FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (9)
Shin Gulma da Giba da Annamimanci da Zagin mutane suna karya Azumi?
Ya tabbata cikin Hadisin da Imamul Bukhari ya riwaito da isnadinsa:
عن أبي هريرة رضي الله عنه، قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «من لم يدع قول الزور والعمل به، فليس لله حاجة في أن يدع طعامه وشرابه»
صحيح البخاري (3/ 26)
Daga Abu Huraira (ra), Annabi (saw) ya ce:
"Duk wanda bai bar yin maganar karya ko aiki da ita ba, to Allah ba ya bukatar ya bar cin abinci da shan abin shansa (Allah ba ya bukatar Azuminsa)".
Wannan ya sa wasu Malamai cikin Salaf suke ganin gulma da cin naman mutane da annamimanci suna karya Azumin mutum. Wasu Malaman kuma suna ganin ba ya karyawa.
Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya ya fayyace mas'alar inda ya ce:
"وتحقيق الأمر في ذلك أن الله تعالى أمر بالصيام لأجل التقوى وقد قال صلى الله عليه وسلم: "من لم يدع قول الزور والعمل به فليس لله حاجة في أن يدع طعامه وشرابه"، فاذا لم تحصل له التقوى لم يحصل له مقصود الصوم فينقص من أجر الصوم بحسب ذلك".
مختصر الفتاوى المصرية (ص: 289)
"Tantance magana a kan haka shi ne; lallai Allah Madaukaki ya yi umurni da yin Azumi ne don samar da Taqwa da jin tsoronsa, kuma Annabi (saw) ya ce:
"Duk wanda bai bar yin maganar karya ko aiki da ita ba, to Allah ba ya bukatar ya bar cin abinci da shan abin shansa".
To idan Taqwar ba ta samu ga mai Azumi ba, to ba a samu manufar da ake so na yin Azumin nasa ba, don haka zai tauye ladansa gwargwadon munanan abin da ya aikata".
Saboda haka Azuminsa yana nan, amma kuma ba shi da ladan Azumin.
Don haka matukar mutum yana Azumi, amma bai kiyaye harshensa daga maganganun banza da karerayi da gulman mutane da zaginsu da cin namansu ba, to wahalar banza kawai yake sha, ba zai samu ladan komai ba, saboda Allah ba ya bukatar Azumin da ba zai samar da Taqwa ma bawa, ta hanyar kare gabobinsa daga aikata munanan aiyuka ba.