Ramadhaniyyat@1439H [7]
Baragurbin Dalibi
1.Allah Ta'ala yana cewa:
(Daga cikinsu kuma akwai wadanda suke aibata ka game da rabon sadaka; idan an ba su wani abu daga cikinta to sai su gamsu, idan kuwa ba a ba su daga cikinta ba sai ka gan su suna fushi). At-Tauba, aya ta 58.
2.Wajibi ne a kan malamai su himmatu wajen gina al'umma mai tarbiyya mai ganin girman shugabanninta da malamanta da tsare musu hakkokinsu.
3.Duk al'ummar da matasanta suka rasa kyakkyawar tarbiyya, to babu shakka wannan al'umma ce da ta dauko hanyar rushewa da lalacewa.
4.Babu wata al'umma da gininta zai kai ga cika matukar dai dabi'un matasanta dabi'u ne marasa kyau da rashin ganin kan kowa da gashi.
5.Babban abin takaicini a wayi gari alakar dalibi da malamansa ta tashi daga alaka ta ilimi da karantarwa ta koma alaka ta duniya zalla; kamar alakar mai saye da mai sayarwa ko ma'aikaci da wanda ya dauke shi aiki.
6.Yau an wayi gari idan dalibi yana tare da malaminsa tsawon lokaci yana karuwa da iliminsa da nasiharsa da tarbiyyarsa, to abu ne mai sauki gobe ka ji shi yana bata malamin nasa da hujjar ba ya taimaka masa da komai yana bautar da shi ne kawai.
7.Wannan shi yake nuna maka cewa, irin wannan dalibi ko da ma can bai kusanci malaminsa don karuwa da iliminsa ba, a'a ya kusance shi ne don ya rika samun wani abu na duniya daga wajensa. Idan an ba shi a zauna da shi lafiya, idan ba a ba shi ba ya yi fushi ya dauki ko wane irin mataki na cin mutunci da tozarta wanda ya koyar da shi addininsa.
8.Malaminka idan bai cancanci hidimarka kyauta ba, to babu wanda ya cancance ta.
9.Mai kama da wannan baragurbin dalibi kuwa a wajen mummunar sakayya shi ne dan da zai bijire wa mahaifinsa da hujjar cewa bai kula da shi ba lokacin da yake dan karami; bai biya masa kudin makaranta ba, bai dinka masa sababbin kaya ba…. da dai sauransu. Watau dai ya takaita alakarsa ta girmamawa da darajtawa tsakaninsa da mahaifinsa a kan wadannan abubuwa da yake ambato, ya manta babbar alakar dake tsakaninsu ta zamantowarsa mahifinsa kamar yadda wancan dalibi baragurbi ya manta alakarsa da malaminsa ta zamantowarsa malaminsa wanda yake nuna masa addininsa. Allah ya yi mana da kyau. Amin.