Ramadhaniyyat@1439H [12]
Jarrabar Allah: Banbanci Tsakanin Mumini Da Kafiri
Allah Ta’ala yana cewa:
(Kuma lalle mun aika da (manzanni) zuwa ga al’ummun da suka gabace ka, sai muka dora musu tsananin talauci da cutuka ko sa kaskantar da kai.
To me ya hana lokacin da musibarmu ta zo musu, su kaskantar da kai? Sai dai kuma zukatansu ne suka kekashe, Shaidan kuma ya kawata musu abin da suka kasance suna aikatawa.
To yayin da suka yi watsi da abin da aka yi musu wa’azi da shi, sai muka bude musu kofofin kowane irin abu, har zuwa lokacin da suka yi fariya da abin da aka ba su, sai muka damke su ba zato ba tsammani, sai ga su suna masu yanke kauna (daga kowane alheri).
Abubuwan lura daga wandannan ayoyi su ne:
1.Talauci da wadata da cuta da lafiya, duk abubuwa ne da mutanen kirki suke samun darussa daga gare su, su wa’azantu.
2.Shi ya sa duk al’amarin mumini alheri ne gare shi; idan abin farin ciki ya same shi sai ya gode wa Allah, sai ya zame masa alheri; idan kuwa abin bakin ciki ne ya same shi sai ya yi hakuri, sai hakan ya zama alheri a gare shi. Kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya fada [Duba, Muslim #2999].
3.Amma wanda ba mumini ba idan yana cikin damuwa da matsi, ba zai dauki darasi ba balle ya koma ga Allah, ya bauta masa shi kadai. Ko da ya kirawo Allah yana neman taimakonsa, to na wani dan lokaci ne; da zarar an yaye masa masifar da yake ciki sai ya sake komawa ga kafircinsa.
4.Idan kuwa ni’ima ce Allah ya nufe shi da ita, to sai ya yi ta dagawa da girman kai ga Ubangiji, sai Allah ya yi masa talala har sai lokacin da ya kama shi ba zato ba tsammani a lokacin da ba zai iya kubuta ba.