Subscribe Our Channel


TSOKACI AKAN MUHADARAR MALAM MUSA ASADUS SUNNAH (1)

Hakika Allah ya jarabci da'awar Sunnah anan Nigeria da matsaloli masu yawa , daga ciki akwai rigingimu da suke faruwa tsakanin masu dangantuwa zuwa ga ita da'awar ta Sunnah ; an samu wasu matasa masu kishin Sunnah da manhajin Magabata wa'danda su ka kafu akan ya'ki da ababen da suke ganin wasu masu da'awar sun shigo da su cikin Sunnar alhali kuma ababen basa cikin Sunnah , basu tsaya akan haka ba , a'a sun tsallaka har zuwa ga yin hukunci akan wasu ayyanannu cikin masu da'awa na bidi'antarwa da tsoratarwa akansu , wanda anan zaka samu suna fa'dawa cikin kuskure a wannan mataki ; wani lokaci zaka samu laifin da mai da'awar ya yi bai kai matakin bidi'antarwa ba , wani lokaci kuma zaka samu kwata_kwata ma ba laifi ya yi ba , a'a kawai sun bidi'antar da shi ne kawai bisa tsuran son zuciya , wani lokaci kuma zaka samu sune basu fahimci mas'alar da suke sa'bani akanta ba ; don haka sai su ka yi azar'ba'bi wurin yin hukunci akan wanda ya sa'ba musu , wani lokaci kuma zaka samu shi Malamin laifin da ya yi laifi ne mai girma , wanda ya cancanci fitarwa daga Sunnah ga wanda ya aikata shi , to amma sai dai sharu'd'dan aiwatar da hukuncin ba su cikaba , ko kuma akwai ababen da za su hana tabbatuwar hukuncin akansa , amma sai wa'dannan matasa Su yi gaggawan yanke hukuncin , ko dai saboda son zuciya , ko kuma saboda kishin Sunnah . 

Wani lokaci kuma Su Matasan suna amfanine da wasu qa'idoji wa'danda suke haifar da rabon bidi'antarwa ga jama'a ba tare da qaidi ba ; wa'dannan qa'idojin wani lokaci zaka samesu tabbatattu a shari'a amma suna da qaidi , wani lokaci kuma zaka samu qa'idoji marasa tushe a Shari'a .

Wani lokaci kuma akan samu dacewa akan wanda Su ka yi hukuncin bidi'antarwa akansa , musamman irin malaman da asali su ba Ahlussunah bane , amma yanayin yanda ake da'awar Sunnah a Nigeria ya mayar da su Ahlussunah bisa qarya .


Babu shakka akwai bu'katar gyara acikin wannan tafiyar ; wajibine a yaqi abunda take 'dauke da shi na wuce iyaka , abayyana sa'bawarsa ga Shari'a bisa dalilai na ilimi , Kuma a qarfafi abunda suke 'dauke da shi na gaskiya , a bayyanashi a ilmance , a kira mutane zuwa gareshi , a yi martanin qaryar da take kishiyantarsa , kuma a yi husuma da masu inkarin gaskiyar .


A 'dayan bangaren kuma , akwai masu kishiyantar wa'dancan matasa , wa'danda suke qalubalantarsu a kan tafiyarsu ta yin hukunci akan wasu masu da'awa , da Kuma husuma da Su akan wasu al'amura da suke sa'bani akan bidi'ancinsu . Anan zaka samu masu husumar dasu suna sakaci akan wasu tabbatattun al'amura acikin Shari'a ; suna qaryata gaskiya da qaryar da wa'dancan suke 'dauke da Su , suna wuce iyaka wurin bada kariya akan malaman da wa'dancan suke yin hukunci akansu ; suna bada kariya akan wa'danda suke sanannu ne wurin yaqi da Sunnah , da mummunan qiyayya ga ma'abotanta , babban matsalar da wannan bangare yake 'dauke da Shi shine : caku'duwarsa da gur'batattu wa'danda ba ma'abota Sunnah ba , kawai domin a kishiyanci wancan 'bangare na farko .


Abunda yake gaskiya shine : tabbatar da gaskiyar da kowane bangare yake 'dauke da ita , da inkarin qaryar da kowanne yake 'dauke da ita , da ji'bintan kowa da yabonsa gwargwadon ji'bintarsa ga Sunnah , da nisantar kowa gwargwadon nisansa ga Sunnah , da taimakon duk wanda yake kan gaskiya bisa gaskiyar da yake tare da ita , da inkari akan duk wanda yake tare da qarya aduk lokacin da ya rungumeta .


 Shaikhul Islam yana cewa :


والله قد أمرنا ألا نقول إلا الحق ، وألا نقول عليه إلا بعلم ، وأمرنا بالعدل والقسط ، فلا يجوز لنا إذا قال يهودي أو نصراني ، فضلا عن الرافضي قولا فيه حق أن نتركه أو نرده كله ، بل لا نرد إلا ما فيه من الباطل ، دون ما فيه من الحق " 

( منهاج السنة ، ٢/٣٤٢)


Hakanan yana cewa :


والواجب على كل مسلم يشهد ألا إله إلا الله وأن محمدا رسول الله أن يكون أصل قصده توحيد الله بعبادته وحده لا شريك له وطاعة رسوله ، يدور على ذلك ويتبعه أين وجده ، ويعلم أن أفضل الخلق بعد الأنبياء هم الصحابة ، فلا ينتصر لشخص انتصارا مطلقا عاما إلا لرسول الله صلى الله عليه وسلم ، ولا لطائفة انتصارا مطلقا عاما إلا للصحابة رضي الله عنهم أجمعين ، فإن الهدى يدور مع الرسول حيث دار ، ويدور مع أصحابه دون أصحاب غيره حيث داروا "


( منهاج السنة ، ٣/٦٦)


________________________________


A makon da ya gabatane Malam Musa Asadussunnah ya gabatar da muhadara domin qalubalantar wa'dancan matasa masu wuce iyaka awurin hukunci akan wasu Malamai , Malam Musa ya fa'di wasu ababe wa'danda su ka sa'bawa Shari'a , kuma da shi da Almajirinsa mai suna Shehu Liman sun auka cikin abunda suke jifan abokan husumarsu da shi na wuce iyaka wurin yin hukunci .

Mafi yawan abunda Malam Musa ya ambata acikin muhadarar babu tahqiqi aciki ; Idan mas'ala ce ta ilimi , to zaka ga kwata_kwata ba iya tahqiqinta , Idan Kuma naqali yazo yi daga wani ; to anan ma babu tahqiqi wurin ajiye naqalin a mahallinsa , hakanan idan ya zo yin hukunci to nan ma babu tahqiqi ...


Zamu kawo wani sashe na bayanansa sai mu yi taqaitaccen tsokaci akansu :


1. Malam Musa Asadussunnah ya yi wa Shaikh Rabi'u qarya , kuma ya yi wa qasar Amurka qarya ; ya ce wai Shaikh Rabi'u ne ya yi wa Amurka Fatawa da ta shiga qasar Iraqi ta rusata ta miqata a hannun 'Yan Shi'a !


Ka ga wannan maganar ba gaskiya bace , maganar bata da amsar da ta wuce ace : qaryane " 


A qa'ida ta shari'a ba'a yin qarya wurin mutum ya kare abunda yake ganin shine gaskiya , ita gaskiya bata buqatar qarya wurin kareta . 


Ga sautin Malam Musa akan haka : 


https://a.top4top.io/m_2477azid61.mp3


Acikin wannan sautin bayan Malam Musa ya yi wa Shaikh Rabi'u sharri , sai kuma ya biyunta da inkarin bidi'ancin tawaye ga Shuwagabanni Musulmi !


Duk wanda yake Ahlussunah ne to ya san da cewa tawaye ga Shuwagabanni Musulmi haramunne , kuma ba Manhaji bane na Ahlussunah _ Koda kuwa an samu wasu daga cikin magabata sun aikata hakan bisa kuskure _ , kuma wannan al'amarine mutawaturi acikin littattafan Aqida na Ahlussunati Wal Jama'ah .


Shaikhul Islam yana cewa :


" استقر أمر أهل السنة على ترك القتال في الفتنة للأحاديث الصحيحة الثابتة عن النبي صلى الله عليه وسلم ، وصاروا يذكرون هذا في عقائدهم ، ويأمرون بالصبر على جور الأئمة وترك قتالهم وإن قاتل في الفتنة خلق كثير من أهل العلم والدين " 


(منهاج السنة ٢/٢٤١)


Wa'danda aka sani da halatta tawaye ga Shuwagabanni Musulmi sune qungiyoyi 'yan narko ( Khawarijawa da Mu'utazilawa da wa'danda suke kan tafarkinsu ) .


Shaikhul Islam yana cewa :


" كان من أصول السنة والجماعة لزوم الجماعة ، وترك قتال الأئمة ، وترك القتال في الفتنة . وأما أهل الأهواء كالمعتزلة فيرون القتال للأئمة من أصول دينهم " 


( الاستقامة ، ٣٦٣)


2. Daga cikin kwamacalan da Malam Musa ya yi wa Shari'a shine : tattauna mas'ala ta ilimi ba bisa ilimi ba . Haramun ne mutum ya kutsa kansa cikin mas'alar ilimi kuma ya ringa magana na jahilci ko shirme acikinta . Malam Musa ya kawo hadisin Iyad bin Ganm , Hadisin da Ananbi yake hani acikinsa akan bayyana nasiha ga Shuwagabanni ; maimakon Malam Musa ya tattauna hadisin a ilmance , misali ya yi magana akan ingancinsa ko rashin ingancinsa , ko ya yi magana akan manuniyarsa , ko kuma idan akwai wasu hadisan da suke karo da Shi a zahiri sai ya kawo so ya naqashasu a ilmance , a'a kawai sai Malam Musa ya 'buge da cewa : 


" Ai masu kawo wannan hadisinma ko da yawansu ko gidan Gwamnati ba su ta'ba zuwa ba , Ni kuma tun ina Yaro ake gayyatana gidan Gwamnati , ai masu kawo hadisin basu san hanyar da ake bi ba wurin zuwa gidan Gwamnati ... Daga nan kuma sai ya 'buge da kawo labarai ...


Ga sautinsa anan :


https://g.top4top.io/m_2477ci3ju1.mp3


3. Malam Musa a maimakon ya yi magana na ilimi akan abunda yake jayayya akansa , a'a kawai sai ya 'buge da yin tsageranci ga Shaikh Rabi'u ; yana cewa wai zai buga shi da qasa ! 


Ga sautinsa anan : 


https://e.top4top.io/m_2477xsbzy1.mp3


4. Almajirin Malam Musa , wato Shehu Liman shima ya wuce iyaka akan wa'danda shehinsa yake husuma da Su , ya bidi'antar da su ; ta yanda ya dangantasu ga qungiyar bidi'a ta Murji'a .


Babu shakka wannan hukunci da Shehu Liman ya yi hukunci ne na zalunci da biyewa son zuciya , kuma ya afka kansa cikin abunda yake zargin abokan husumarsa da shi ( duk da cewa su sun fi shi shubuha mai qarfi akan hukuncin da khawarijanci da suka yi akan wasu Malamai da ake husuma da su akan hakan ) 


Shehu Liman bai tsaya nan ba , a'a ya qara da zabga musu qarya ; ya ce wai abokan husumarsa tuntuni sun kafirta Malam Ahmad Algarkawy da ke Kaduna .


Wannan magana ta Shehu Liman ba gaskiya bane , abunda aka sani shine : wasu daga cikin wa'dannan Matasan sun bidi'antar da Malam Algarkawy , amma ba'a samu wa'danda su ka kafirta shi ba . 


Ga sautin Shehu Liman a nan :


https://j.top4top.io/m_247830qzt1.mp3


Rubutunmu na gaba zamu cigaba da yin tsokaci akan sauran ga'bo'bin muhadarar

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter