Subscribe Our Channel

Ramadhaniyyat@1439H [5]

Dr. Sani Umar

Munafurci Da Munafukai

1. A lokacin da Annabi (SAW) yake zaune a Makka mutane kashi biyu ne: muminai sai kafirai. To amma bayan Musulmai sun yi hijira zuwa Madina, sai aka samu kashi na uku, su ne munafukai.
2. Don haka babu munafuki ko daya daga cikin mutanen Makka da suka yi hijira zuwa Madina. An sami munafukai ne a cikin mutanen Madina kawai.
3. Munafiki shi ne wanda yake bayyana Musulunci a bakinsa, amma yana voye kafirci a zuciyarsa.
4. Munafukai iri biyu ne:
Nau'i na farko su ne: Kafirai wadanda suke boye kafircinsu suna bayyan imani a zahiri, kamar wanda a zahiri zai nuna ya yi imani da Allah da Littafinsa da Manzonsa, amma azuciyarsa yana karyata su. Wannan shi ne munafurci babba.
Nau'i na biyu, su ne musulmin da za su boye sabon Allah amma sai su rika bayyana biyayya ga Allah a zahiri, kamar mutumin da zai nuna shi mai amana ne mai cika alkawari amma yana boye ha'incinsa ne da yaudararsa. Ya nuna shi mai gaskiya ne amma ba haka yake ba. Wannan shi ne karamin munafurci.
5. Ana samun munafukai ne duk lokacin da Musulunci yake da karfi da kwarjini ake tsoronsa. Amma yayin da Musulmi suka yi rauni to sai ka ga duk wani baragurbin Musulmi ya bayyana kansa a fili, ya cire nikabin kunya da tsoro daga fuskarsa. Wannan shi ne halin da al'ummar Musulmi take ciki a yau.
6.Ana yi wa munafuki mu'amala irin wadda ake yi wa Musulmi

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter