Ramadhaniyyat@1439H [9]
Son Zuciya
1. Allah Ta’ala yana cewa:
(To idan ba su amsa maka ba, to ka sani ba abin da suke bi sai soye-soyen zukatansu kawai, babu kuwa wanda ya fi bacewa kamar wanda ya bi son zuciyarsa kawai, ba tare da wata shiriya daga Allah ba. Hakika Allah ba ya shiryar da mutane azzalumai). [Al-Kasas, aya ta 50].
2. Son zuciya cuta ce mai saurin hallakar da wanda ta kama, domin tana da wuyar sha’ani.
3. Duk wanda Allah ya tsare shi daga bin son zuciyarsa to wannan shi ne wanda zai iya bin karantarwar wahayi (Alkur’ani da Sunna) cikin sauki ba tare da ya sha wata wahala ba.
4. Wanda kuwa ya kamu da cutar bin son zuciya to wannan ya yi hannun riga da shiriyar wahayi kwatakwata. Domin son zuciya kishiya yake ga bin shiriyar Allah, duk wanda ya zabi dayansu to dole sai ya rabu da dayan.
5. Bin Son zuciya shi ne ramin bata mafi zurfi. Duk wata fandara a duniya to hade take da bin son zuciya.
6. Hanyoyin dai biyu ne kacal babu ta ukunsu; ko dai mutum ya bi tsantsar gaskiya ya mika wuya ya yi imani da wahayi (Alkur’ani da Sunna); ko kuma ya yi jayayya ya ki gaskiya ya bi son zuciyarsa ya karyata wahayi.
7. Duk wanda ya zabi ya bi son zuciyarsa to bai zalunci kowa ba kansa kawai ya zalunta, kuma ya sani cewa ya haramta wa kansa samun shiriyar Allah kenan har sai ranar da ya tsabtace zuciyarsa ya nufi Allah da ayyukansa. Allah ya sa mu dace. Amin.