Subscribe Our Channel

HUKUNCE - HUKUNCEN MUQALLIDI (MABIYI) A MAS'ALOLIN SABANI

Da ace: kowa zai san matsayinsa a cikin Mas'alolin Ilimi da na Hukunce – hukuncen Addini, kuma ya tsaya a kan matsayin nasa da ba a samu sabani abin zargi a tsakanin Ahlus Sunna ba.

Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya (r) ya ce:
"فمن صار إلى قول مقلدا لقائله لم يكن له أن ينكر على من صار إلى القول الآخر مقلدا لقائله، لكن إن كان مع أحدهما حجة شرعية وجب الانقياد للحجج الشرعية إذا ظهرت.
ولا يجوز لأحد أن يرجح قولا على قول بغير دليل، ولا يتعصب لقول على قول ولا لقائل على قائل بغير حجة، بل من كان مقلدا لزم حكم التقليد، فلم يرجح ولم يزيف ولم يصوب ولم يخطئ، ومن كان عنده من العلم والبيان ما يقوله سمع ذلك منه، فقبل ما تبين أنه حق، ورد ما تبين أنه باطل، ووقف ما لم يتبين فيه أحد الأمرين، والله تعالى قد فاوت بين الناس في قوى الأذهان، كما فاوت بينهم في قوى الأبدان. وهذه المسألة ونحوها فيها من أغوار الفقه وحقائقه ما لا يعرفه إلا من عرف أقاويل العلماء ومآخذهم فأما من لم يعرف إلا قول عالم واحد وحجته دون قول العالم الآخر وحجته، فإنه من العوام المقلدين لا من العلماء الذين يرجحون ويزيفون، والله تعالى يهدينا وإخواننا لما يحبه ويرضاه".
الفتاوى الكبرى لابن تيمية (1/ 175)، مجموع الفتاوى (35/ 233)

"Duk wanda ya kasance a kan wani ra'ayi yana mai taqlidanci (koyi) ma wanda ya fadi ra'ayin, bai halatta gare shi ya yi inkari ma wanda ya tafi a kan daya ra'ayin yana mai taqlidanci wa mai ra'ayin ba. Sai dai idan daya daga cikinsu yana da hujja ta Shari'a wajibi ne a mika wuya ga hujjojin Shari'a idan sun bayyana a fili. Bai halatta ga wani mutum ya rinjayar da wani ra'ayi a kan wani ba tare da dalili ba, ko ya yi ta'assubanci ga wani ra'ayi a kan wani ra'ayi ba, ko ya yi ta'assubanci ga wani mai ra'ayi a kan wani ba tare da hujja ba, a'a, duk wanda ya kasance shi mai taqlidanci ne to ya lazimci hukuncin taqlidancin; kada ya rinjayar da wani ra'ayi a kan wani, kada ya rushe wani ra'ayi, kada ya gyara wani ra'ayi a kan wani, kada ya kuskurantar da wani ra'ayi a kan wani. Amma duk wanda ya kasance yana da ilimi da bayani a kan abin zai fada za a saurare shi, sai a karbi abin da ya bayyana cewa shi ne gaskiya, sai kuma a jefar da abin da yake batacce ne, kuma sai a dakata a kan abin da daya daga cikin wadannan abubuwa biyu bai bayyana ba.

Allah Madaukaki ya fifita tsakanin mutane a karfin kwakwalwa kamar yadda ya fifita tsakaninsu a karfin jiki.

Ita wannar mas'ala da makamantanta (wata mas'ala ce da yake magana a kanta) a cikinta akwai zurfafan Fiqhu da hakikaninsa wanda babu wanda ya sansu sai wanda ya san duka maganganun Malamai da tushen da suke kafa maganganun nasu a kansu. Amma wanda ra'ayin malami guda daya kawai da hujjarsa ya sani, bai san ra'ayin wani malamin da hujjarsa ba, to shi yana cikin gama garin mutane masu kokkoyon malamai ne (masu taqlidanci) ba cikin malamai wadanda suke iya rinjayar da ra'ayi a kan ra'ayi kuma suke iya rushe ra'ayi a kan wani ra'ayi ba".

ABIN LURA:
1- Mas'alolin Ijtihadi da ake sabani a kansu a tsakanin Ahlus Sunna bai kamata su zama abin tsanantawa da zafafa inkari a kansu ba.
2- Bai ya halatta ga wani mutum ya rinjayar da wani ra'ayi a kan wani ba tare da dalili bayyananne ba.
3- Duk wanda yake matsayin Muqallidi (mabiyi) ba Malami (mai Ijtihadi) ba to bai halatta gare shi ya rinjayar da wani ra'ayi a kan wani ba, ko ya rushe wani ra'ayi ba, ko ya gyara wani ra'ayi a kan wani ba, ko ya kuskurantar da wani ra'ayi a kan wani ba, balle kuma ya tsangwami wanda ya tafi a kan wani ra'ayi da ya saba ma nasa ba.
4- Duk lokacin da Hujja ta Shari'a ta bayyana wa mutum a bisa sabanin ra'ayin da yake kai, to wajibi ne ya ajiye ra'ayin nasa ya bi Hujja ta Shari'a.
5- Irin mas'alolin da Ahlus Sunna suke sabani a kansu, sawa'un tsakanin bangarorin Izala guda biyu, ko tsakanin 'Yan Salafiyya ko 'Yan Kungiyar Salafiyyun ko 'Yan Ba-kungiya tsakaninsu da sauran Ahlus Sunna duka da za a tafi a kan wannar ka'ida da an zauna lafiya.

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter