Ramalana //3
(1) Watan Ramadana wata ne na ayyukan al-khairi, wata ne da ake so bawa ya ninninka ayyukansa na Al-khairi, domin Allah yana Rubunya ladan ayyukan bayi.
(2) Yana daga cikin ayyukan Al-khairi shine Ciyarwa don Allah, domin Allah yana ninninkawa ga masu ciyarwa don Allah da lada 70 yakan karawa wanda yaso, matukar bai 6ata sadakar ba da cutarwa da gori.
(3) Hakika Allah yakan gadarwa masu ciyarwa don shi wani katafaren gida a gidan Al-Janna don haka yaku bayin Allah ku tuna ku dage da ayyukan Al-khairi.
(4) Yaku yan uwa masu al-khairi ku ciyar da abu mai kyau daga abinda Allah ya azurtaku dashi koda da tsagen dabino ne, ku ciyar da abu mai kyau daga abunda kukafi so, ko kun dace da aikin Al-khairi, lallai Allah yana sane da duk abunda kuke ciyarwa donshi, daga Al-khairanku.
(5) Yaku yan uwa Lallai wannan watan watane na ciyarwa don haka ku ciyar da abunda Allah ya azurtaku dashi. Yana daga cikin fa'idar shar'anta azumin watan Ramalana shine don masu hannu da shuni su shaidi abunda talakawa keji na yunwa, da halin rayuwa.
Allah ka datar damu da ayyukan Al-khairi
#IbrahimAbuammar
#Haskensunnah,Blogspot,com
05/09/1439
Ramalana //3
Subscribe Our Channel