FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (3)
Wanda ya yi "Istimna'i" ya fitar da maniyyi da hanunsa ko da wani abun, Azuminsa ya baci. A baya an yi ishara a kan wannan.
Wanda Maziyyi ya fito masa saboda kallon mace ko abin da ya yi kamata da haka Azuminsa bai baci ba. Al-Ba'aliy a cikin "Ikhtiyaraatu Shaikhil Islam Ibnu Taimiyya" ya ce:
ولا يفطر بمذي سببه قبلة، أو لمس، أو تكرار نظر، وهو قول أبي حنيفة والشافعي، وبعض أصحابنا.
الاختيارات للبعلي (160)
"Azuminsa ba zai karye ba saboda fitan Maziyyi, imma saboda sunbanta ko shafan mace ko maimaita kallonta. Wannan shi ne fadin Abu Hanifa da Shafi'iy da wasu a cikin Hanabila".
Ibnu Muflih ya ce:
وإن مذى بذلك أفطر أيضا، نص عليه "وم" واختار الآجري وأبو محمد الجوزي وأظن وشيخنا: لا يفطر، وهو أظهر "وهـ ش" عملا بالأصل، وقياسه على المني لا يصح، لظهور الفرق.
الفروع وتصحيح الفروع (5/ 10)
"In Maziyyi ya fito masa saboda runguma to Azuminsa ya baci...
Amma Shaihinmu (Ibnu Taimiyya) ya ce: Azuminsa bai baci ba, kuma wannan shi ne mafi inganci (shi ne fadin Abu Hanifa da Shafi'iy), saboda aiki da asali. Amma yin kiyasin Maziyyi a kan Maniyyi abu ne da bai inganta ba, saboda akwai banbanci tsakaninsu".
Saboda haka fitar da Maniyyi da gangan yana karya Azumi, amma fitan Maziyyi saboda kallon mace ko magana da ita, ko wani abun daban ba ya karya Azumi.
Amma fa kar mu manta, akwai abubuwa da ba sa karya Azumi amma kuma suna rage ladan Azumin. Don haka kar mu manta da babbar manufar Azumi, wato samar da Taqwa.