Ramadhaniyyat@1439H [11]
Daga Shiriyar Alkur’ani Mai Girma
Allah Ta’ala ya ce:
(Kuma in da a ce lallai mun wajabta musu cewa: “Ku kashe kawunanku ko ku fita daga gidajenku,” da ‘yan kadan ne daga cikinsu za su aikata hakan. Da a ce sun aikata abin da ake musu wa’azi da shi, to da ya fi alheri, kuma da ya fi tsananin tabbatar da su (a kan hanya madaidaiciya). [An-Nisa’i, aya ta 66].
Daga wannan aya za mu iya fahimtar abubuwa kamar haka:
1. Bayanin raunin dan’adam da cewa, ba zai iya aikata duk abin da aka umarce shi ba, musamman idan akwai raunin imani.
2. Yi wa Allah da’a da bin umarninsa shi ne hanyar dacewa da kowane alheri.
3. Gwargwadon aikin mutum shi ne gwargwadon sakamakonsa. Idan mutum ya yi aiki mai kyau karbabbe a wajen Allah, to wannan aiki nasa zai haifar masa da wani aikin mai kyau a matsayin sakamako gare shi.
4. Nuna wa dan’adam ya nemi falala a wurin Allah () domin tasa ce, shi ne mai ba da ita ga wanda ya ga dama.
5. Fitar da mutane daga gidajensu abu ne mai ciwon gaske, dubi yadda Allah a nan ya hada shi da kashe kai.
6. Bacin maganar masu cewa, mutum ya bauta wa Allah ba don tsoron wutarsa ba, ba kuma don kwadayin Aljannarsa ba. Idan haka gaskiya ne, to da fadar za a ba da lada mai yawa ya zama ba shi da wani amfani a ayar. Domin Allah () bai kawo ambaton ‘lada’ ba, ya kuma kwadaitar a kan a yi aiki a same shi, sai domin kasancewarsa ba zai raunana niyya ba, kuma bai saba wa ikhlasi ba. Allah () ya siffanta Annabinsa () da sahabbansa da cewa, suna ibada, suna neman wata falala daga Allah. [Dubi Suratul Fathi, aya ta 29].