Subscribe Our Channel

Ramadhaniyyat1439H [2]

Rubutawa: 
Dr. Muh'd Sani Umar R/Lemu
Mafi Mamakin Abubuwa

1. Mutum ya san wane ne Allah amma ya ki sonsa, ya kuma ji mai kiransa yana kira amma ya ki amsa masa.
2. Hakanan ya san ribar dake cikin mu'amala da shi amma ya bar shi ya koma yana mu'amala da waninsa.
3. Ko ya san girman fushinsa amma ya tsokano shi.
4. Ko ya dandani radadin dake cikin kewar sabonsa, amma ya ki neman gusar da wannan kewa ta hanyar yi masa da'a.
5. Ko ya dandani kuncin zuciya saboda kutse a cikin ambaton waninsa sannan ya ki sha'awar yalwal kirjin dake cikin ambatonsa da ganawa da shi.
6. Ko ya dandani azabar kamuwa da son waninsa, amma kuma ya gagara guduwa zuwa ga ni'imar dake tattare da komawa gare shi da mayar da al'amari wajensa.
7. Abin da ya fi wadannan mamaki duka shi ne mutum ya  san cewa dole ne sai ya nemi taimakonsa ba kuma zai iya rayuwa ba sai da shi, amma kuma sai ya rika guje masa yana nisantarsa.
Ibnul Kayyim, Al-Fawa'id, shafi 47.

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter