Ramadhaniyyat@1439H [13]
Giba: Fuskokinta Na Halal
Giba haramun ce. Amma tana halatta a wasu lokuta shida:
1. Na farko, ga wanda aka zalunta, ya rika magana a kan wanda ya zalunce shi gwargwadon yadda yake zaton zai iya samun hakkinsa daga wajensa; ko ya yi maganarsa a gaban wanda yake tsammanin zai iya taimaka masa da shawara ko ya karbo masa hakkinsa.
2. Na biyu, Bayani a kan halayen wanda ake da bukatar bayanin a kansa; kamar bayani a kan maruwaita hadisai don banbnce mai karya da mai gaskiya daga cikinsu; ko kuma bayani don a gane wanda ake nufi da magana, kamar a ce ‘wane gurgu, wane makaho ko gajere da makamantan haka.
3. Na uku, gargadi game da wani mai mummunan hali ga wanda ake tsoron zai iya cutar da shi, kamar bayyana halin maha’incin dan kasuwa don gudun kada wani ya saki jiki ya cuce shi, ko mutumin da yake nuna shi nagartacce ne alhalin ba haka ne ba, don yana son ya auri wata.
4. Na hudu, mai bayyana fasikancinsa a fili, kamar mai bayyan shan giya, ko matar da take yawo bainar jama’a da mummunar shiga. Ambaton irin wadannan da halinsu da aka son su da shi ba giba ba ce.
5. Na biyar, mai neman fatawa a kan wata masa’alar da lalle sai ya ambaci wani wanda wannan fatawar take da alaka da shi; kamar mace ta yi fatawa a kan mijinta ko miji ya yi fatawa a kan matarsa
6. Na shida, neman taimako a kan mai barna, don hana shi barnarsa. Babu laifi a fada wa wanda yake da ikon taimakawa wajen gyaransa irin barnar da yake yi ko da kuwa a boye yake yin ta, domin yin haka taimaka masa ne.