FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (1)
Malamai sun yi sabani a kan sanya kwalli ga mai azumi, haka yi masa allura ko d'iga masa magani ta kororon roba, ko sa masa magani a rauni da ya yi a kai, ko rauni a ciki. Wasu Malaman sun ce Azuminsa ya baci, wasu kuma sun ce: Azumin ya yi.
Sai Ibnu Taimiyya ya ce:
والأظهر أنه لا يفطر بشيء من ذلك. فإن الصيام من دين المسلمين الذي يحتاج إلى معرفته الخاص والعام فلو كانت هذه الأمور مما حرمها الله ورسوله في الصيام ويفسد الصوم بها لكان هذا مما يجب على الرسول بيانه ولو ذكر ذلك لعلمه الصحابة وبلغوه الأمة كما بلغوا سائر شرعه. فلما لم ينقل أحد من أهل العلم عن النبي صلى الله عليه وسلم في ذلك لا حديثا صحيحا ولا ضعيفا ولا مسندا ولا مرسلا - علم أنه لم يذكر شيئا من ذلك.
مجموع الفتاوى (25/ 233 - 234)
"Magana mafi inganci ita ce: lallai AZUMIN MUTUM BA YA BACI saboda wadannan abubuwa, saboda Azumi hukunci ne na Addinin dukkan Musulmai, wanda kowa yana bukatar saninsa, malamai da gama garin mutane gaba daya. Da a ce: wadannan abubuwa Allah da Manzonsa sun haramta su ga mai azumi, kuma suna bata azumi, da dole Annabi (saw) zai yi bayaninsu, kuma da a ce: ya yi bayanin to da Sahabbansa sun sani, su kuma da sun isar da shi ga al'umma, kamar yadda suka isar da sauran hukunce-hukuncen Shari'a.
To saboda babu wani cikin Malamai wanda ya ruwaito wani abu a kan haka daga Annabi (saw), babu Hadisi ingantacce, ko da mai rauni, mai Isnadi ko Mursali, to sai aka san cewa; Annabi (saw) bai ambaci komai a kan wadancan abubuwa ba".
A cikin wannan bayanin akwai ka'ida mai muhimmanci wajen fahimtar Addini, ta yadda babu abin da yake zama Shari'a sai abin da ya zo ta hanyar Annabi (saw), Sahabbansa kuma suka isar da shi ga al'umma.
Don haka sa kwalli, da yin allura da sauran hanyoyin sa magani a jikin mutum ba sa karya Azumi.
Allahu A'alam.