Rubutawa:
Dr. Muh'd Sani Umar R/Lemu
Inuwar Alkur'ani1. Rayuwa a karkashin inuwar Alkur'ani ni'ima ce da babu mai sanin dandanonta da gardinta sai wanda ya same ta.
2. Wanda ya rayu a karkashin inuwar Alkur'ani zai gane cewa babu wani abu mai mahimmanci kamar kulla kyakkyawar alaka tsakanin bawa da Ubangijinsa.
3. Wanda ya rayu karkashin inuwar Alkur'ani zai fahimci girmamawar da Allah ya yi wa dan'adam duk kuwa da kakantar halittarsa idan ka kwatanta shi da sauran manya-manyan halittu dake sama ko a kasa. Amma duk da haka sai ga shi Allah yana magana da shi domin ya shiryar da shi ya kuma dora shi a kan madaidaiciyar hanya.
4. Wanda yake rayuwa a karkashin inuwar Alkur'ani zai rika ganin wautar masu tinkaho da duniya masu homa da sabon Allah masu yin biyayya ga makiya Allah da Manzonsa.
5. Wanda yake ruyuwa a karkashin inuwar Alkur'ani shi ne yake karantar hakikanin rayuwa yadda take, zai gane alakarsa da sauran halittun Allah na sama da na kasa. Shi ne wanda ya fahimci dalilin samuwarsa a wannan duniya, ya kuma san ina ya dosa a cikin tafiyarsa a ban kasa.
6. Babu wani lokaci da mumini yakan kara kusantar Alkur'ani yakan kara karfafa alakarsa da shi kamar watan Ramadan watan Alkur'ani.
7. Ma'aiki (S.A.W) da kansa yakan kara dankon alakarsa da Alkur'ani a wannan watan fiye da kowane wata yayin da yake bitarsa tare da Mala'ika Jibrilu (AS).
8. Don haka wannan dama ce a gare mu da mu shiga rayuwa a karkashin inuwar Alkur'ani domin mu dandani babbar ni'imar dake cikinta. Allah ya sa mu dace. Amin.