QISSAR IMAMUL HARAMAINI ABUL MA'ALIY AL- JUWAINIY TARE DA ABU JA'AFAR AL- HAMAZANIY A KAN DAUKAKAR ALLAH A SAMAN AL'ARSHINSA
Al- Imamuz Zahabiy (r) ya ambata a cikin littafinsa Tarikhul Islami ya ce:
وذكر محمد بن طاهر أن المحدث أبا جعفر الهمذاني حضر مجلس وعظ أبي المعالي، فقال: كان الله ولا عرش، وهو الآن على ما كان عليه. فقال أبو جعفر: أخبرنا يا أستاذ عن هذه الضرورة التي نجدها، ما قال عارف قط: يا الله؛ إلا وجد من قلبه ضرورة تطلب العلو، لا نلتفت يمنة ولا يسرة، فكيف ندفع هذه الضرورة عن أنفسنا. أو قال: فهل عندك من دواء لدفع هذه الضرورة التي نجدها؟ فقال: يا حبيبي، ما ثم إلا الحيرة. ولطم على رأسه ونزل، وبقي وقت عجيب، وقال فيما بعد: حيرني الهمذاني.
تاريخ الإسلام ت بشار (10/ 427 - 428)، العلو للعلي الغفار (ص: 259)
"Muhammad bn Dahir (Malamin Hadisin Sufaye) ya ambata cewa: Malamin Hadisin nan Abu Ja'afar Al- Hamazaniy (Al- Sufiy) ya halarci majalisin wa'azin Imamul Haramaini Abul Ma'aliy Al- Juwainiy sai ya ce: Allah ya kasance a lokacin da babu Al'arshi, a yanzu kuwa yana kan abin da ya kasance a kansa a farko. (Ma'ana: tun da ya nuna cewa; tun a farko Allah yana nan a lokacin da babu Al'arshi, saboda Al'arshin Allah ne ya halicce shi, to don haka yanzu ma yana kan abin da yake ne a tun farkon, wato dai yana kore daukakar Allah a saman Al'arshinsa).
Sai Abu Ja'afar Al- Hamazaniy ya ce: Ya Ustazu, ba mu labari a game da wannar larura da muke jinta a zuciyarmu, babu wani Arifi (Sufiy masanin Allah) da ya taba cewa: Ya Allah! face sai ya ji zuciyarsa tana neman sama a bisa dole. (Ma'ana: daga ya kira sunan Allah sai ya ji zuciyarsa ta nufi sama saboda a dole zuciyar tana jin cewa: Allah a sama yake), ba ma juyawa dama ko hagu. Don haka ta yaya za mu iya ture wannar lurara (abin da yake faruwa a bisa dale, ko mutum ya ki ko ya so) daga zukatanmu?
Ko kuma cewa ya yi: Shin kana da maganin wannar Lurara (abin da yake samunmu a dole) wanda muke jinsa a zukatanmu na jin cewa: Allah a sama yake?
Sai ya ce: Ya masoyina, ai babu wani abu face ka rudar da ni. Sai ya fara marin kansa, ya sauka daga minbarin wa'azin, ya zauna lokaci yana mamaki, yana cewa: AL- HAMAZANIY YA RUDAR DA NI".
SABODA HAKA DAGA CIKIN DALILAI MAFI GIRMA A KAN DAUKAKAR ALLAH A SAMAN DUKKAN HALITTUNSA AKWAI ITA WANNAR FITIRA DA ALLAH YA HALICCI DUKKAN BAYINSA A KANTA, NA CEWA; KOWA A CIKIN ZUCIYARSA DOLE YANA JIN CEWA: ALLAH A SAMA YAKE, BA A CIKIN HALITTUNSA BA, BALLE ACE: YANA KO'INA, HAR WANI YA CE: ALLAH YA ZAMA KOMAI, KOMAI ALLAH NE.
SUBHANALLAH.