﺳﻤﻌﻮﺍ ﻭ ﺃﻃﻴﻌﻮﺍ "
To amma an wadatu da jumlar shara'din daga rashin ambaton
sakamakon shara'din saboda an gabatar da lafazin da yake
nuni akan ma'anarsa .
Zuwan sakamakon shara'di a irin wannan yanayi yana
wajabta rashin ambaton Sa da wadatuwa da jumlar shara'di ,
misali akan haka fa'din Allah ma'daukaki :
" ﻭ ﺧﺎﻓﻮﻥ ﺇﻥ ﻛﻨﺘﻢ ﻣﺆﻣﻨﻴﻦ "
Ta'kadirin jumlar shine :
" ﻭ ﺧﺎﻓﻮﻥ ﺇﻥ ﻛﻨﺘﻢ ﻣﺆﻣﻨﻴﻦ ﻓﺨﺎﻓﻮﻧﻲ "
Amma an goge sakamakon shara'din saboda an gabatar da
lafazin da yake nuni akan ma'anar Sa .
Ibnu Malik ya ce :
" ﻭ ﺍﻟﺸﺮﻁ ﻳﻐﻨﻲ ﻋﻦ ﺟﻮﺍﺏ ﻗﺪ ﻋﻠﻢ ** ﻭ ﺍﻟﻌﻜﺲ ﻳﺄﺗﻲ ان المعنى فهم
"
Saboda haka , ga'ba ta farko na hadisin :
" ﺃﻭﺻﻴﻜﻢ ﺑﺘﻘﻮﻯ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭ ﺟﻞ ، ﻭ ﺍﻟﺴﻤﻊ ﻭ ﺍﻟﻄﺎﻋﺔ "
Wannan ga'bar tana wajabta biyayya ga ko wane irin shugaba
ne a dun'kule ; hakan ya 'kunshi Adali da Azzalumi , 'Da ko
Bawa .
Ga'ba ta biyu kuma :
" ﻭ ﺇﻥ ﺗﺄﻣﺮ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻋﺒﺪ "
Tana 'kara 'karfafa wajibcin wannan biyayyar koda kuwa
shugabancin ya samu ne ta haramtacciyar hanya .
10 . Wannan umurni da Annabi ya yi na wajibcin biyayya ga
shuwagabanni a bisa yanayin da suke _ kamar yanda muka
fahimta daga lafuzzan hadisin _ , yana nuni akan haramcin
tawaye garesu komin munin halinsu , kuma a bisa ko wace
irin hanya suka haye madafan iko .
Kamar yanda yake sananne a ilimin usulul fiqh cewa; umurni
da wani abu hani ne gameda kishiyar wanabun ( ﺍﻷﻣﺮ ﺑﺎﻟﺸﺊ
ﻧﻬﻲ ﻋﻦ ﺿﺪﻩ ) .
Saboda haka , umurni da aka yi da biyayya ga shugaba yana
lazimta haramcin tawaye gareshi ;saboda tawayen yana
warware biyayya ta wajibine gareshi , saboda haka, tawayen
haramun ne .
Manzan Allah ya ha'da abubuwan guda biyu a wuri 'daya _
domin qarfafa wajibcin biyayya ga shugaba da haramcin
tawaye gareshi _ a cikin hadisin Ubadah bin Samit , Ubadah
ya ce :
" ﺑﺎﻳﻌﻨﺎ ( ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ) : ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺴﻤﻊ ﻭ ﺍﻟﻄﺎﻋﺔ ﻓﻲ ﻣﻨﺸﻄﻨﺎ ﻭ ﻣﻜﺮﻫﻨﺎ ﻭ
ﻋﺴﺮﻧﺎ ﻭ ﻳﺴﺮﻧﺎ ، ﻭ ﺃﺛﺮﺓ ﻋﻠﻴﻨﺎ ، ﻭ ﺃﻥ ﻻ ﻧﻨﺎﺯﻉ ﺍﻷﻣﺮ ﺃﻫﻠﻪ "...
( ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ : ٧٠٥٦ )
Anan da Annabi ya umurci Sahabbai da Biyayya ga
shuwagabanni _ wanda hakan yana lazimta rashin tawaye
garesu _ , Amma sai bai wadatu da hakan ba domin ya
'karfafa musu Wannan umurni, kuma ya fayyace musu 'karara
cewa baya halatta su sa'bawa Wannan umurni ta hanyar
tawaye ga shuwagabanni , sai ya 'kara musu da cewa :
" ﻻ ﺗﻨﺎﺯﻋﻮﺍ ﺍﻷﻣﺮ ﺃﻫﻠﻪ "
Ma'ana : kar Ku yi fito_na _fito da Shuwagabanni domin
'kwace mulkin su .
Ibnu Taimiyyah yana bayanin ma'anar Wannan lafazin sai
yake cewa :
" ﻭ ﻧﻬﻰ ( ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ) ﻋﻦ ﻣﻨﺎﺯﻋﺔ ﺍﻷﻣﺮ ﺃﻫﻠﻪ ، ﻭ ﺫﻟﻚ ﻧﻬﻲ ﻋﻦ
ﺍﻟﺨﺮﻭﺝ ﻋﻠﻴﻪ ، ﻷﻥ ﺃﻫﻠﻪ ﻫﻢ ﺃﻭﻟﻮ ﺍﻷﻣﺮ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺃﻣﺮ ﺑﻄﺎﻋﺘﻬﻢ ، ﻭﻫﻢ
ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻟﻬﻢ ﺳﻠﻄﺎﻥ ﻳﺄﻣﺮﻭﻥ ﺑﻪ ، ﻭﻟﻴﺲ ﺍﻟﻤﺮﺍﺩ ﻣﻦ ﻳﺴﺘﺤﻖ ﺃﻥ ﻳﻮﻟﻰ ﻭﻻ
ﺳﻠﻄﺎﻥ ﻟﻪ ، ﻭﻻ ﺍﻟﻤﺘﻮﻟﻲ ﺍﻟﻌﺎﺩﻝ ، ﻓﺈﻧﻪ ﻗﺪ ﺫﻛﺮ ﺃﻧﻬﻢ ﻳﺴﺘﺄﺛﺮﻭﻥ ، ﻓﺪﻝ
ﻋﻠﻰ ﺃﻧﻪ ﻧﻬﻰ ﻋﻦ ﻣﻨﺎﺯﻋﺔ ﻭﻟﻲ ﺍﻷﻣﺮ ﻭ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﺴﺘﺄﺛﺮﺍ "
( ﻣﻨﻬﺎﺝ ﺍﻟﺴﻨﺔ ، ٤ / ٨٨ )
Saboda haka ,wannan Hadisin yana nuni akan haramcin
tawaye ga Azzaluman Shuwagabanni , kuma akan haka
mazhabar Ahlussunnah ta gudana , wa'danda suka sa'bawa
musu akan haka sune 'kungiyoyi 'yan narko ( ﺍﻟﻮﻋﻴﺪﻳﺔ ) ;
KKhawarij da mu'tazila da Shi'a Rafidha .
Shaikhul Islam ya ce :
" ﺍﺳﺘﻘﺮ ﺃﻣﺮ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻋﻠﻰ ﺗﺮﻙ ﺍﻟﻘﺘﺎﻝ ﻓﻲ ﺍﻟﻔﺘﻨﺔ ﻟﻸﺣﺎﺩﻳﺚ
ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ ﺍﻟﺜﺎﺑﺘﺔ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭ ﺳﻠﻢ ، ﻭ ﺻﺎﺭﻭﺍ ﻳﺬﻛﺮﻭﻥ
ﻫﺬﺍ ﻓﻲ ﻋﻘﺎﺋﺪﻫﻢ ﻭ ﻳﺄﻣﺮﻭﻥ ﺑﺎ ﻟﺼﺒﺮ ﻋﻠﻰ ﺟﻮﺭ ﺍﻷﺋﻤﺔ ﻭ ﺗﺮﻙ ﻗﺘﺎﻟﻬﻢ ،
ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻗﺪ ﻗﺎﺗﻞ ﻓﻲ ﺍﻟﻔﺘﻨﺔ ﺧﻠﻖ ﻛﺜﻴﺮ ﻣﻦ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻭ ﺍﻟﺪﻳﻦ "
( ﻣﻨﻬﺎﺝ ﺍﻟﺴﻨﺔ ، ٤ / ٢٤١ )
11. Acikin wannan Hadisi akwai tabbatar da 'ka'idar " ﺍﺭﺗﻜﺎﺏ
ﺃﺧﻒ ﺍﻟﻀﺮﺭﻳﻦ " , ta yanda Annabi ya yi umurni akan ha'kuri da
wanzuwa 'kar'kashin jagorancin wanda bai cancanci
jagorancin ba ; sai aka ha'kura da aikata ''karamar 'barna ta
hanyar gujewa 'barnar da ta 'daranmata ; Wannan 'barnar
kuwa itace tawaye garesu .
12. Biyayya ga shuwagabanni al'amari ne mai muhimmanci a
shari'a , shi yasa Annabi ya yi nuni zuwa ga haka acikin
wannan Hadisin ta hanyar ambaton hakan a dunqule a farkon
saqonsa ; inda ya ce :
ﺃﻭﺻﻴﻜﻢ ﺑﺘﻘﻮﻯ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ "
Babu shakka biyayya ga shuwagabanni yana daga cikin
kiyaye dokokin Allah da Annabi ya yi umurni da shi , amma
kuma sai Annabi ya sake ambaton wajibcin biyayya ga
shuwagabannin 'karara a ke'be , domin ya bayyana girman
muhimmancin hakan a musulunci , kuma ya tabbatar da cewa
lallai hakan yana daga cikin kiyaye dokokin Allah .
Irin Wannan salo na zance shine Malaman Balaga suke ce
dashi :" ﺍﻹﻃﻨﺎﺏ " .
13. Kamar yanda tawaye ga Azzalumin Shugaba yake
haramun , to hakanan duk abunda zai iya zama kafa zuwa ga
Samar da wannan tawaye to shima haramun ne , kamar
yanda yake hakan 'ka'ida ce tabbatacciya acikin shari'a
.Malamai suna cewa :
" ﻛﻞ ﻣﺎ ﻳﻜﻮﻥ ﺫﺭﻳﻌﺔ ﺇﻟﻰ ﻣﺤﺮﻡ ﻓﻬﻮ ﻣﺤﺮﻡ "
Shaikhul Islam ya ce :
" ﻭﺍﻟﻔﻌﻞ ﺇﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﻳﻔﻀﻲ ﺇﻟﻰ ﻣﻔﺴﺪﺓ ﻭ ﻟﻴﺲ ﻓﻴﻪ ﻣصلحة ﺭﺍﺟﺤﺔ ﻳﻨﻬﻰ
ﻋﻨﻪ "
( ﻗﺎﻋﺪﺓ ﺟﻠﻴﻠﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﻮﺳﻞ ﻭ ﺍﻟﻮﺳﻴﻠﺔ ، ٤٦ )
Saboda haka , Samar da wasu Qungiyoyi masu fafutuka akan
hayewa madafan iko bayan samuwan shugaba ; wadanda
zasu zama 'Yan Hamayya ga shugaban , Wannan ya sa'bawa
tsari na musulunci .
Hakanan bayyana inkari ga shugaba abainar jama'a shima
haramun ne ; saboda kafa ce zuwa ga tawaye gareshi .
Shi yasa Annabi ya fito 'karara ya hana gyàrawa Shugaba
kuskuren Sa ta Wannan fuskar ; ya taqaita hanyar gyaran_
kawai _ ta hanyar ke'bewa da shugaban .
Ibnu Abi Asim ya ruwaito da tabbataccen isnadin Sa , daga
Sahabi Iyadh bin Ganam , ya ce Annabi ya ce :
" " ﻣﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﺃﻥ ﻳﻨﺼﺢ ﻟﺬﻱ ﺳﻠﻄﺎﻥ ﻓﻼ ﻳﺒﺪﻩ ﻋﻼﻧﻴﺔ ، ﻭﻟﻜﻦ ﻳﺄﺧﺬ ﺑﻴﺪﻩ
ﻓﻴﺨﻠﻮ ﺑﻪ ، ﻓﺈﻥ ﻗﺒﻞ ﻣﻨﻪ ﻓﺬﺍﻙ ، ﻭ ﺇﻻ ﻛﺎﻥ ﻗﺪ ﺃﺩﻯ ﺍﻟﺬﻱ ﻋﻠﻴﻪ "
( ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻻﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻋﺎﺻﻢ ، ٥٢١ )
Cewa da Annabi ya yi " ﻟﺬﻱ ﺳﻠﻄﺎﻥ " , yana nuni akan
haramcin
bayyana inkarin ga ko wane irin Shugabancin Mutumin yake
dashi ; ma'ana shugabanci ne baba ko 'karami , shugabanci
ne na daular musulunci , ko ko shugabancin ba na musulunci
bane .
Dalili akan haka shine : Annabi ya fa'di lafazin ne a sake "
ﻋﻠﻰ ﺍﻻﻃﻼﻕ " , saboda haka ko wane irin shugabanci zai shiga
cikin lafazin Hadisin , duk wanda ya fito ya ce : banda irin
shugabanci Kaza " , to za'a neme shi da ya Kawo dalilinsa na
dabaibaye lafazin Hadisin da wata sifa da Annabi bai bayyana
ta ba ga Wannan lafazin.
Acikin haka akwai martani ga masu cewa : wai shugabanni
bisa shugabanci na demokra'diyya ya halatta a caccake su a
bayyana inkari garesu abayyana inkari garesu a bainar jama'a
, suka ce wai Annabi shuwagabanni na musulunci yake nufi !!
babu shakka Wannan yi wa Maganar Annabi dabaibayi ne da
abunda bai mata dabaibayi da shi ba , yin hakan kuma ba
haqqi ne na wani mahaluqi ba , a'a haqqi ne na Annabi ,
tunda kuma shi bai yi ba , to babu wanda ya Isa ya yi hakan
kuma a kar'bi hakan daga gareshi !!
Hakanan cewa da Annabi ya yi :" ﺃﻥ ﻳﻨﺼﺢ " ,shima lafazi ne
sakakke ( ﻣﻄﻠﻖ ) , saboda haka nasihar ta shafi ko wane
kuskure ne yake aikatawa; kuskure ne da cutarwassa ya
ta'kaita akan Kansa shi ka'dai , ko ko a'a kuskuren
cutarwassa ya shafi al'ummar da yake jogaoranta , ko kuma
kuskure ne da yake aikatawa a bayyane , ko kuma kuskure na
'boye ; dukkan wa'dannan nau'uka na kurakurai na shugaba
zasu shiga cikin lafazin hadisin .
Saboda haka , duk wanda ya
ware wani nau'i na kuskure ya ce ya halatta
a bayyana inkari akan shugaba akan Sa , to za'a nemeshi da
ya Kawo dalilin ware Wannan Surar da halasci .
Sahababn Annabi sun gudana akan tabbatar da abunda
Wannan HADISI yake nunawa ; na ke'bewa da shugaba yayin
nasiha gareshi .
Wasu mutane sun sami Usama bin zaid, sai
suka neme shi da ya yiwa Khalifah nasiha akan sha'anin
jagorancinsa , sai Usama ya ce da su :
" ﻗﺪ ﻛﻠﻤﺘﻪ ﻣﺎ ﺩﻭﻥ ﺃﻥ ﺃﻓﺘﺢ ﺑﺎﺑﺎ ﺃﻛﻮﻥ ﺃﻭﻝ ﻣﻦ ﻳﻔﺘﺤﻪ "
( ﺑﺨﺎﺭﻱ : ٧٠٩٨ )
Anan sai Usama ya fa'da musu cewa ; ya yi masa
nasiha akan matsalar , Amma a 'boye ya yi masanasihar ; bai
bayyana nasihar a bainar jama'à ba domin kar ya zama yazo
da wata sabuwar Bid'a ta bayyana inkari ga shugaba a bainar
jama'a ,wanda babu wanda ya gabaceshi akan haka . Saboda
haka , haramun ne bayyana inkari ga shugaba .
Ibnu Hajar ya ce gameda wannan Hadisi :
" ﻗﺎﻝ المهلب : ﻗﺎﻝ ﺃﺳﺎﻣﺔ : " ﻗﺪ ﻛﻠﻤﺘﻪ ﺳﺮﺍ ﺩﻭﻥ ﺃﻥ ﺃﻓﺘﺢ ﺑﺎﺑﺎ ، ﺃﻱ
ﺑﺎﺏ
ﺍﻟﭑﻧﻜﺎﺭ ﻋﻠﻰ ﺍﻷﺋﻤﺔ ﻋﻼﻧﻴﺔ ﺧﺸﻴﺔ ﺃﻥ ﺗﻔﺘﺮﻕ ﺍﻟﻜﻠﻤﺔ "
ﻭ ﻗﺎﻝ ﻋﻴﺎﺽ :
" ﻣﺮﺍﺩ ﺃﺳﺎﻣﺔ ﺃﻧﻪ ﻻ ﻳﻔﺘﺢ ﺑﺎﺏ ﺍﻟﻤﺠﺎﻫﺮﺓ ﺑﺎ ﻟﻨﻜﻴﺮ ﻋﻠﻰ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻟﻤﺎ
ﻳﺨﺸﻰ ﻣﻦ ﻋﺎﻗﺒﺔ ﺫﻟﻚ ﺑﻞ ﻳﺘﻠﻄﻒ ﺑﻪ ﻭ ﻳﻨﺼﺤﻪ ﺳﺮﺍ ﻓﺬﻟﻚ ﺃﺟﺪﺭ ﺑﺎ
ﻟﻘﺒﻮﻝ "
( ﻓﺘﺢ ﺍﻟﺒﺎﺭﻱ ، ١٣ /٤٤ )
maganar kuma cewa ai wani Malami , ko wani Sahabi ya yi ,
Wannan duk ba Hujja bane , Hujja itace maganar Allah ko ta
Annabi , amma wani mutum _ko wanene _ aikinsa ba Hujja
bane a addini , balle kuma idan Aikin nasa ma ya ci karo da
maganar Allah ko ta Annabi !!.
Abunda za'a iya cewa a Wannan yanayi shine : a bawa
Wannan malamin uzuri da cewa ; ya yi ri'ko ne da dalilai
gamammu da suke umurni da inkari ga wanda ya sa'bawa
shari'a kai tsaye , sai malamin ya gafala da dalilin da ya
ke'be shugaba da rashin bayyana hakan gareshi a bainar
jama'a .
ko kuma a ce malamin yana ganin maslahar bayyana inkarin
a wannan yanayi yafi rinjaye
Sama da rashin haka , ko kuma ma zata yiwu in ba a wannan
yanayin ba gusar da ''barnar ba zata yiwu ba . saboda haka
sai malamin ya ribaci Wannan yanayin domin ya cimma
maslaha mafi rinjaye . Sanannen
abune a shari'a cewa dukkan
abunda aka haramtashi Saboda zamantowarsa kafa ne zuwa
ga abunda yake haramun ,to ana halasta shi saboda
wata maslaha mafi rinjaye .
Shaikhul Islam ya ce:
" ﺍﻟﻨﻬﻲ ﺇﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﻟﺴﺪ ﺫﺭﻳﻌﺔ ﺃﺑﻴﺢ ﻟﻤﺼﻠﺤﺔ ﺭﺍﺟﺤﺔ "
( ﻗﺎﻋﺪﺓ ﺟﻠﻴﻠﺔ ، ٤٦ )
Saboda
haka , Wannan yana daga abunda za'a iya cewa
gameda
irin Wannan yanayi , amma bai yiwuwa a yi watsi da Hadisi
_wai_Saboda ya
sa'bawa aikin wani mutum , ko kuma a ce za'a yi jam'i
tsakanin Hadisin Annabi da aikin wani malami da ya sa'bawa hadisi , wannan duka kuskure ne ; ba'a yin jam'i tsakanin abunda yake Hujja da wanda ba Hujja ba ; ana jam'i net sakanin dalili da dalili . Al'imam Ashshaukany ya ce :
" ﺇﻧﻤﺎ ﻳﻘﺘﺪﻱ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﺄﻫﻞ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﺨﻴﺮ ، ﻓﺈﻥ ﺟﺎﺅﻭﺑﻤﺎ ﻳﺨﺎﻟﻒ
ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭ ﺍﻟﺴﻨﺔ ، ﻓﺎﻟﻘﺪﻭﺓ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﻣﻊ ﺇﺣﺴﺎﻥ ﺍﻟﻈﻦ ﺑﻬﻢ ، ﻭ
ﺣﻤﻠﻬﻢ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﺎﻣﻞ ﺣﺴﻨﺔ ﻣﻘﺒﻮﻟﺔ "
( ﺍﻟﻔﺘﺢ ﺍﻟﺮﺑﺎﻧﻲ ، ٥٥٩٣ )