Subscribe Our Channel

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (6)

Mutane sun kasu kashi biyu wajen karya Azuminsu:
1- Akwai mai ganganci. Wannan dole ya rama Azumin da ya karya, in kuma saduwa ne (jima'i) dole ya yi kaffara bayan ya yi ramuko.
2- Akwai mai kuskure, ko mantuwa, ko rashin sani (jahilin da bai san hukunci ba ko bai san yadda ake yi ba). Wannan babu ramuko in ya karya Azuminsa bisa kuskure, ko mantuwa ko rashin sani balle kuma kaffara.

Wasu Malaman sun banbanta tsakanin mai manyuwa da jahili maras sani wajen karya Azumi. Al-Imam Ibnul Qayyim ya ce:
قستم الجاهل على الناسي في عدة مسائل وفرقتم بينهما في مسائل أخر، ففرقتم بينهما فيمن نسي أنه صائم فأكل أو شرب لم يبطل صومه، ولو جهل فظن وجود الليل فأكل أو شرب فسد صومه، مع أن الشريعة تعذر الجاهل كما تعذر الناسي أو أعظم؟ كما عذر النبي -صلى الله عليه وسلم- المسيء في صلاته بجهله بوجوب الطمأنينة فلم يأمره بإعادة ما مضى...
وعذر عدي بن حاتم بأكله في رمضان حين تبين له الخيطان اللذان جعلهما تحت وسادته ولم يأمره بالإعادة
إعلام الموقعين (3/ 10)

"Kun yi kiyasin jahili maras sani a kan mai mantuwa a mas'aloli da yawa, amma sai kuma kuka raba tsakaninsu a wasu mas'alolin, sai kuka raba tsakaninsu a mas'alar mai Azumi idan ya manta ya ci abinci ko ya sha abin sha, kuka ce: Azuminsa bai baci ba, amma sai kuka ce: idan bai sani ba, sai ya yi zaton akwai sauran dare, sai ya ci ko ya sha Azuminsa ya baci, alhali Shari'a tana yin uzuri ga jahili kamar yadda take yi wa mai mantuwa ko ma fiye da haka, kamar yadda Annabi (saw) ya yi uzuri ga wanda ya munana Sallarsa saboda ya jahilci wajabcin nitsuwa a cikin Sallah, sai bai umurce shi da ramukon Sallolinsa na baya ba...
Haka kuma Annabi (saw) ya yi uzuri ga Adiyyi bn Hatim (ra) a kan cin abinci da ya yi a Ramadhan har sai da gari ya waye wartal, har sai da ya iya banbance tsakanin farin zare daga bakin zare, wadanda ya sanya su a karkashin filonsa, amma Annabi (saw) bai umurce shi da ramuko ba".

Saboda haka jahili mai halin rashin sani dadai yake da mai kuskure ko mantuwa a wajen karya Azumi, duka babu ramuko a kansu. Wannan shi ne zabin Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya kamar yadda Almajirinsa Al-Imam Ibnul Qayyim ya hakaito inda ya ce:
تناقضوا كلهم في جعل الناسي في الصوم أولى بالعذر من الجاهل، ففطروا الجاهل دون الناسي، وسوى شيخنا بينهما، وقال: الجاهل أولى بعدم الفطر من الناسي
إعلام الموقعين (5/ 506)

"Masu Qiyasi gaba dayansu sun yi tufka da warwara ta yadda suka sanya mai mantuwa a Azumi shi ya fi cancantar uzuri feye da jahili mai rashin sani, sai suka ce: Azumin jahili ya baci, amma in mai mantuwa ne Azuminsa bai baci ba. Amma Shehinmu (Ibnu Taimiyya) ya daidaita tsakaninsu, ya ce: Jahili shi ya fi cancantar a ce: Azuminsa bai baci ba fiye da mai mantuwa".

Saboda haka duk wanda ya karya Azuminsa saboda mantuwa ko kuskure ko rashin sani to babu ramuko ko kaffara a kansa, kawai zai ci gaba da Azuminsa ne, Azuminsa yana nan bai baci ba. A kan haka Shaikhul Islami ya ce:
قد ثبت بدلالة الكتاب والسنة أن من فعل محظورا مخطئا أو ناسيا لم يؤاخذه الله بذلك وحينئذ يكون بمنزلة من لم يفعله فلا يكون عليه إثم ومن لا إثم عليه لم يكن عاصيا ولا مرتكبا لما نهي عنه وحينئذ فيكون قد فعل ما أمر به ولم يفعل ما نهي عنه. ومثل هذا لا يبطل عبادته إنما يبطل العبادات إذا لم يفعل ما أمر به أو فعل ما حظر عليه.
مجموع الفتاوى (25/ 226)

"Ya tabbata da dalilan Alkur'ani da Sunna cewa; duk wanda ya aikata wani abu da aka hana a halin kuskure ko mantuwa to Allah ba zai kama shi a kan haka ba, a wannan halin zai zama kamar bai aikata laifin ba, don haka babu zunubi a kansa, duk wanda babu zunubi a kansa kuwa to shi ba mai sabo ba ne, ko bai zama wanda ya aikata abin da aka hana ba. To a wannan lokaci sai ya kasance ya aikata abin da aka umurce shi, bai aikata abin da aka hana shi ba. Irin wannan kuwa ibadarsa ba ta baci, kawai ibada tana baci ne ne idan mutum bai aikata abin da aka umurce shi ya aikata ba, ko kuma in ya aikata abin da aka hana shi aikatawa".

Lallai wannar ka'ida ce ta Shari'a mai girma wajen hukunci wa mutane da aiyukansu, rashin sanin irin wannar ka'ida ne yake jefa jahilai da masu guluwwi cikin kuskure wajen hukuncinsu ga mutane ko a kan aiyukansu.

Allahu A'alam.

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter