Ramadhaniyyat@1439H [6]
Hatsarin Bidi'a A Addini
1.Dan bidi'a mutum ne mai yi wa Shari'a gardama, mai yin hannun riga da ita, saboda Allah da Manzonsa sun bayyana wa bawa wasu hanyoyi na musamman da zai sami biyan bukatunsa na addini. Suka kuma umarci kowa da ya tsaya a kansu kada ya kuskura ya ketare su.
2.Wadannan hanyoyi na musamman kuwa sun kunshi umarni da hani da alkawarin sakamakon lada da na narkon azaba
3.Suka kuma bayyana cewa, dukkan alheri ya tattara cikin bin wannan hanyar, haka kuma sharri duka yana tare da kauce mata da bin wata hanyar daban.
4.Domin Allah shi ne ya san komai mu ba mu san komai ba, shi ne kuma ya aiko da Manzonsa don ya zama rahama ga talikai.
5.Dan bidi'a ya sa kafafunsa ya shure wannan batu duka, domin kuwa shi yana ganin cewa akwai wasu hanyoyi na daban da ya gano ba wadanda Shari'a ta zo da su ba, sannan kuma hanyoyin da ita Shari'a ta shimfida ta yi umarni a bi su bai zama dole sai an bi su ba. Kai kamar ma yana cewa Allah ya sani shi ma kuma ya sani, ko ma ana iya gane cewa yana fifita saninsa a kan na Allah da Manzonsa, saboda karin da yake shigo musu da shi a cikin Shari'a. To idan kuwa har zai zamanto wannan shi ne abin da yake gani to lalle kuwa ya kafirce wa Shari'ar da mai Shari'ar. Idan kuwa ba haka yake nufi ba, to lalle abin da yake kai na bidi'a bata ne mai girma.
As-Shatibi, Al-I'itisam, juzu'i na1, shafi na 65.