SHIN AKWAI SALAFIYYA SHAIDANIYA?
Asali in an ce: "Salafiyyah" suna ne madanganci da ake siffanta hanyar Salaf da shi, musamman hanyarsu a Mas'alolin Aqeeda. Wato "طريقة السلف" sai a danganta hanyar zuwa ga Salaf a siffanta ta da su a ce: "الطريقة السلفية". Don haka in an ce: "Salafiyyah", kamar an ce: "الطريقة السلفية" ko "العقيدة السلفية" ne.
In an ce: Salaf kuwa duk Musulmai sun san cewa; "Salafus Salihu" (السلف الصالح) ake nufi, wato magabata na kwarai.
Wadannan Magabata kuwa su ne karni ukun farko wadanda Annabi (saw) ya ambace su a cikin Hadisin:
"خير الناس قرني، ثم الذين يلونهم ثم الذين يلونهم"
Ma'ana; Mafi alherin karni (jeeli) shi ne karnin Annabi (saw), wato Sahabbai kenan, sai wadanda suke biye da su, wato Tabi'ai, sai wadanda suke biye da su, wato Tabi'ut Tabi'ina.
Don haka wadannan karni guda uku su ne:
1- Jeelin Sahabbai.
2- Jeelin Tabi'ai.
3- Jeelin Tabi'ut Tabi'ina.
Su ake kira ma'abota karnoni uku masu falala.
Allah da Manzonsa sun yi umurni da bin Sahabbai da Mabiyansu da kyautatawa. Allah ya ce:
{وَالسَّابِقُونَ الْأَوَّلُونَ مِنَ الْمُهَاجِرِينَ وَالْأَنْصَارِ وَالَّذِينَ اتَّبَعُوهُمْ بِإِحْسَانٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ وَأَعَدَّ لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي تَحْتَهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ } [التوبة: 100]
A cikin wannar Ayar akwai yabo da yarda ga Sahabbai da wadanda suka bi su da kyautatawa, don haka wannan ya kunshi umurni da bin hanyarsu.
Shi ya sa Allah ya yi alkawarin narkon azaba ga wanda ya saba hanyarsu, inda ya ce:
{وَمَنْ يُشَاقِقِ الرَّسُولَ مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُ الْهُدَى وَيَتَّبِعْ غَيْرَ سَبِيلِ الْمُؤْمِنِينَ نُوَلِّهِ مَا تَوَلَّى وَنُصْلِهِ جَهَنَّمَ وَسَاءَتْ مَصِيرًا } [النساء: 115]
Kowa ya san Sahabbai su ne Muminan farko.
Haka ya zo a shahararren Hadisin nan na rabuwar al'umma kashi 73, Annabi (saw) ya siffanta kungiya mai tsira daga wuta da cewa; su ne wadanda suke kan abin da yake kai shi da Sahabbansa.
ما أنا عليه وأصحابي
Wannan ya kunshi wajabcin bin hanyarsu da haramcin saba mata.
Saboda haka, abin da wadannan magabata suka hadu a kai, suke tafiya a kansa a matsayin hanyarsu shi ne abin da ya wajaba kowa ya bi, kuma ya haramta kowa ya saba masa.
Abin da suka hadu a kai kuwa shi ne abin da ake kira "Usulud Deen", wato manyan Mas'alolin Addini; Mas'alolin Aqida da manyan Mas'alolin Fiqhu. Kamar babin Imani da Allah da tabbatar da Siffofinsa, da Mas'alar Alkur'ani cewa; Maganar Allah ne ba halittacce ba, da Babin Imani da Kaddara da Babin Mas'alolin Imani, da sauran babukan da Salaf suka yi Ijma'i a kansu.
Da kuma Babin Kafa Hujja da Alkur'ani ba tare da Tawili ko ikirarin "Majaaz" a cikinsa ba, da karban dukkan Hadisan da suka tabbata daga Annabi (saw) da kafa hujja da su, ba tare da da'awar banbance "Qat'iy" ko "Zanniy" daga cikinsu ba, da sauran manyan Mas'aloli da ake ambata a cikin littatafan Aqeedar Salaf, wadanda babu wanda ya saba a kansu sai 'Yan Bidi'a da Mabiya son rai.
Saboda haka irin wadannan su ake ambata a matsayin hanyar Salaf, kuma shi ne ma'anar Salafiyya a bisa hakika.
Amma Mas'alolin Fiqhu kuwa, galibi Mas'aloli ne da Ijihadi zai iya shiga cikinsu, shi ya sa babu wanda aka wajabta binsa a cikin Malaman Fiqhu, sai wanda yake da Nassi ko Ijma'i. Iyakaci abin da aka sani shi ne; duk Mas'alar da aka yi sabani a kanta zuwa kauli biyu to bai halasta wani ya kirkiri sabon kauli na uku ba. Amma babu wanda ya isa ya wajabta ma wani bin Mazhaba guda daya, bin Malikiyya ko Shafi'iyya ko waninsu.
Kuma ko a Fiqhun ba a maganar Salafiyya a cikinsa, saboda mafi yawan wadannan Littatafan Mazhabobi da muke karantawa a yanzu da sunan Littatafan Mazhaba, ba Malik ko Shafi'iy ne suka rubuta su ba, galibi 'yan baya ne can suka yi "Takhriji" bisa "Usul" da ka'idojin wadancan Malaman farkon. Haka kuma galibi "Usul" da ka'idojin ma ba nassanta su Malaman farkon suka yi ba, Ijtihadi aka yi aka fitar da su, aka jingina musu su.
Don haka ta yaya za a ce: Littatafan Fiqhun Mazhabobin nan guda hudu kawai su ne Fiqhun Salaf?!
Fiqhun Salaf shi ne abubuwan da aka ruwaito daga Sahabbai da Tabi'ai da Tabi'ut Tabi'eena, su kuwa suna rubuce cikin littatafan Athaar; "Muwadda'a", "Musannafu Ibni Abi Shaibah", "Musannafu Abdirrazzaq", "Sunanu Darimiy" "Sunanu Sa'eed bn Mansuur" da sauran littatafan da aka tara riwayoyin Sahabbai da Tabi'ai a kan Mas'alolin Fiqhu.
Kuma hatta a wannan zamani Shaikh Muh'd Nasirud Deen Al-Albaniy abin da ya yi kenan, wato kira zuwa ga komawa ga Fiqhun Salaf a Mas'alolin Fiqhu, a bar makalkale ma Ijtihadodin Malaman Fiqhun da galibinsu zamaninsu ya yi matukar nisa da Salaf.
Misali ka dauki babban littafi a Malikiyya da sharhohinsa, wato "Mukhtsarul Khaleel", tsakaninsa da zamanin Salaf shekara dari nawa?
Saboda haka ba komai ne Mazhaba ba face bin Ijtihadin Malaman Mazhabar Malikiyya da suka yi Ijtihadi da Takhriji bisa ka'idoji da Usul na Imam Malik.
Don haka ta yaya za a ce: wannan shi ne Fiqhun Salafiyya, alhali an yi watsi da abin da aka ruwaito daga Sahabbai da Tabi'ai da Tabi'ut tabi'eena?!
Saboda haka asali hanyar Salaf a Aqeeda da Manyan Mas'alolin Addini ne ake kira da "Salafiyyah" ba Mas'alolin Fiqhu ba. Wannan ya sa manazarta ba sa ambaton Salafiyyah sai in ana magana a kan Aqeeda da riko da Nassin Alkur'ani ba tare da tawili ba, da riko da dukkan Hadisan Annabi (saw) tabbatattu ba tare da jefar da wasu bisa da'awar Hadisi kaza zato ne ba "qat'iy" ba. Saboda ba a san haka daga Salaf ba. Wannan shi ne abin da aka sani ya banbanta tsakanin Salafiyyah da Mazhabar "Mutakallimina"; Asha'ira da Maturidiyya da kuma hanyar sauran 'Yan Bidi'a da suka saba a Aqeedar Salaf, ba magana a kan Mas'alolin Fiqhu da Mazhabobinsu ba.
Manyan Malaman Fiqhu nawa, wadanda duka manyan 'Yan Bidi'a ne, imma "Mutakallimuna" ko Sufaye?!
Ta yaya za a danganta wadannan ga Salaf?!
Sai kuma wani abu da ya kamata a fahimta a nan, akwai banbanci tsakanin "Salafiyyah" a matsayin hanyar Salaf, da kuma "Salafiyyun" masu dangantuwa zuwa ga hanyar Salaf din. Lallai za a iya samun rarrabuwa tsakanin masu dangantuwa ga hanyar Salaf, kowa yana da'awar bin Salafiyya, har ma wani bangare yana koran sauran bangarorin daga cikin Salafiyyar, duka wannan ba abu ne mai tasiri ba, saboda matukar mutum yana kan Bin Alkur'ani da Sunna ba tare da Tawili ko jefar da Hadisai bisa da'awar Hadisi "Ahaad" zato ba "qat'iy" ba, da bin Manhajinsu a fahimtar Nassi, kuma yana kan Ijma'in Salaf a Manyan Mas'alolin Aqeeda (Usulus Sunna), babu wanda ya isa ya fitar da shi daga Salafiyyah, sai dai a kore shi daga kungiyar wasu 'yan Salafiyyar.
Kuma wannan sabani ne da bai kai a siffanta kungiyar ko jama'ar da suke kiran kansu da Salafiyyar da Shedanci ba, saboda siffanta hanya da Shedanci yana hukunta raba ta da hanyar Sunnar Manzon Allah (saw) gaba daya, wannan kuwa ba abu ne mai sauki ba, a siffanta wanda yake dangantuwa ga Salafiyyah ba tare da bayyananniyar Bidi'a ba da shedanci.
A takaice, ta kowace fiska siffanta Salafiyyah da Shaidanci, a kira ta da "Salafiyya Shaidaniya" babban kuskure ne, saboda kowa ya san hanyar Salafus Salihu ake nufi, hanyarsu kuwa hanya ce da Allah da Manzonsa suka yabe ta, suka wajabta binta.
Don haka ta yaya za a kira Salafiyyah da Shaidaniya?!
Don haka yana da kyau mutane suna lura, suna tantance lafuza da "Musdalahaat" da suke amfani da su, da hukunci da suke yankewa a kansu.