Ramadhaniyyat@1439H [10]
Zuciya
1. Allah Ta’ala yana cewa:
(Ya Ubangijinmu, kada ka karkatar da zukatanmu bayan ka shiryar da mu, kuma ka yi mana rahama daga gare ka. Lalle kai Mai yawan baiwa ne) [Ali-Imran, aya ta 8].
2. Zuciya tana da hali guda biyu, halin daidaita da kuma halin karkata, don haka mutum a ko da yaushe yana bukatar ya rika rokon Allah da kada zuciyarsa ta karkace, domin ba a hannunsa take ba, tana hannun Allah ne, shi ne yake yin yadda ya ga dama da ita.
3. Don haka kada mutum ya rudu da kansa, ya dogara a kan imaninsa, sau tari an sami mai imanin da ya tabe, ya saki hanya.
4. Ya yawaita neman agajin Allah a kan ya tabbatar da dugadugansa a kan shiriya, ka da ya bar shi santsi ya kwashe shi zuwa ga ramin halllaka ba tare da ya ankara ba.
5. An karbo daga Abdullahi dan Amru (t) ya ce, Annabi (r) ya ce: “Lallai zukatan ‘yan’adam duka suna tsakanin yatsu biyu ne daga yatsun Allah Mai rahama, tamkar zuciya daya, yana sarrafa su yadda ya ga dama.” Sannan sai Annabi (r) ya yi addu’a yana cewa: “Ya Allah Mai sarrafa zukata, ka sarrafa zukatanmu a kan da’arka.” [Muslim #2654].