FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (7)
Shari'a ta yi sauki ga wasu nau'in mutane guda hudu, ta ba su daman shan Azumi matukar suna cikin halin da ya sa aka yi musu rangwamen. Wadannan nau'ukan mutane kuwa su ne:
1- Matafiyi.
2- Maras lafiya.
3- Mai ciki ko mai shayarwa.
4- Gajiyayyen tsoho.
Kowanne akwai bayanai da za su zo nan gaba a kansa insha Allahu.
Na farko a cikinsu shi ne: Matafiyi.
Shi Matafiyi an ba shi daman ya sha Azumi a watan Ramadhan, sai bayan Sallah ya rama Azumin da ya sha.
Shaikhul Islami ya ce:
الفطر للمسافر جائز باتفاق المسلمين سواء كان سفر حج أو جهاد أو تجارة أو نحو ذلك من الأسفار التي لا يكرهها الله ورسوله. وتنازعوا في سفر المعصية كالذي يسافر ليقطع الطريق ونحو ذلك على قولين مشهورين...
ويجوز الفطر للمسافر باتفاق الأمة سواء كان قادرا على الصيام أو عاجزا وسواء شق عليه الصوم أو لم يشق بحيث لو كان مسافرا في الظل والماء ومعه من يخدمه جاز له الفطر والقصر.
مجموع الفتاوى (25/ 209 - 210)
"Shan ruwa ga Matafiyi ya halasta bisa Ittifaqin Musulmai, sawa'un tafiya ce ta Hajji ko Jihadi ko kasuwanci ko makamancinsu cikin tafiye-tafiye da Allah da Manzonsa ba sa kinsu. Amma Malamai sun yi sabani a kan shan Azumi a tafiya ta sabon Allah, kamar fashi da makami da makamancinsa zuwa shahararrun maganganu guda biyu...
Saboda haka ya halasta Matafiyi ya sha Azumi bisa Ittifaqin Al'umma, sawa'un zai iya yin Azumin ko ba zai iya yi ba, sawa'un Azumin zai wahalar da shi ko ba zai wahalar da shi ba, ta yadda a ce: tafiyar tasa a cikin inuwa ce ko cikin ruwa, kuma a tare da shi akwai mai yi masa hidima, to ya halasta ya sha Azuminsa, kuma ya yi Sallar Kasaru".
Kuma shan Azumin shi ya fi falala a kan yin Azumin.
Shaikhul Islami ya ce:
أما المسافر فيفطر باتفاق المسلمين وإن لم يكن عليه مشقة والفطر له أفضل. وإن صام جاز عند أكثر العلماء. ومنهم من يقول لا يجزئه.
مجموع الفتاوى (25/ 214)
"Amma shi Matafiyi zai sha Azumi bisa Ittifaqin Musulmai, ko da kuwa ba zai sha wahala ba shan Azumin shi ya fi falala. In kuma ya ce: zai yi Azumin to ya halasta gare shi wajen mafi yawan Malamai. Amma akwai wadanda suke ganin yin Azumin bai isar masa ba".
Saboda haka duk wanda zai yi tafiya ta da'a ma Allah, kamar tafiya aikin Hajji ko Umra ko Jihadi, ko tafiya ta halas kamar tafiya kasuwanci to abin da ya fi masa falala ya sha Azuminsa, bayan Sallah sai ya rama. Kuma sawa'un tafiyar a jirgi ne ko mota, duka ya halasta ya sha Azumin, kuma hakan shi ya fi falala.
Wannan shi yake nuna mana saukin Shari'ar Muslunci da rahamar Allah ga bayinsa.
Allahu A'alam.