ALAKAR IBNU TAIMIYYA DA TA'ADDANCI
Wasu da ba sa fahimtar Larabci, bayan sun jahilci Addini suna fassara maganganun Shaikhul Islami bnu Taimiyya suna canza masa ma'anar maganarsa, don su yi masa ta'addanci.
1- Wani ya ce: Ibnu Taimiyya ya ce: A kashe wanda ya bayyana Niyya.
To ga nan asalin maganar Ibnu Taimiyya kamar haka:
الجهر بلفظ النية ليس مشروعا ...
ومن ادعى أن ذلك دين الله وأنه واجب فإنه يجب تعريفه الشريعة واستتابته من هذا القول فإن أصر على ذلك قتل
مجموع الفتاوى (22/ 236)
"Bayyana Niyyar Sallah (furtawa da baki) ba a shar'anta shi ba...
Duk wanda ya yi ikirarin cewa; hakan Addinin Allah ne, kuma wajibi ne, to wajibi ne a koyar da shi ya san Shari'a, kuma a nemi ya tuba daga wannan ra'ayi, idan ya doge a kan ra'ayin to a kashe shi".
Ibnu Taimiyya ya yi maganan kisa ne idan mutumin ya doge a kan yin karya ma Allah na cewa; hakan Wajibi ne kuma Addinin Allah ne, alhali an sanar da shi, kuma an nemi ya tuba amma ya ki. Sabanin yadda shi wancan ya yi karya wa Ibnu Taimiyya.
2- Kuma ya ce: Ibnu Taimiyya ya ce: A kashe wanda ba ya ki yin Sallar Juma'a ko ta Jam'i.
Ga maganar Ibnu Taimiyya kamar haka:
وسئل: عن رجل جار للمسجد ولم يحضر مع الجماعة الصلاة ويحتج بدكانه.
فأجاب: الحمد لله، يؤمر بالصلاة مع المسلمين فإن كان لا يصلي فإنه يستتاب فإن تاب وإلا قتل.
مجموع الفتاوى (23/ 254)
"An tambayi Ibnu Taimiyya a kan makobcin Masallaci alhali ba ya halartar Sallar Jam'in, yana kafa hujja da jiran shagonsa?
Sai ya ba da amsa da cewa: Alhamdu lillah, za a umurci mutumin da yin Sallah tare da Musulmai (cikin Jam'i), idan kuma ya ki yin Sallar to za a nemi ya tuba, in ya tuba shi kenan, in kuma ya ki sai a kashe shi".
To ka ga wannan wanda ya ki yin Sallar ne bayan an sa shi ya yi, sai ya ki yi saboda bai yarda da Sallar Jam'in ba. Alhali duk wanda bai yarda da Sallar Jam'i ba to za a nemi ya tuba, in ya ki sai a kashe shi.
Kuma ai ko ma ba wannan ba, ai Annabi (saw) ya yi niyyar kona gidajen masu kin halartar Jam'i ba tare da uzuri ba:
«لقد هممت أن آمر بالصلاة فتقام، ثم أخالف إلى منازل قوم لا يشهدون الصلاة، فأحرق عليهم»
صحيح البخاري (3/ 122)
«لقد هممت أن آمر رجلا يصلي بالناس، ثم أحرق على رجال يتخلفون عن الجمعة بيوتهم»
صحيح مسلم (1/ 452)
To shin menene laifin Ibnu Taimiyya?!
Ko don ya ya fi kowa yakar Falsafa da Shi'anci da Sufanci?!
3- Kuma du ya ce: -wai- Ibnu Taimiyya ya ce: A kashe wanda ya ci naman maciji ko kunama.
Alhali ga nan maganar Ibnu Taimiyyar kamar haka:
أكل الخبائث وأكل الحيات والعقارب حرام بإجماع المسلمين. فمن أكلها مستحلا لذلك فإنه يستتاب فإن تاب وإلا قتل.
مجموع الفتاوى (11/ 609)
"Cin kazanta da cin macizai da kunamai haramun ne bisa Ijma'in Musulmai. Duk wanda ya ci maciji ko kunama YANA MAI HALASTAWA to za a nemi ya tuba, in ya tuba shi kenan, in kuma ya ki sai a kashe shi".
To kun ga wannan ma magana yake yi a kan wanda ya halasta cin haram. Kuma kowa ya san halasta haram kafirci ne.
4- Kuma ya sake cewa: "sunan malamin (dan bidia) mai kira zuwa bidia. Kuma gashi Ibn Taimiyya yace a kasheshi!".
To wannar magana ba haka a sake take ba, ga yadda take:
والداعي إلى البدعة مستحق العقوبة باتفاق المسلمين وعقوبته تكون تارة بالقتل وتارة بما دونه كما قتل السلف جهم بن صفوان والجعد بن درهم وغيلان القدري وغيرهم.
مجموع الفتاوى (35/ 414)
"Mai kira zuwa ga bidi'a ya cancanci horo bisa ittifaqin Musulmai, wani lokaci horon zai kasance da kisa, wani lokacin kuma da horo kasa da kisan, kamar yadda Magabata suka kashe Jaham bn Safwan da Ja'ad bn Dirham da Gailan Baqadare da wasunsu".
To abin lura a nan, Ibnu Taimiyya bai ce a kashe dukkan masu kira ga bidi'a ba, a'a, kashi biyu ya raba horon:
1. Akwai wadanda horonsu kisa ne.
2. Akwai kuma wadanda horon nasu bai kai kisa ba.
Wadanda yake nufin a yi musu horo da kisa su ne wadanda suke kira ga bidi'a ta kafirci, kamar wadanda ya kawo misalansu. A wannan zamanin kuma kamar 'Yan Hakika cikin Sufayen Darikar Tijjaniyya da Qadiriyya.
Kai, akwai 'yan bidi'ar da ana iya kashe su ko da bidi'ar tasu ba ta kafirci ba ce, kamar Khawarijawa. Saboda Annabi (saw) ya ce:
«سيخرج قوم في آخر الزمان، أحداث الأسنان، سفهاء الأحلام، يقولون من خير قول البرية، لا يجاوز إيمانهم حناجرهم، يمرقون من الدين، كما يمرق السهم من الرمية، فأينما لقيتموهم فاقتلوهم، فإن في قتلهم أجرا لمن قتلهم يوم القيامة»
صحيح البخاري (9/ 16)
Sa'annan kuma shi wannan mai wadancan maganganu yana nuna cewa; Kungiyoyin Ta'addanci na zamani suna kashe mutane ne riko da irin wadannan maganganu na Ibnu Taimiyya, alhali babu mai fadin haka sai jahili ko azzalumi, saboda duk wani horo da uquba da Ibnu Taimiyya ya yi bayaninsa bai yarda daidaikun mutane su zartas da ita ba, masu zartaswan su ne hukuma da shugabanni.
Shaikhul Islami ® ya ce:
ليس لأحد أن يزيل المنكر بما هو أنكر منه: مثل أن يقوم واحد من الناس يريد أن يقطع يد السارق، ويجلد الشارب، ويقيم الحدود؛ لأنه لو فعل ذلك لأفضى إلى الهرج والفساد؛ لأن كل واحد يضرب غيره ويدعي أنه استحق ذلك؛ فهذا مما ينبغي أن يقتصر فيه على ولي الأمر المطاع كالسلطان ونوابه.
مختصر الفتاوى المصرية (ص: 580)
"Bai halasta ga wani mutum ya kawar da mummunan aiki da abin da ya fi shi muni ba. Misali wani daga cikin mutane ya tashi da nufin zai yanke hanun Barawo, zai yi bulala wa mashayin giya, zai tsayar da haddi, saboda in ya aikata haka to zai kai ga zubar da jini da barna, saboda kowane mutum zai iya dukan waninsa sai ya yi ikirarin cewa; ya cancanci ayi masa hakan ne. Wannan kuwa abu ne da ya kamata a takaita shi a kan Shugaba mai iko wanda ake yi masa da'a da kuma mataimakansa (Alkalai, 'Yan Sanda da sauran jami'an tsaro)".
Kuma ya ce:
وإذا قدر على كافر حربي فنطق بالشهادتين وجب الكف عنه؛ بخلاف الخارجين عن الشريعة، كالمرتدين الذين قاتلهم أبو بكر رضي الله عنه، أو الخوارج الذين قاتلهم علي: كالخرمية، والتتار، وأمثال هذه الطوائف ممن نطق بالشهادتين ولا يلتزم شرائع الإسلام.
وأما الحربي إذا نطق بها كف عنه، ثم إن لم يصل فإنه يستتاب، فإن صلى وإلا قتله الإمام، وليس لأحد من الرعية قتله، إنما يقتله ولي الأمر عند مالك والشافعي وأحمد؛ وعند أبي حنيفة يعاقبه بدون القتل.
مختصر الفتاوى المصرية (ص: 510)
"Idan an kama Kafiri Abokin Gaba (Mai yakar Musulmai), sai ya furta Kalmar Shahada, TO WAJIBI NE A KAME DAGA YAKARSA, sabanin masu fita daga Shari'a, kamar 'yan Ridda, wadanda Abubakar (ra) ya yake su, ko kuma Khawarijawa wadanda Aliyu (ra) ya yake su, kamar "Kharmiyya", "Tatar" da makamantan wadannan kungiyoyi daga cikin wadanda suka furta Kalmar Shahada amma kuma ba su yi riko da Shari'ar Muslunci ba.
Amma shi Kafiri Abokin Gaba (mai yakar Musulmai) idan ya furta Kalmar Shahada za a kame daga yakarsa, sa'annan idan ya ki yin Sallah za a nemi ya tuba, in ya yi Sallar to shi kenan, in kuma ya ki TO SAI SHUGABA YA KASHE SHI. BABU WANI TALAKA DA YAKE DA DAMAN YA KASHE SHI, KAWAI SHUGABA NE ZAI KASHE SHI, haka abin yake a wajen Imamu Malik, Shafi'iy da Ahmad, amma a wajen Abu Hanifa za a yi masa horo ne da abin da ba kisa ba".
Saboda haka, da wannan za ka san shi wancan mai rubuce - rubuce jahilci ne da son zuciya suke damunsa.
Da farko bai san Larabci ba shi ya sa ya kasa fahimtar maganar Ibnu Taimiyya, bai san cewa; Ibnu Taimiyya yana magana ne a kan wanda ya halasta haram ko ya ki yarda da wajabci abin da yake wajibi ne a Shari'a ba, kuma bai san Addini ba, shi ya sa bai san dalilan Ibnu Taimiyya a kan maganganunsa ba, kuma bai san maganganun sauran malamai a kan mas'alolin ba.
Saboda haka, in an yi ma wannan mutumin uzuri a kan jahilci to ba za a yi masa uzuri a kan son zuciya da Ta'addanci da ya yi wa Ibnu Taimiyya ba.
Ibnu Taimiyya ciwon ido sai hakuri.