FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (4)
Kowa ya sani, saduwa (jima'i) da rana da gangan a watan Ramadhan yana bata Azumin mutum, kuma yana wajabta ramuko da kaffara. To amma idan mutum ya sadu da iyali kusan Asubahi fa, yana zaton da sauran lokaci ashe bai sani ba tun tuni Alfijir ya keto, ko kuma ya manta ya sadu da iyalinsa da rana tsaka, BISA MANTUWA, me ya wajaba a kansa?
To Malamai sun yi sabani a kan haka, daga cikin Malaman Salaf akwai wadanda suka ce: BABU RAMUKO A KANSA, BALLE KAFFARA.
Wannan shi ne abin da Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya ya rinjayar, kuma shi ne zabinsa kamar yadda Almajirinsa Ibnu Muflih ya fada a cikin "Al-Furu'u" (5/ 41).
Shaikhul Islami ya ce:
وهذا القول أصح الأقوال وأشبهها بأصول الشريعة ودلالة الكتاب والسنة وهو قياس أصول أحمد وغيره فإن الله رفع المؤاخذة عن الناسي والمخطئ. وهذا مخطئ وقد أباح الله الأكل والوطء حتى يتبين الخيط الأبيض من الخيط الأسود من الفجر واستحب تأخير السحور ومن فعل ما ندب إليه وأبيح له لم يفرط فهذا أولى بالعذر من الناسي.
مجموع الفتاوى (25/ 264)
"Wannar fahimta ta fi sauran inganci, kuma ta fi dacewa da ka'idojin Shari'a da dalilan Alkur'ani da Sunna, kuma kiyasi ne bisa ka'idojin Imam Ahmad da waninsa cikin Malamai. Saboda Allah ba zai kama mai mantuwa da mai kuskure ba. Wannan kuwa mai kuskure ne, Allah ya halasta masa ci da saduwa da iyali har sai farin zare ya bayyana daga bakin zare na Alfijir (sai hasken Alfijir ya bayyana daga duhun dare), kuma an sunnanta jinkirta Suhur, don haka duk wanda ya aikata abin da aka sunnanta masa ko aka halasta masa ba tare da sakaci ba, to wannan shi ya fi cancantar uzuri fiye da mai mantuwa".
Saboda haka, duk wanda ya yi saduwa (jima'i) da rana, wato tsakanin fitowan Alfijir har zuwa faduwar rana, da gangan, da saninsa, Azuminsa ya baci. Kuma ramuko da kaffara sun wajaba a kansa.
Amma wanda hakan ya faru da shi, cikin mantuwa, ko cikin rashin sanin ketowan Alfijir, to babu komai a kansa, kawai zai cigaba da Azuminsa ne, babu ramuko a kansa balle kaffara.
Alal hakika duk wanda ya fahimci Shari'a a dunkulenta, bisa ka'idojinta da gamayyar dalilan Shari'a zai ga cewa; lallai wannar fahimta ita ce mafi inganci kuma mafi karfin dalilai.
Allahu A'alam.