Subscribe Our Channel

Ramalana //1
(1) Yana daga cikin Fa'idojin Azumin Watan Ramalana, shine bawa ya kara kusantar Ubangijinsa, bayan yayi hutun watanni 11, domin ya tabbata a hadisi da atharai irin yadda Annabi SAW yake kara zage damtse wurin ibada, duk da kasancewarsa mai yawan ibada, haka sahabbansa da sauran magabata na kwarai.
(2) Sannan bawa zai samu yafiya da Kuma Rahamar Ubangijinsa , Shiyasa a hadisin da Al-Imamul Bukhari da Muslum suka ruwaito, manzon Allah SWA yake cewa: Allah yana kankare zunubai Tsakanin ramadana zuwa ramadan, yayin da mutum yayi dakon tarin zunubansa, shiyasa a wani hadisin da Bukhari da Muslum suka ruwaito, Annabi da mala'ika Jibrilu sukayi mummunar addu'a ga wanda bai ribaci wannan wata ba, domin hadisin bukhari da Muslum daga Annabi yana cewa: Idan Ramadana ya shigo, ana bude kofofin Al-Janna (Kofofin rahma kenan), sannan ana kulle kofofin Wuta (kofofin sharri), sannan za'a daure shaidanu (Wataun a saka musu kasalar takura bayin Allah lokacin ramadana).
(3) Don Haka yakai dan uwa, kada ka zakkewa sharri, domin Wannan watan kirkine na yayan kirki, dage aikata kirki, sai kaga kirki a cikin account dinka na kirki.
Haskensunnah,blogspot,com
#IbrahimAbuammar
02/09/1439H - 2018M
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter