Subscribe Our Channel

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (2)

Malamai sun yi sabani a kan yin k'aho da tsaga da zane ga mai Azumi, wasu sun ce Azumin wanda aka yi masa k'ahon da na wanzamin ya baci, wasu sun ce; a'a, bai baci ba. Amma Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya ya rinjayar da bacin Azumin wanda aka yi masa k'aho da na wanzamin, da kuma na wanda aka yi masa tsaga ko zane da aska a jikinsa.

Al-Imam Ibnul Qayyim da Ibnu Muflih sun hakaito hakan daga gare shi. Ibnul Qayyim ya ce:
الصواب الفطر بالحجامة والفصاد والتشريط وهو اختيار شيخنا أبي العباس بن تيمية
تهذيب السنن (6/ 368)

"Magana ta dadai; Azumi yana baci in an yi k'aho ko tsaga ko zane a jikin mai Azumi, kuma shi ne zabin Shehinmu Abul Abbas Ibnu Taimiyya".

Ga nan inda Shaikhul Islamin ya yi bayani kamar haka:
قد بينا أن الفطر بالحجامة على وفق الأصول والقياس وأنه من جنس الفطر بدم الحيض والاستقاءة وبالاستمناء. وإذا كان كذلك فبأي وجه أراد إخراج الدم أفطر كما أنه بأي وجه أخرج القيء أفطر سواء جذب القيء بإدخال يده أو بشم ما يقيئه أو وضع يده تحت بطنه واستخرج القيء فتلك طرق لإخراج القيء وهذه طرق لإخراج الدم ولهذا كان خروج الدم بهذا وهذا سواء في (باب الطهارة)
مجموع الفتاوى (25/ 257)

"Mun yi bayanin cewa; k'aho yana karya Azumi bisa ka'idojin Shari'a da Qiyasi, kuma lallai yana cikin jinsin bacin Azumi saboda jinin haila ne, da jawo amai, da jawo fitan maniyyi. In haka ne, ta kowace hanya idan mutum ya fitar da jini daga jikinsa to Azuminsa ya karye, kamar yadda ta kowace hanya in ya fitar da amai Azuminsa ya karye, sawa'un ya jawo aman ne ta hanyar sanya yatsa a baki, ko ya shanshana abin da zai jawo masa amai, ko ya sanya hanunsa a kasan cikinsa ya turo aman, wadancan su ne hanyoyin jawo amai. Wadannan kuma hanyoyin fitar da jini (k'aho, tsaga da zane), wadannan kuwa duka dadai suke a Babin Tsarki".

Shi ma wanzami mai yin k'ahon Azuminsa yana baci saboda yana zuk'an jinin da bakinsa. Ya ce:
وأما الحاجم فإنه يجتذب الهواء الذي في القارورة بامتصاصه والهواء يجتذب ما فيها من الدم فربما صعد مع الهواء شيء من الدم ودخل في حلقه وهو لا يشعر...
وأما الشارط فليس بحاجم وهذا المعنى منتف فيه فلا يفطر الشارط
مجموع الفتاوى (25/ 257 - 258)

"Amma shi wanzami mai yin k'aho, yana zuk'an iskan da yake cikin k'ahon nasa, ta hanyar tsotsa, da kuma iskan da yake zuk'an abin da ke cikinsa na jini, ta yiwu wani abu na jinin ya tafi da iskan da ya zuk'a ya shiga mak'ogwaronsa alhali bai sani ba…
Amma shi mai yi wa mutane tsaga ba kamar mai yin k'aho ba ne, shi ba a samun zuk'an jini da baki a tsaga, don haka shi Azuminsa ba ya baci".

Saboda haka, wanzami mai yin k'aho Azuminsa yana baci, amma mai yin tsaga da zane shi Azuminsa ba ya baci. Haka wanda aka yi masa daya daga cikin wadannan; k'aho, tsaga ko zane to Azuminsa ya baci.

Aallahu A'alam.

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter