Subscribe Our Channel

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (8)

Da Nassin Alkur'ani Allah ya saukaka wa Matafiyi da Maras lafiya yin Azumin Ramadhana a halin tafiya ko rashin lafiya. Don haka ya halasta su sha Azumi sai su rama Azumin da suka sha bayan Ramadhan, in uzurin nasu ya gushe. A kan wannan Musulmai suka yi Ijma'i.

Don haka Maras lafiya da ake nufi shi ne wanda ba zai iya yin Azumin ba saboda rashin lafiya ko kuma in ya yi rashin lafiyan nasa zai karu.

Shaikhul Islami ya ce:
المريض الذي لا يطيق الصيام أو الذي يزيد الصوم في مرضه؛ له أن يفطر، وإن تحمل وصام وأجزأه
شرح العمدة لابن تيمية (1/ 208)

"Maras lafiya shi ne wanda ba zai iya yin Azumi ba, ko wanda Azumin zai kara masa rashin lafiyan nasa. Amma idan ya jure ya yi Azumin to ya isar masa ba sai ya rama ba".

To a kan samu wasu masu lafiya amma kuma in sun yi Azumin za su kamu da rashin lafiya, to su ma ana kiyasinsu a kan marasa lafiya, saboda haduwarsu cikin illarn hukuncin, wato samun shan wahala.

Shaikhul Islam ya ce:
وفي معنى المريض الصحيح الذي يخاف من الصوم مرضا أو جهدا شديدا، مثل من به عطاش لا يقدر في الحر على الصوم، وهو يقدر عليه في الشتاء، أو امرأة قد حاضت والصوم يجهدها.
شرح العمدة لابن تيمية (1/ 209)

"Mai lafiyan da yake tsoron kamuwa da rashin lafiya, ko yake tsoron wahala mai tsanani shi ma zai shiga cikin ma'anar maras lafiya, misalin wanda yake da jin kishin ruwan da ya kai ba zai iya yin Azumi a zafi ba, sai a lokacin sanyi ne kawai zai iya yi, ko matar da bayan ta yi al'ada Azumin yana wahalar da ita".

Saboda haka hukuncin Maras lafiya ko wanda yake tsoron kamuwa da rashin lafiya in ya yi Azumi shi ne ana so kar ya yi Azumin, kuma ba a so ya yi, wato yin nasa Makruhi ne.

Shaikhul Islam ya ce:
إن المريض يستحب له الفطر، ويكره له الصوم، فإن صام أجزأه.
شرح العمدة لابن تيمية (1/ 209)

"Maras lafiya ana so ya sha Azumi, ba a son ya yi Azumin, amma in ya yi Azumin ya isar masa ba zai yi ramuko ba".

Wannan sauki ne na Shari'a, saboda Allah yana son bayinsa da sauki ne, ba ya so su shiga tsanani da wahala. Allah ya ce:
{يُرِيدُ اللَّهُ بِكُمُ الْيُسْرَ وَلَا يُرِيدُ بِكُمُ الْعُسْرَ } [البقرة: 185]

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter